63-64

171 11 6
                                    

‍✈️CAPTAIN UMAR👨🏻‍✈️

    Story and writing
                By
        Fatima(Zarah)

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

*Wannan labarin kirkirarren labarine banyi dan wata ko wani ba Wanda yaga labarin yazo dai dai danasa toh akasine ban yarda a chanzamin labari ba Wanda ya chanzamin ban yafeba.*

*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*

*Typing..........*
*31/01/2021*

Page 65⏩66

     Bayan wasu watanni hankula duk sun kwanta,kowa ya bar was Allah lamarinsa,Kamar ko yaushe yau ma Zarah na zaune a man bed dinta tana kallo a laptop din ta,shiru tayi can Yana tuna halin rayuwa,bata taba tunanin cewa Wai akwai ranar da zasu rabu da Sadeeq ba sai gashi cikin kankanin lokaci komai ya chanza cikin ikon Allah,yanzu ta maids lamuranta ga ubangiji Dan tasan shine Wanda yafi sanin daidai akan duk abunda ya kaddara wa bawansa.

      Zaune Ammi take da Abba saboda yace tana son magana dashi,kallon sa tayi cike da wani irin yanayi sannan ta fara magana"abban Zarah dama nace me kazo muyi magana game da abunda ya faru da yarinyar man,a ganina tunda yanzu komai ya wuce Kuma shi wancan har ma yayi ajren sa, toh mai zai hana ka nama Umar auren yarinyar nan,ni  kuma na maka alkawarin cewa zamu time mama amanarta",wani irin farin ciki me Abba ya tsinci kansa a ciki wanda bai taba ji ba,cike da jin Dadi yace"Alhamdulillah,Masha Allah gaskiya na dade banji farin cikin da naji yau ba,Kuma na gode was Allah da yasa zan bayar da auren Zarah gurin wanda bani da haufi a kansa wanda nasan ko bayan raina baxai taba cin amanata ba,amma shi Umar din yasan da wannan maganar kuwa?",kallon sa Ammi tayi tace"Kar ka damu no xanyi magana dashi kuma nasan zai amince da wannan auren dan haka kar kasa wannan a zuciyar ka",haka suka zauna suka Dan tattauna akan maganar sannan suka rabu.

       Kamar ko wanni weekend yau ma Umar na gari,yau ma Kamar kullum yazo gaishe da Ammi,bayan sun Gama gaisawa ta kalleshi sannan race"dama Ina son zamu yi magana me dakai,kana da lokacin me yanzun ko sai anjima,just kawai ka sa lokacin I want to talk with u",dukar da kai yayi yace"haba Ammi har sai kince in sa mana lokacin kawai ki saka duk time din da kika ga ya dace"ajiyar zuciya Ammi tayi tace"shikenan yanzu ma zamu iya yin maganar kenan",jinjina mata kai yayi tare da cewa"eh Ammi zamu iya yi yanzu"kallon sa tayi tace"kasan na Dade ina maka maganar aure amma kayi banza da abun baka kulani ba,shikenan yanzu na zaba maka mata wacce nasan tarbiyar ta da nagartar ta,wacce zata iya kula da kai da kuma yaran da zaki samu a gaba",shiru kawai umar yayi zuciyar sa na wani irin bugawa,aure kuma,wa Ammi ta samo mai da zai aura,shi daij ya bani,kallon Ammi yayui yace'" INA jinki Ammi wacece,a ina take?",kallon shi tayi tace"ba wata have illa Zarah",cike da firghita yace"Zarah kuma  Ammi,wannan yar karamar yarinyar "kallon sa Ammi tayi tace" yarinya kuma,shikenan jeka amma ina tabbatar maka da cewa dole ka aureta ko kana so ko baka so,na fada maka in ba haka ba zaka fuskanci mummunan hukunci daga gare ni Wanda bakayi tunani ba",ajiyar zuciya ya sauke sannan  cike da saanyin jiki yace"Dan Allah kiyi hakuri Ammi ban fadi haka Dan ranki ya baci ba,naga yarinyar nan ba sona take yi ba,bana so a kware ta,dan kar aazo a aikata abun da za'a zo ana danasani",kallon shi Ammi tayi tace"kar ka samu komai zai tafi yadda ya kamata,tunda kai dai ka amince ai shikenan,jeka Allah yayi maka albarka",mikewa yayi yana ansawa da "ameen y rabb".

     Ko da Mami ta fada ma Zarah abunda ake cika,kuka ta saka mata tana cewa" Allah Mami bana son sa,shima haka,kinga fa yadda yake zalinta ta,taya zan zauna dashi,ni daij gaskiya ki fada ma Abba bana son sa",kallon ta Mami tayi cikin matsananciyar bacon rai tace"Zarah ni like ce ma haka,dama akwai lokacin da zamu umurce ki da kimana Abu ki bijire,shikenan like kiyi yadda ranki ke so",firgita Zarah tayi jin abunda Mami tace, tasowa tayi ta riko hannnun Mami tana cewa"Dan Allah  kiyi hakuri wallahi INA cikin tashin hankali ne shiyasa kika ji na fadi haka,shikenan na amince da abunda kika ce,Allah yasa hakan shine yafi zama mafi alkhairy a rayuwata da addinina",wani murmushi ne yayi escaping daga bakin mami ,share hawayenta tayi tace"na gode sosai,insha Allahu sai kin samu rayuwa mai kyau da umar,yanda kika mana biyayya kema Allah ya baki masu miki biyayya,yanda ba kya son ganin bacin ranmu kema Allah ya baki wadanda NASA son ganin bacin ranki",sañnnanta rungume ta a jikin ta tana lallasin ta........

https://www.wattpad.com/story/315404360?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_reading&wp_page=reading_part_end&wp_uname=Zahrah193&wp_originator=GNuNn8Z7oQNr8wMvHoDtKLUcCELITN2gRfVMtAcFlyTwLzKF4kvYyuQAA0YqvcWn4zz7TyhGdn4q5W9n5h0o6cby5baHtdAHBiSeOgSZBloRACdikmWk5K5MFxtYsKBe

Vote
Comment
Share

Zahraty

CAPTAIN UMAR Where stories live. Discover now