51-52

1K 54 7
                                    


🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of

*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.








51_52

Gaban Abba ya faɗi amma ya dake, cike da jarumta yace "ok to shikenan ba damuwa, zan kira insha Allah"

Ya ajiye wayar, Amira ta kalli Abba tace "da shi kake waya ko? Ka bani in masa Magana"

Abba yace "ba dashi nake magana a waya ba, wayarsa ba ta shiga amma insha Allah zan masa magana yazo da kansa ya ganki"

Amira ta jinjina kai tana share hawaye.

Sukai musu sallama suka tafi.

Gaba ɗaya Amira ta zama ita ba me hankali ba, ita ba mahaukaciya ba, se ana zaune lafiya seta birkice gaba ɗaya ta fara sambatu.

Jikin Abba gaba ɗaya a sanyaye yake, suna tafe a hanya Ammi ta kalli Abba tace "lafiya kuwa? Naga duk jikin ka a sanyaye?"

Abba yace "lafiya ƙalau, kawai yanayin jikin Amira ne ya ɗagamin hankali gaba ɗaya"

"To ai Addu'a za kai mata Allah ya bata lafiya, bawai ka ɗaga hankalinka ba kasan kaima ba cikakkiyar lafiya ce da kai ba"

Abba yace "hakane, Allah ya bata lafiya"

Haka suka tafi gida, jungun jungun kamar masu zaman makoki.

Minal tana falo tana kallo suka shigo, bayan Abba ya wuce ne Minal ta kalli Ammi tace "Ammi, lafiya naga Abba a haka, me kuma ya faru?"

"Mhmm ke ni duk yadda nake tunanin lamarin Yarinyar nan abun ya wuce nan, abun nata ma dai gashi nan kamar hauka ne dai ya kamata"

"Hauka kuma Ammi?"

"Eh hauka mana, banda haka me zesa ta dinga zabure zabure tana ihu, wai ƙadangaru take gani, hadda ƙoƙarin yin tsirara?"

"Taɓɗijan kuma fa hakane, Yanzu shikenan ta haukace kenan?"

"To waye yasan mata? Amma abun nata ma hadda Iskanci, daga gani na ta hau kuka wai na hana Imran zuwa gurinta, salon ta haɗamin wata kutungwilar"

"Kuma dai? Anya ba ƙarya take ba tana sane take wannan abun? In ba haka ba meye dan ta ganki zata fara kuka tace kin hanshi zuwa gurinta"

"Oho ita ta sani, inma gaske take inma ƙarya take ita ta shafa"

"Ba fa abunda ba zata iyayi ba, kin san tsohuwar karuwa ce, ba duniyanci ko pretending ɗin da ba zata iya ba, gara ma ai hakan Ammi sa rabu salin alin kinga base kin kashe Auren ba, tunda baze zauna da Mahaukaciya ba"

"Hakane, dan nima ba zan lamunta ba sam, tunda ta haukace se a raba Aure ga uban ciki tana fama ga hauka"

Minal ta ɗan taɓe baki tace "Allah ya kyauta, hadda alhakin Anty Ihsan ma da suke ɗauka"

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now