Part 5

48 2 0
                                    

*TSANTSAR YAUDARA😭💔*

*'Yar mutan zazzau Naanah M Sha'aban✍🏾*

*Sadaukarwa ga habibaties👯🏽‍♂️💃🏼*

*Habibaties👯🏽‍♂️gashi nan ku koya masa yawo, idan nace yawo ina nufin ku koya masa tafiya💃🏼ku tabbatar ya san ko ina a cikin social media🥳*

*Shafi na 5*

Alhaji Lawal mahaifin Fad'ima suka gani tsaye a bayansu, fuskarsa babu alamar wasa ya had'eta tam kamar bai tab'a yin dariya ba, gaba d'ayansu sunyi matuk'ar mamakin jin kalaman da yake fad'a a kan su, Mummy ta mik'e tsaye tana kallonshi irin kallon nan na me ka ke nufi ta ce "To yau kuma Abban Fad'ima mu ka ke cewa mayaudara?" Wata muguwar tsawa ya daka mata "Ke kina tunanin cewa ni zan baku goyan baya akan yaudarar baiwar Allah da tayi matuk'ar yarda da ku, to duk abun da ku ke b'oye min na ji kuma ni da kai na ba zan tab'a yarda Abdulrahman ya auri Fad'ima ba har abada zan kira Alhaji Saleh ma na gaya masa ni na janye auren gaba d'aya" Yana gama magana ya nufi b'angarensa zuciyarsa nayi masa zafi, yanzu ace 'yarsa tilo ita ce take da hali irin wannan ta ci amanar k'awarta tabbas zai san matakin da zai d'auka akan hakan kuma ko Fad'ima zata mutu ba zai tab'a yarda ta auri Abdulrahman ba, da wannan tunanin ya samu ya yi wanka sannan ya kwanta a tsararran gadon d'akinsa.

Shin ya ya akayi Alhaji Lawal ya san yaudarar da Fad'ima ta yi wa Khausar??? Yadda akayi shine Alhaji Lawal ya dawo daga gurin aikinsa, ya biya wani supermarket dan ya yi musu siyayyan kayan tab'awa, bayan ya fito daga cikin motarsa yana kok'arin shiga Babban shagon yaji wasu matasan maza guda biyu suna hirar yadda Fad'ima da Abdulrahman suka yaudari Khausar d'in, ransa ya yi matuk'ar b'aci siyayyar da bai yi ba kenan ya shiga mota ya nufi gida, dan shi a rayuwarsa ya tsani mutum maci amana kuma mayaudari.

Fad'ima kuwa tana jin abun da Abban na ta ya fad'a ta mik'e tsaye tare da fasa wata gigitatciyar k'ara ta fad'i k'asa sumammiya, Hajiya Laure ta nufi gurinta a rud'e tana kiran sunanta "Fad'ima! Fad'ima!! Fad'ima!!!" Amman ina babu alamar numfashi a jikin Fad'ima, ruwa ta d'auko a fridge ta shiga shek'a mata amman ko kad'an babu alamar zata farfad'o, wani irin kuka ta fashe dashi tana cewa "Alhaji ka kashe min yarinyata, akan me zaka fad'i haka, to menene a ciki dan ta nuna tana son saurayin k'awarta ai ba haram ba ne, idan kuma akwai inda aka ce bai halatta k'awa ta auri saurayin k'awarta ba sai ka zo ka janyo min ayar ko kuma hadisi idan kuma a fik'ihu ne shima ka janyo min na ji" Haka dai tai-tayin b'ab'atunta kamar wata zararriya tana surutai barkatai, daga k'arshe da ta ga dai abun yana neman ya gagareta Alhaji Lawal ya yi banza da ita kamar bai san tana yi ba, ta shiga kok'arin d'aga Fad'ima da yake Hajiya Laure tana da k'iba sosai haka ta d'auki Fad'ima kamar wata jaririya ta fita da ita waje tana k'wad'awa driver kira "Mati! Mati!! Mati!!!" Da gudu Mati ya k'araso inda take har yana tuntub'e dan yasan halinta yanzu sai ta yi masa rashin mutunci ta ce tana kiransa ya yi mata banza, cikin tsawa ta ce "Dallachan je ka bud'e min kofar mota, ka zo ka wani tsaya min a gaba saboda tsabar kai dak'ik'i ne" Jikin Mati a sanyaye ya nufi motar ya bud'e mata bayan motar, sai da ta fara saka Fad'ima sannan ita ma ta shiga ta zauna, Mati wanda yana bud'ewa Hajiya Lauren kofar baya ya shiga mazaunin driver, sai da ya tabbatar ta shiga ta rufe motar sannan ya ja motar ya d'auki hanyar asibitin da suke zuwa, a hanya Hajiya Laure sai jaraba takeyi masa a kan ya yi sauri, Mati ya rasa ma ya zai yi dan shi irin gudun da yake yi ma tsoro yake ba shi, amman a haka take so ya yi gudu, a zuciyarsa ya ce "To wannan matar idan ba so ki ke na tashi sama ba, ko kuma na je na bigi wata motar na mutu a banza, saboda neman lafiyar wannan mayaudariyar, ban san ya ki ke so nayi ba" Ya k'arasa maganar tare da jan wani d'an k'aramin tsaki, wanda shi kad'ai ne yasan ya yi, suna isa katafaran asibitin tun kafin Mati ya yi parking Hajiya Laure ta bud'e murfin motar tana kok'arin fitowa, wani irin wawan burki Mati ya ja, Hajiya Laure sai da kanta ya bugu da kujera ai kuwa tana d'agowa ta wanke Mati da wani irin mahaukacin mari wanda sai da kansa ya bugu da sitiyarin motar ta ce "Shashasha mahaukaci, dabba mara tunani saboda kai jahili ne zaka ja wannan burkin wato so ka ke ka kasheni, to wallahi baka isa ba dan gidan talakawa kawai" Tana gama magana ta fita a dai-dai lokacin kuma wasu nurses guda hud'u suka k'araso wajen suna tura wani dogon gadon da ake d'aukar mara lafiya, Hajiya Laure ta matsa musu suka d'auko Fad'ima suka dorata a kan gadon, kai tsaye emargency room sukayi da ita Hajiya Laure na biye dasu a baya, sai da aka je wajen bakin kofar shiga emargency room Hajiya Laure ta ja ta tsaya dan ta san komai za ta yi ba za su tab'a barinta ta shiga ba, Mati kuwa bai iya d'agowa ba, sai da ya tabbatar sunyi nisa, sannan ya d'ago da'kyar yana rik'e goshinsa hawaye na zuba daga cikin idanuwansa ya ce "Insha Allahu ba za ku tab'a yin farin ciki a rayuwa ba har abada haka zaku dauwama cikin bak'in ciki" Sai da ya yi kuka mai isarsa sannan ya ja motar ya nufi gida.

TSANTSAR YAUDARAWhere stories live. Discover now