UKU-BALA'I=14

1K 49 1
                                    

UKU-BALA'I

NA

KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA GOMA SHA HUDU.

Hannu bibbuyu ta zabga tagumi idanuwanta kan Mu'azzam. sosai take kallonsa tana jin wani irin abu na sauka kan zuciyarta da ruhinta, sosai take jin wani abu mai kama da ruwa yana kwaranya a ko wani sashi da loko na ma'ajiyar zuciyarta, komai take ji yana yi mata wani iri sosai take jin kauna da so mai girma na saukar mata akan kaninta ba abin da take nisawa a ranta sai yarda duniya lokaci guda take shirin juye mata da wata irin ƙaddara mai girma a rayuwarta. sosai take jin duniyar na wargajewa da dukkan wani farinciki mai girma, da ta san tana samu cikin kankanuwar rayuwarta.

Ya za tayi kenan in ta rasa wadannan madogaran rayuwarta ta mai duniyarta za ta kwaso mata in ta rasa wadannan mutane masu matukar muhimmanci a duniyarta.

Wasu hawaye masu zafi matuka taji suna sauka akan fuskarta da can cikin zuciyarta da ruhinta.

Ta sani kuma ta dade jimawa cikin duniyarta ba ta da sa'a a rayuwarta domin kuwa sosai ta fuskata ƙaddara mai kaifi ce ta fado mata da abubuwa masu matukar tashin hankali da yankewar farinciki Babanta ya tafi ya barta ga Ummanta bata da lafiya ga karamin kaninta wanda shi ƙaddara ta sunkuto shi cikin wannan duniyar mai dauke da kwamatsai rashin dadi ina ma tana da dama ina ma tana da iko ina ma ta san zai fado duniyar nan a haka da bata yarda ba da bata amince ba ina ma ace ana tuntuba kamin a sako dan'uwa duniya da ta roki ubangiji bai sako kaninta ba sai dai ba yarda ta iya komai na Allah tabbatacce ne a duniyar dangin rai kana naka yana nashi.

Hannu ta sanya tana mai dauke zafafan hawaye da take jin su a ko ina na sashin zuciyarta tana dauke su wasu na biyo bayan su tana jima cikin wannan yanayin kafin ta motsa ganin Mu'azzam yayi barci ta kai shi makwancinsa ta kwantar bayan tayi Hugging din sa a ko ina na fuskarsa sosai take jin kauna mai girma a tsakanin ko ina na sassan jikinta akan shi sosai take hango wa a duniyar nan bata da kowa dangin yan uwa sai shi dole ta kula dashi dole ta so shi domin shi kadai ne take zaton zai shafe duk wani daci da kunci da ukuba da take ji a zuciyarta na rashin yan uwantaka.

A hankali ta fara takawa har inda Umma take kwance ta na barci hankali kwance kallo daya zakayi mata ka tabbatar akwai alamun warakar natsuwa a tare da ita.

Idanuwanta sosai ta buɗe akanta tana kallonta kamar wacce aka ce in ta dauke idanuwanta za a gudu da ita zuciyarta taji tana wani amsawa da wasu abubuwa mabambanta wanda ita kanta ba za ta ce me nene ba.

Wani murmushi ya subuce mata kalaman Dr.Karami suke mata yawo a kunne a jiya bayan ya zo ya duba Umma.

****

Kallonta yake yi sosai yana yawatawa da idanuwansa masu wani irin yanayi mai matukar kashe jikin wanda ake kallo sosai take jin kallon nasa na shiga duk wani sassa na jikinta yana haifar mata da wasu abubuwa wanda ba ta san a mizanin da za ta ajje su ba sosai take jin bugun zuciyarta sosai take jin yarda zuciyar ta ta take tsalle a duk wata dakika daya na kallon da Dr.Karami yake yi mata ta rasa mai yasa take jin haka ta rasa dalili lokaci da dama ana kallonta mutane masu muhimmanci a idanuwanta amma bata jin haka sai a kansa shi kadai kwallin kwal!.

"Mariya".

Yarda Dr.Karami ya ambaci sunan sai taji aduniyar rayuwarta bata taba jin wanda ya kira sunan da wani irin yanayi mai matukar amsa kuwwa a kwakwalwa da kashe jiki da sanya zuciya tsalle tsalle kamarsa ba sosai take jin duk wani sashi na jikinta na wani irin amsawa da narkewa kamar ana narka roba a wuta wani numfashi take ja mai matukar girma wanda take ji kamar in har batayi jarumtar jan sa ba numfashin katsewa zaiyi daga gareta kanta a kasa tana faman wasa da kasar rigar atamfar ta da take jikinta wanda kallo daya zaka yi mata kasan taji jiki sosai da sosai.

UKU BALA'I (Completed)Where stories live. Discover now