46=UKU-BALA'I

363 29 3
                                    

Zuciyarta zafi take sosai kwanyarta sai kokarin kamawa da wuta take yi ta rasa komai nata mai armashi ta rasa duniyar guntun farin cikinta dake rayuwarta sosai take cikin yanayin kunci zuciyarta sai faman yayyagewa take yi da girman tashin hankalin da take ciki kuka ya daina samun gurbi a idanuwanta HAWAYEN ZUCIYA su ma kan su sun dai samun gurbin zuba komai ya kafe komai ya daina samun numfashi mai kwari daga gareta ba ta san ya zata

kwatanta wannan lamarin ba bata san ya zata dauke shi ba bata san mai yasa duniyarta take kokarin yamutsewa ba koma tace ta ya mutse ALKALAMIN KADDARA yayi rubutu mai tsauri akanta bata yi tsammanin rayuwarta zata kare a haka ba farin ciki babu shima kwanciyar hankali babu komai da komai babu kawai dai...

Wani irin kartawa zuciyarta tayi da hanzari ta mike daga kwancen da take tana sanya hannayenta duk biyu tana dafewa idanuwanta a runtse kamar wacce ake sokawa karfe mai tsanani jar wuta a jikinsa numfashi take da kyar tana jin kirjinta na kara tsananta bugawa mikewa tayi kan kafafuwanta tana faman cizon laɓɓa kamar zata fizge su daga mazauninsu.

Kai kawo ta shiga yi cikin dakin a hankali tana duban su Umma da suke barcinsu cikin kwanciyar hankali ba tare da matsala ba sosai take tausayin kanta sosai take ganin kamar ita kadai ce a filin duniyar nan take cikin tashin hankali gani take kamar ita kadai ne so yake bugawa yadda ransa ke so kamar wata ball bata san ya zata dauki AL'AMARIN SO ba a filin

rayuwarta bata san ya zata kwatanta bala'in da fada ba A DALILIN SO ba tana shakka akan cewa so yana da dadi gaskiya ba za ta amince da haka ba so guba ne ba komai ba.

Haka tai ta safa da marwa a tsakar dakin har zuwa wani lokaci mai tsayi cikin DUHUN DARE ba tare da ko yaya ne barci ya so kama ta ba in aka ce ma barci zai zo wajan ta zata karya ta domin kuwa ita a karan kanta ta manta yaushe rabonta da yin barci mai ansa suna barci...

"Ke Mariya wai lafiyarki kalau kuwa?".

Kamar daga sama taji muryar Umma a dan razane ta juya ta dube ta zaune ta hangi Umma ta kafeta da idanu kafun ta cigaba da fadin.

"Ke yanzu fisabilillahi kina ganin haka ya dace miki Mariya kina zaton wannan abin da kike yi shi ne zai zame miki mafita a filin duniyarki bana zaton haka wannan damuwar da kike shiga ba karamar matsala zata jefa ki ba ke ko fada ba zakiyi wa kanki  ba yaushe ki ka farfaɗo daga ciwo wa yayi zaton ma za ki sake WATA RAYUWA a duniyar nan".

Rausayar da kai tashiga yi cikin rashin abin cewa ta sani duk maganganun da Umma take fadi akanta gaskiya ne amma ita bata san ya zata koyi duk wannan abubuwan ba zuciyarta sosai da sosai take zafi sosai take cikin tashin hankali wanda ba ta san ya zata kwatanta shi ba.

"Zo ki zauna muyi magana".

Cewar Umma cikin Muryar rarrashi da tausayin 'yar tata a hankali Mariya ta ja jiki ta isa kusa da ita ta zauna kafun ta dago ido ta dubi Umma jikinta ya shiga rawa kamar wata mai jin sanyi.

"Umma ina cikin bala'i ban san ya zan kwatanta shi ba bana zaton na shigo duniyar nan a nasara bana tunanin akwai wata rayuwa da zan yi har karshen numfashi na bayan wannan...".

Sosai tausayin ta ya kara rikita zuciyar Umma nan da nan ƙwalla suka tarun mata a ido bata bari Mariya ta gani ba domin kuwa ita ta san halin da take ciki akan duk matsalolinta amma bata nuna mata ba ta son abin da zai kara dagula mata lissafi dakatar da ita tayi.

"ki daina fadin haka Mariya na sha fada miki duk abin da ki ke ganin yana faruwa da baya dama tun fil'azal ALKALAMIN KADDARA ya zana masa haka a KUDINSA don haka Mariya ke daina cewa ke ce kika fi kowa rashin rabo a duniyar nan ke taki matsalar kika sani in da zaki ga na wani zaki sha mamaki zaki ce ke ba komai bane ya same ki godiya zakiyi wa Allah duk wannan abubuwan suna cikin KUDIN JARABAWARKI...".

UKU BALA'I (Completed)Where stories live. Discover now