39_40

885 45 4
                                    


🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of

*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.


39_40

Shiru Imran yai be ce komai ba, Ammi ma ba tace uffan ba, jira take suje gida ta tabbatar idan da gaske Abba yake Wannan maganar.

Gidan Imran suka nufa kai tsaye,aka ajiye Imran da Amira, Amira tace zata bi Alhaji Hashim su koma gida, yace "wani gidan kuma Amira?"

"To ai ban gayawa Anty zan zauna ba, kuma bani da lafiya"

"Ai ga magnin nan ya dawo, kije ki kula dashi, zamu dawo muyu masa sannu da zuwa ta mussaman".

Ammi se hararar Amira take, Amira ta nuna kamar bata ga me Ammin take ba.

Suka shiga cikin gidan, ɓangaren Ihsan a rufe na Amira ma haka, Amira ta duba Kitchen ɗin falo, ta ɗakko mukulli, ta buɗe part ɗinta, ta kalli inda Imran ya zauna a kan kujera, tace "Naga Ihsan bata nan, bari in haɗa maka ruwa kai wanka".

Jinjina mata kai yayi, ba tare da yace komai ba, taje ta haɗa ruwan ɗumi a banɗakin bedroom ɗinta.

Ta fito falo tace "Captain bisimillah na haɗa"

Ya miƙe yabi bayan ta, yana cike da mamakin ina Ihsan ta tafi haka? Ba ta san da dawowarsa bane ko kuwa me hakan yake nufi?

Duk da ta kwan biyu ba ta gidan, amma komai nata tsaf da shi, Imran ya samu ruwan ɗumi, yai wanka kan ya fito har ta shiga Kitchen, ya zauna a gaban mudubi yana ƙarewa kansa kallo, shi kansa yasan ya rame, saboda anyi gwagwarmaya a dajin nan.

Amira ta shigo zata masa magana amma tai turus tana kallonsa, se taga kamar ba shi ba, ya zama wani ƙato sosai.

Ya kalleta yace "Ya dai?"

"Amm bakomai, da..daama zance ne, in kawo maka Abinci nan in na gama?"

"No zan zo nan falon in ci" ya faɗa a taƙaice.

Ya fito Falo, ya buɗe jakarsa ya fito da wando na sojoji da shirt ya saka, Amira ta zo ta ajiye masa kayan Abinci, ta haɗa masa tea, da dafaffiyar doya da miyar ƙwai.

Yadda Imran yake zura Abincin nan a tumbinsa, zaka san lallai ba ƙarama wahala yaci ba, Amira se kallonsa take kamar ba ta taɓa ganinsa ba, ita tausayinsa ne ma ya dinga kamata, duk yai duhu.

Amira tace "Sannu"

Imran ya jinjina mata kai kawai, ya cigaba da zura Abincin sa.

Kallon gefen kafaɗarsa tai tace "meya sameka a nan?"

"Bullet ne" ya bata amsa.

"Harbin ka akayi?"

"Eh harbi ne"

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now