CHAPTER 33

416 70 15
                                    

Naman munira ta bashi tare da fadin ku zo mu tafi yawo yan uwa na. Yimla yace ina muka nufa. Munira tace kasuwa mutumi na tare da delewa tana mai shafa kanshi. Zul kam sai sude baki yake dan ya samu nama ya ci.

Yawon su sukayi sosai sanda taga dare ya fara yi kafa ya fara raguwa sannan suka koma fada ta wannan ramin tabi ta koma bayan tayi sallama da abokan ta saide shigan ta ke da wuya taga yarima kabir tsaye kamar ita yake jira tace ba nace bazaka dame ni ba da hannu ya mata alamun ta wuce kamin yace ni ban ma san bakyanan ba allah ne yasa muka hadu.

Murkuda vaki tayi ta nufi bangaren bayi tana me daura aniyan komawa bangaren sarauniya saboda kar yarima kabir yasa a sake kaita bangaren sa. Nace kash an gudu ba'a tsira ba dakin uwar sa fa zaki koma haduwa dole.

Koda ta koma dungure mata kai su nana sukayi tare da mata korafin yanda ta basu tsoro dare yayi sosai bata dawo ba a zahiri dai lokacin karfe 8 ne amma kuma a lokacin su ganin shi suke kanar irin 11 nan.

Ko da gari ya waye kamar kullum wanka kowa yayi ya kama aikin sa yayin da munira ta nufi sashin sarauniya don sanar da ita cewa zata koma bangaren ta. Sarauniya taji dadin hakan dan haka cikin fara'a tace toh tun kamin k8 dawo fara da fitar da kayan karin kumallo na. Hindatu wacce wannan aikin ta ne kuma tafi kowa kusanci da sarauniya tayi kiu ta kalli munira amma bata ce komai ba. Sarauniya tace ya ma sunan naki? Munira tace laila sannan ta fita.

Hade abincin tayi guri guda ta nufi wajen su yimlan ta ta wannan ramin da ta saba wanda ba kowa bane ma yasan dashi itama leke leke ne ya leko mata. Bayan sun cinye ne tace suje su huta ita zata tafi ganin gari wanda a maganar gaskiya ta daklde batayi harbi da kwari da baka ba dan hanka zata tafi neman yan farauta ne dan tabi tawagar su.

Baiwa mace me suna rabi ita aka bawa ragaman bibiyar munira ta bangaren yarima kabir yayin da wani mai suna nuhu shi aliyu ya saka ya bibiyi munira ta bangaren yarima.

Tafiya munira take taji kamar ana binta hakan yasa ta baza kunne tabbas binta ake amma me bin nata a biye yake binta. Waigawa tayi taga wani bafulatani ne kayan sa de kamar na kowa ne hakan yasa bata kawo a ranta shine me bin nata ba. Wanda nuhu kuwa ansa ya cire kayan shi na fada ne dan kar ya ja hankalin mutane.

Kasuwa ta sake shiga ta tare wata baiwar Allah tare da yi mata sallama tace don Allah tasan inda ake saida kwari da baka ? Kwatance tayi mata munira tayi godiya. Waigawa tayi da sauri ganin har yanzu taji ana binta taga de fulanin nan yana bayan ta saide yaci gaba da tafiya har ya wuce ta wanda nuhu yayi haka ne dan kar ta zargi komai.

Haya tayi abinta inda anan ma tahadu da yan farauta tace su yi mata kwatancen inda ake farauta basu kawo komai a ransu ba suka kwanta mata. Sai wajen la'asar ta dawo tare da mayar wa mai kwari da baka abin sa. Bangaje taji anyi ya waigo suka hada ido amma bai tsaya ba yaci gaba da gudu gani tayi kamar ta sanshi amma dai ta dauke kai tayi gaba abinta.

Cigaba tayi da tafiya a kasuwa tana kara ganin gari taji ba'a dena binta ba hakan yasa ta fita da gudu suma gudu suka sa a bayan wani tukuba ta labe nuhu ya wuce ya dauka kwana ta sha. Wani ne ya tsuguna a gefen ta ihu ta fasa tare da fadin ka dena bina yace shh shhhhh sai taga ashe ba shi bane wani ne matsawa tayi tace waye kai? Washe baki yayi yace kanwata sunana munir, yanzu ki taimaka ki yi shiru kar su kamani. Sake kallon shi tayi daga sama har kasa bata ga yayi kama da yan iskan gar ba hakan yasa tayi shiru. Can yace me yasa kika buya anan? Tace ina ruwanka? bana son gulma. Lekawa ta sake yi ganin babu kamar an dena binta yasa ta kade jikin ta tace toh yaya munir na tafi gida.

Hannu shima ya daga mata a ranta tace sunan mu daya dashi amma dai yanzu suna na laila.
Komawa fada tayi zata shiga taga an toshe ramin da take wucewa. Hakan yasa cikin jan kafa ta nufi babban kofa wato gate dogarai ne suka tare ta.

Daya miko hannu tace me yace shedan shiga da fice tace yaya na kayi hakuri na manta yarima kabir ne ya aike ni. Sukace doka ce idan ba da izinin jinin sarauta ba'a shiga ko a fita dan haka idan da shi ya aike ki zai baki shaida. Tace amma na fita ai kun manta nine da ba shaida baza ku bari na fita ba. Dauke kai sukayi dan ba wani gane abinda take fadi sukeyi ba.

Ganin zata damesu da magiya ne yasa dayan ya daka mata tsawa tare da korata. Cikin gari ta shiga tana kalle kalle gashi magriba ya kawo kai bata ma san ina take tafiya ba kawai tana tafiya tana karta sheda ne.  Wani gida ta shiga suka taimaka mata tayi magrib sannan wani tunani yazo mata. Tunda yazu dare yayi me zai hana taje ta haura gini baza'a ganta ba ai.
Nace gidan sarki ne fa ba bukka ba hajiya munira.

Koda taje akwai matsala 1 ginin yayi tsayi ba yanda za'a yi ta iya haurawa ko a mafarki kuma babu wani abu da zata kama ta hau ta dira kamar bishiya ko makamantan su dan ginin kanshi yakai tayi bishiyar maina wato darbejiya irin doguwar nan. Ranan ko ta ina ta gaura ita kanta bata sani ba.

Fata kewayawa tayi tana lallabewa dan kuwa fadawa ne ta kusan ko ina in dare yayi ma sunfi yawa fiye da rana. Wani kansamin ruwa (pond) ta gani kawai ta tuna hira da taji yarima sunyi shi da ali a hanyar su kamain su hadu da barayi har a rabasu.
Kandamin ruwan nan hanyoyi ne da akayi domin tsira ko guduwa yayin afkuwar hatsari ko musiba wato emergency exit.

Na bangaren sarki da yarima da mahaifiyar sa fatima a sade suke wato daga na daya in jabi hanyar ruwa zaka iya zuwa na daya kuma anyi inda zaka dinga tsayawa shan numfashi

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Na bangaren sarki da yarima da mahaifiyar sa fatima a sade suke wato daga na daya in jabi hanyar ruwa zaka iya zuwa na daya kuma anyi inda zaka dinga tsayawa shan numfashi. Na yarima ukun can ma hanyan su daya na sarauniya hauwa kuma kawai da na sarki ne a hade domin har uku ne a bangaren sarki

Bata ma tsaya yin tunani ba ta shiga tana mai fata kar ta fito a inda bai dace ta fito. Amma dai abu daya da ta sani shine ko ma a ina ta fito toh babu shakka a fada zata tsinci kanta wanda shi yafi komai mahimmanci.

Koda ta fito ganin ta tayi a daya daga cikin fadodin dukda ta shiga ko wanne a baya bazata iya tuna wannan na wanene ba. Domin kuwa sanda ta shigo a baya idon ta neman yarima yake ba wai kallon gini ba. Ajiyan zuciya ta kara yi a karo na barkatai dan ta kasa gano dalilin da yasa yarima ya nuna bai santa ba. In ta samu dama zata yi magana dashi a boye kila akwai matsala ne.

Iskan da ya daki fatar ta ne ya tuna mata da bata cikin daki da kuma bargon ta. Karan tafiya dogarai taji da hasken aci balbal dinsu dan haka tayi sauri ta labe a bayan bishiya wucewa sukayi. Da sanda ta fito tana leke leke ta jiyo takun wasu ma da sauri ta tsuguna suna wucewa ta fada kofar da ta gani a gefen ta nace kafci wannan kokari naki da mugun yawa yake.

Baki da hanci da ido ta saka tare da tsayawa a inda take saboda abinda idonta yayi arba dashi.

TOH FA KO INA MUNIRA TA SHIGA ? KU BIYONI DAN JI A CHAPTER NA GABA👌🏼

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CEWhere stories live. Discover now