9_10

743 45 4
                                    

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.

Afuwan banyi Editing ba

9_10

Abba ya nanata innalillahi wa innalillahi raji'un ya kai sau goma, Alhaji Hashim yace "Aliyu ya dai? Koka santa ne?"

"Hashi akwai damuwa fa"

"Damuwar me?"

"A game da wannan yarinyar, ba wai wai bane, 'ya ce a gurina, 'yar ƙanwatace data mutu ta bari, gaskiya bazan ɓoye maka ba nafi shekaru biyar rabona da ita, tana hannun dangin mahaifin ta, kawai se a tsukin kwanakin nan akamin waya akace, tana rashin ji na tura Imran yake ya gano min meke faruwa, yaje ya mata faɗa da jan kunne, ranar da nace maka zan koma gida kano zan tafi, ai gurinta naje ina zuwa suka cemin kwananta kusan huɗu bata gida bsu san inda take ba, na bar saƙon da zarar ta dawo a kirani a waya a sanarmin, kawai se gashi kazo min da wannan hoton, kuma wallahi kwanakin nan kusan kullum senayi mafarki da mahaifiyar ta tana min magiya a kan kar in bar 'yarta ta lalace, nayi Nadamar rashin bawa yarinyar nan mahimmanci, kuma abunda ya janyo haka naga dangin babanta na matuƙar ƙoƙari akanta"

Alhaji Hashim yace "aikuwa da matsala, dan abokan adawa zasu iya amfani da wannan damar gurin yamaɗiɗi da kai a bakin duniya, musamman za'abi diddigi a gano alaƙarka ds ita, da kuma yadda ka gaza kulawa da ita, harta zama haka, dan wannan yarinyar tana kama da kai fiye da yadda take kama da 'ya'yanka"

"Hashim yanzu meye abunyi dan Allah?"

"Abunyi dai kam dole a nemo shi da gaggawa, yanzu duk yadda za'ayi a tabattar an samo inda yarinyar nan take, dan ance jiya akayi hotunan a gurin wani biki a Abuja, kuma shi mawaƙin ya bata kyautar mota"

Alhaji Ali yace "A Abuja akayi bikin?"

"Eh a can ne, a gurin akayi hotunan"

"To yanzu a ina zan gano yarinyar nan ni kuwa, bana son inyi wani kyakkyawan motsi daze sa 'yan Adawa su farga da halin da ake ciki"

Alhaji Hashim yace "kabi komai a sannu, zamu shawo kan matsalar Insha Allah, zan sa a duba min nan Abujan, za'a ganta insha Allah"

"To Allah yasa"

Ɓangaren Amira kuwa, sunyi hotuna da mawaƙin nan, sedai sunyi hotunan ne tana sanye da atamfa da kuma jallabiya, sunyi kyau sosai, sedai wanda akayi agurim party ne take sanye da riga da wando.

Sultan yana ta sake zigata akan ta amince da maganar mawaƙin nan, a fara haskota a cikin raye raye, zatayi kuɗi da kuma suna a duniya, ita dai bata amsawa Sultan ba, ƙarshe ma cewa tayi ya bata guri zata kwanta dare yayi.

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now