WITA A MASAƘA 15_16

665 47 6
                                    

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.

Afuwan banyi Editing ba

KAMAR YADDA NA FAƊA TUNDA FARI, BA LALLAI IN DINGA SAMUN YIN POSTING KULLUM BA, IDAN AN GA BAN POSTING BA AMIN HAƘURI




15_16



NOT EDITED ❌❌❌

Imran ya ajiye wayar ya miƙe ya shiga banɗaki, domin yin wanka.

Dama Yadikko bata san Baba ya kira Imran ba, an ɗauke ta an maida ita ɗaki, se numfarfashi takeyi, jin kanta take kamar an mata rawani da duwatsu, saboda buguwar da tayi, gashi ta bugu a ƙugunta da kafaɗunta.

Baba ya shiga ɗakin Yadikko Yace "na kira yaran nan akan abunda yarinyar nan ta yi, ko za'a samu ya bada wani abu a sai miki magani, amma yace wai ta ɗakko mana wata rigima, kuma lallai a nemo lambarta a tura masa yanzu"

Yadikko ta ɗago tace "ina jibi in Allah ya kaimu zamuje can garin biki, meye na nemo lambarta kuma? Nifa kar inje su kewaye su munfaurce mu fa"

Umma tace "Yadikko da yaya zaki bikin? Kina kallo ko tashi tsaye kin kasa?"

"Kina nufin zaku tafi ku barni ne a nan? Yaseen se naje aje aci duk uwar da za'ayi dani, kuma ni da so samune ma wallahi Amira ba zata gurin bikin nan, ku rabu dashi kar wanda ya bashi lambarta, ni ku bawa su Sadiya lambarsa ma, su dinga gaishe shi ko Allah yasa a dace"

Usman yace "Yadikko, ki rufa mana Asiri ki rufawa kanki, kina ji yace lallai a samo lambarta ta gangamo wata fitinar da zata haɗa damu, amma kima cewa kar a bashi lambar? Idan abun ya haɗa damu fa?"

"Ba abunda ze haɗa kowa, amma baza'a bashi ba, haka kurum ita da ta janyo koma menene ya ƙare kanta"

Usman yasa ka ya fita yace "wallahi baza'a janyo bala'i ya haɗa dani ba, ina dalili?"

Ya kira Fa'iza yace ta tura masa lambar Amira.

Aikuwa ba'a jima ba ta turo masa lambar, yaje ya ɗau wayar Yadikko yai mata ƙaryar ze saka mata kati, ya nemo lambar Imran ya tura masa lambar Amira ba tare da kowa ya sani ba.

Imran yana cikin shiryawa sega Khalid yazo ya sameshi, bayan sun gaisa yace "malam wannan kiran ujula haka? Meke faruwane ma zamuje yi a kano haka da gaggawa?"

"Waccan yarinyar zamuje in ɗakko a Kano, tun bata janyomin abun kunya ba"

Khalid yai murmushi yace "inye kaga angon mata biyu, kace amaryarka za kaje ka ɗakko?"

"Wai wace amarya malam, ance maka an bada sanarwa 'yan sanda su nemota, taci kuɗin wani mawaƙi? Shiyasa nake son mu hanzarta in ɗakkota Kafin su cin mata a can su ɗauketa ace zan auri macen da aka kai Police station"

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now