48-UKU-BALA'I

370 29 3
                                    

Cikin kwana biyun da tayi bayan haduwarta da Dr.Karami gabadaya ta gama rikiciwa ta rasa mai ke yi mata dadi a rayuwarta zuciyarta sai faman zillo take akan lamarin sa ta rasa ma me za tayi.

A hankali take kokarin saita kanta da samo mafitan da take ganin ya dace da ita sosai take hana idanuwanta barci tana kai kukan ta wajan Allah domin ya zaba mata abin da yafi zama alheri a rayuwarta baki daya.

Sosai zuciyarta ke matsewa sosai take jin nauyin da zuciyarta ke yi yana raguwa a hankali sosai take jin ya kamata ace izuwa wannan lokaci ta sarara wa kanta da rayuwarta sosai take jin lokaci yayi da ya kamata ta kawo karshen komai.

Amma ta yaya hakan zai kasance ta yaya hakan zai yuwu ba ta san ya za tayi ba sosai zuciyarta ta karkata zuwa ga Dr.Karami yawancin barci in tana yin sa duk shi take hangowa amma bata jin za ta iya aurensa.

Amma kuma bata san dalili ba in maganar aure tafi karkata ga Dr.Aqeel tana son Dr.Karami shima Dr.Aqeel tana jin son sa sosai a ranta ba kadan ba sai dai fili mai yawa Dr.Karami ya mamaye mata.

Haka rayuwarta tayi ta tafiya har tsayin wata daya amma har lokacin bata yanke hukunci ba ta rasa wanda zata tunkaro ta fada masa halin da take ciki domin samun mafita tana tsoron sanar da Umma domin yanzu duk ta ja baya ta bata dama ita akaran kanta tayi abin da ya dace Baseera kuma har zuwa wannan lokaci taki yarda su hadu domin bata son ta zo mata da wani lamarin na daban bata so ta zaba mata abin da ba shi zuciyarta take so ba.

Haka dai ta cigaba da dakon wannan lamarin har da karshe ta yanke zuwa gidan su Baseera domin ita kadai ce k'awa shakikiya da take ganin ya dace ta san matsalar kuma ta bata shawarar da take ganin ya dace.

Sanye take cikin daguwar riga mai kalar baki da ratsin ja kadan ta sanya jan gyale tayi rolling din shi a kanta sosai ya fito mata da kyanta duk da ba wata kwalliya ba ce ta a zo agani tayi amma tayi matukar kyau takalmi flat ta saka a kafarta sannan ta fito tsakar gida ta tadda Umma zaune ita da Mu'azzam duban su tayi su duka kafun tayi murmushi wanda iyakarsa fuska tausayin kanta da na Umma hadi da na kaninta kawai take ji tunowa da tayi da mahaifinta ko yana ina a halin yanzu Allah masani.

Numfashi ta ja mai tsayi har sai da Umma ta jiyo sautin sa juyowa tayi ta dube ta sosai.

"Lafiyarki kalau kike wannan doguwar ajiyar zuciyar?".

Ta fadi tana kara duban jikinta.

Gyaɗa kai tayi tana sake kokarin kakalo murmushi duk da kwallar da ke kawo mata farmaki a idanu.

"Ba komai kawai dai...Uhmm yawwa Umma zani gidan su Baseera".

Kallon tuhuma Umma ta shiga yi mata na dan lokaci kafun ta gyaɗa kai.

"Allah ya kiyaye hanya ki gaida mutan gidan amma karki dade fa kin ga yamma ta fara yi".

Ansawa tayi da 'to' sannan ta dubi Mu'azzam da yayi kuri yana dubanta dakune masa fuska tayi cikin tsokana.

"Yah Mariya zan biki".

Ya fadi cikin sanyin murya zaro idanu tayi waje.

"Ni zaka bi caɓ! gaskiya a,a ba zan iya jigilar zuwa da kai ba ban son kaje gidan mutane kana yi musu rashin ji ka bar ni da jin kunya".

Ta fadi tana mai kama hanyar ficewa rau-rau yayi da idanu kamar zai yi kuka amma Umma ta hana shi ta shiga rarrashin sa.

UKU BALA'I (Completed)Where stories live. Discover now