Kauthar 4

513 30 17
                                    

✿✿KAUTHAR!!✿✿

✪✪°04°✪✪

Kauthar | Babi Na Hudu https://hikaya.bakandamiya.com/kauthar-babi-na-hudu/

Bata san ko wacece mahaifiyarta ba, bata san dangin mahaifiyarta ba. Tana da dan insight na mahaifiyarta a lokacin yarintarta kafin batan mahaifiyarta.
Tana tuna daren da abin ya faru daki-daki, a kowane lokaci a cikin rayuwarta. Ta yaya ma zata manta da wannan rana? Bayan koda yaushe ta kasance cikin mafarkin abinda ya faru?!

Tana tuna irin kauna da soyayya da iyayenta suka nuna mata lokacin da tana yarinya. Amma suma wadannan in pieces take ganinsu, vividly.

Abinda tafi tunawa sosai kuma da kyau, shine lokacin data farfado daga hatsarin daya rutsa musu, wanda kuma ya tarwatsa mata rayuwa. Da kuma abubuwan da suka faru bayan nan.

Ta bude idanune ta tsinceta a gadon asibiti, kunnenta na dama yana mata wani masifaffen zugi da wata irin kuwwa kamar an jona shi da amsa kuwwa.
Ta yunkura zata tashi, taji kafarta ta dama ta amsa, wani azababben zafi ya ratsata har sai data saki ihun azaba.

Aka tura kofar dakin da sauri aka shiga, ta juya tana kallon matar data shiga fuska dauke da alamun rashin sanayya.
A kallon farko babu kari, zaka tabbatar da cewa matar ta hadu gaban kwatance, kuma ilimi da wayewa sun ratsata ta kowane bangare. Cikin shiga take ta mutunci irinta hausawa, abinda bata saba gani tattare da mahaifiyarta ba. Kullum cikin kananun kaya take, babu canji.

Ta nufeta da alamun damuwa da kulawa akan fuskarta, ta taimaka mata ta zauna tare da jingina mata filo a bayanta ta kuma kara mata wani a kasan kafarta inda sai a lokacin ta kula da cewa kafar sangale take a jikin wani abu.
Tace, "sannu Kauthar, ya kike jin jikinki?"

Bata iya bata amsa ba saboda bata jinta sosai, sama-sama ta dinga jinta kamar a cikin ruwa take, ga kuma rashin saninta da bata yi ba don daga ganinta dai ba nurse bace.

Matar taci gaba da watsa mata tambayoyi, amma Kauthar ta rasa bakin amsawa. Ta kuma kasa daga baki ta tambayeta ina Mamanta da Babanta kamar yadda take so tayi saboda yadda bakin nata yayi nauyi sosai.

Cikin ikon Allah sai ga Baban nata ya shiga dakin da sauri, likitoci biyu suna binshi a baya. Kamar wadda take jira, tana ganinshi sai taji ta saki kuka. Matar nan ta jata jikinta da sauri tana lallashi da bata baki, ta hau fuzge-fuzge har ta samu ta janye daga jikinta ta fada jikin Daddynta tana rizgar kuka kamar ana zare mata rai.

Likita ya matsa ya dubata tana daga jikin Daddyn kamar wadda take tsoron a rabata dashi, ya tabbatar musu da cewa lafiyarta lau, kuma za a iya bata abinci, ya tafi ya barsu a nan.

Ba ita ta samu bakinta ba sai bayan da aka yi mata allura, zogin kunnenta ya ragu, matar nan ta goge mata jiki da towel da ruwan dumi, ta taimaka mata tayi brush, ta bata abinci mai ruwa da madara, duka Daddy yana zaune a gefen gadon yana kallonsu, kafin ta iya daga baki ta tambayeshi,
"Daddy, ina Mommyna?!"

Shi da matar suka hada idanu, ya rankwafa ya dafa kanta adoringly, "baby, Mamanki tayi tafiya ne amma babu dadewa zata dawo, meanwhile, wannan ita ce new Mom dinki, understand?!"

Sai ta girgiza kai maimakon gyadawa, don kuwa bata fahimta ba. Kamar ya Mamanta ta ainihi tayi tafiya amma kuma tayi wata sabuwa cikin dan kankanin lokaci? Kwalwar Kauthar a wannan lokaci bata fahimta ba, kuma ba zata fahimta ba sam.

Ya zauna a gefen gadon tare da kara janta cikin jikinshi, "ina nufin itama wannan kamar Mommy dinki ce, yadda zaki kira Mamanki 'Mommy', itama haka zaki kirata. Sannan ina so ki dinga jin maganarta da kyau".

Ta daga baki tace, "to ita din wacece ita, Daddy?!"

Suka sake yin musayar kallo, "Matata ce ita, kuma zata koma gidanmu, mu zauna tare da ita. Kina so ko?"
Nan ma ta sake girgiza kai, daga nan kuma bata sake daga baki tayi magana ba har garin Allah Ya waye.

KAUTHAR!! Where stories live. Discover now