44=UKU-BALA'I

316 25 1
                                    

Sosai ta shiga tashin hankali cikin lokaci kankani ta rasa mai yake mata dadi a filin duniyar nan komai ya kara kwance mata tashin hankali ta ya kara hawa mataki mai girman gaske bata san me za tayi ba bata san mai ya kamata tayi ba lokaci tafiya yake komai kara kusantowa yake yi har zuwa wannan lokacin ta rasa mafitar da zata samu don cimma burin ta ba tare da auranta ya tabbata da Dr.Erena.

Numfashi take ja cikin sauri-sauri tana faman juyi saman faɗaɗɗen gadon ta wanda take jin sa kamar kan garwashin wuta take kwance komai na duniyar take ji yana yi mata k'iwa baya son ta da farinciki ko yaya ne.
Zuciyarta na ta hasaso mata cewa 'ta kashe shi ba tare da kowa ya sani ba' amma ta kasa tana tsoron haka ba kisa a tsarin daukar fansanta bata so ace wani abu ya gifta a tsakaninta da shi wanda zai sanya ta zama sanadin kashe shi tsoro take ji tsoron abin da zai je ya dawo tsoron yawan zunubansa da zai dawo kanta tana tsoron mutuwarta bata shirya ba ba zata iya ba.

'to ki kashe kanki tunda baki shirya auren dashi ba'.

Zuciyarta ta sake bata wani zaɓin na daban wanda yayi matukar girgizata lokaci guda ta shiga girgiza kai kamar wanda ya fada mata maganar a gabanta yake ba zuciyarta ba wasu hawaye ne masu dumi taji sun zubo mata sosai take jin kunci da matsi cikin zuciyarta sosai take jin zuciyarta na mikata wani mataki mai tashin hankali sosai take jin zuciyarta na buɗe wani wagegen ciwo mai girman gaske.

Runtse idanu tayi sosai tana jin yarda jijiyon kanta da na cikin idanuwanta ke wani irin murɗewa da tashin hankali tana jin yarda wani irin raɗaɗi da zafi ke samun mazukunni cikin idanuwanta mikewa tayi daga kwance da take tana buɗe idanuwan nata hannaye bibbiyo ta zabga tagumi tana kallon yanayin DUHUN DARE da ya mamaye cikin dakin bata ganin komai ko jikinta bata iya hangowa sake runtse idanu tayi kafin ta sauke kafafuwanta a gefen gadon tana kai hannunta wajan fitilar dake girke gefen gadon kunnawa tayi haske ya wanzu sosai ta ko ina dakin ta shiga bi da kallo kafun ta mike saman kafafuwanta da take jin su kamar za su watsar da ita zuciyarta na ta karanto mata huɗubobin da suke kara caza mata kwanya.

Maganganunta da Alhaji Abdulwahaab ne suke dawo mata a jiya da rana inda yake kara karfafa mata gwuiwa amma tana zillewa.

*****

"Ban san mai zan ce miki ba kuma Areefa da farko na dauko za ki zama jaruma mai dakakkiyar zuciya wajan cimma fata da burin da kike dashi a zuciyarki amma gabadaya duk wannan fatar da burin naki ya rugeje lokaci guda ban san mai yasa ba Areefa ban san mai yasa kike kaunar jinkiri a wannan lamarin ba dama ce sau daya take zuwa in kuwa ta kubuce da wuya WATA DAMAR ta sake zuwa".

Cire hannayenta tayi daga tagumi tana mai runtse idanu kafun ta buɗe su sosai tana dubansa zuciyarta na kara narkewa da lamarin Aurenta da Dr.Erena.

"ba wai na cire burin fata na bane akan Dr.Erena ba ba abin da ya canza...".

Ta fadi dakyar tana jan numfashi kafun ta dauki Glass Cup mai dauke da sanyayyan ruwa ta kai bakinta ta kurba ba wai don jin dadi ba a,a domin kuwa ji take yi kamar ta kurbi maɗaci a dandanon da harshenta ya bata runtse idanu tayi ta hadiye shi dakyar kafun ta buɗe tana dubansa shima idanuwansa na kanta.

"ina son fatana a kansa ya tabbata amma wannan lamarin da aka kawo min ne nake jin kamar zuciyata ba zata iya hakura ya tabbata ba".

Mikewa yayi kan kafafuwansa yana binta da wani irin kallo kafun yayi taku kadan ya goya hannayensa a bayansa.

"ko RIGAR SILIKI haka ta ganki ta barki Areefa ana taroki ta nan kina watse wa ta can ban san mai yasa ba...ko da yake shikenan amma ki sani auren ki da Dr.Erena shi ne mafita kuma ita ce hanyar da zaki bi domin cimma burinki kamar yarda Hajiya Layla ta fadi bana tunanin zata cutar dake ko da cikin rashin sani ne ki sani baki da wata a duniyar nan ita ce uwarki da ubanki baki da mai kaunarki kamar ita ba zata taba yin abin da zai taba miki rayuwa ba kuma kema kin san haka don haka ya kamata ke ma ki yaki ce duk wani k'i da zuciyarki take nuna miki ki koya mata hakuri da juriya".

UKU BALA'I (Completed)Where stories live. Discover now