WUTA A MASAƘA 23_24

813 58 6
                                    

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of

*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.

23_24

Imran na fita Amira Tayi tsaki, ta kwanta akan gadonta taja bargo, kwata kwata da ta tuna dukan da Imran yai mata se taji ta tsaneshi bata ƙaunar ganinsa.

Imran kuwa a harabar gidan ya tarar dasu Abba, sukayi Sallama dasu Alhaji Hashim suka tafi.

Suna dawowa cikin gidan, Anty Nafisa ta tafi ɗakin Amira, tana shiga tai sallama Amira ta amsa, Anty tace Amira tashi zaune Magana zamuyi.

Amira ta tashi zaune, Anty ta zauna kusa da Amira tace "Amira wace irin sallama kukayi da mijinki ne?"

Amira tace "mijina kuma?"

"Eh mijinki Imran mana" ita Amira mantawa take wai Imran yanzu mijinta ne, idan ma aka faɗa se taji wani banbarakwai.

Maimakon ta bata amsa se tayi shiru ta sunkuyar da kai.

Anty tace "Amira, duk da Imran ba sonki yake ya aureki ba kefa zaki nemo soyayyar nan da kanki"

Ɗan tura baki Amira tayi a ranta tace "ji wata Magana mara ma'ana, ni zan bishi ya soni lallai"

"Ki dena tura baki, kamar yadda na gaya miki ke zaki nemo soyayyar nan da kanki, sannan karki kuskura ki kuma ce masa mugu, ko yana cin zalinki yanzu mijinki ne shi, ki manta da abunda yafaru gaba ɗaya, ki fuskanci rayuwarki, banda gaya masa baƙar magana ko abunda ze tunzurashi, ko kin fiso ya sakeki ki zama ƙaramar bazawara?"

Ba Kunya Amira ta ɗaga kai alamar eh, "au kin fiso ki zama bazawara, ya sakeki?"
Amira ta kuma jinjina mata kai alamar Eh.

"Lallai Yarinta na ɗawainiya dake, amma meyasa kike so ya sake ki?"

"Ni wallahi ba irinsa nake so in aura ba, bashi da tausayi"

"To ke wane iri kike so?"

"Irin mijin Anty Fa'iza nake so"

Anty tai murmushi tace "wane iri ne wai wannan mijin na Anty Fa'iza?"

Amira ta gyara zama tace "kinga fa shi mijin Anty Fa'iza yana lallaɓata sosai, gashi da sauƙin kai, yana da matuƙar haƙuri, kuma yana son yai abunda ze burgeta, gashi da fara'a da yawan murmushi, amma ba irin wannan Imran ɗin ba da ko dariya bayayi"

Wani ƙasaitaccen murmushi Anty tayi, ta fuskanci Amira 'yar soyayyace tafi son wanda ze dinga lallaɓata yana biyewa taɓararata.

Ta kalli Amira tace "Ai baki san wani abu ba, sufa maza tamkar yara suke a gurin mace, duk yadda kika so zaki sarrafa su, amma bata ƙarfin tuwo ba ta hikima da rarrashi, idan kin so seki maida Imran ɗin irin yadda kike so"

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now