67=UKU-BALA'I

449 29 0
                                    

Gumi ne kawai ke ta faman keto mata kamar wacce aka juyewa diron ruwa sai faman yamutse fuska take yi tana cizon laɓɓa gabadaya ta gama galabaita ta fice daga hayyacinta lokaci-lokaci take ajiyar zuciya ita kadai tasan bala'i da masifan da take ciki yau kusan kwana uku kenan tana jin ciwon a tsaitsaye amma na yau ya shafe na kwanakin da tayi.

Jikinta har karkarwa yake yi buɗe idanuwanta tayi da suke runtse sun kaɗa sunyi jajir jijiyoyin goshinta sun fito sosai kamar shirya su akayi kan fatar goshinta hawaye ne suka

kwaranyo mata karo na ba a dadi duban dakin tayi gani take yi yana juya mata sama na dawo kasa kasa na dawo sama sake runtse idanun tayi gami da yin wani yinkuri da ya sanyata sakin wata kara mai razanarwa kafun lokaci guda tayi luf! kamar ba ita bace tayi ihun ba.

Goggo Marka ce ta fado dakin cikin hanzari tana dubanta ganin yanayin da take ciki ya sanyata saurin isa gareta rikota tayi tana faman

duddubata kafun lokaci guda ta gano abin da ke wakana da sauri ta gyara mata zaman dirshan da tayi tana mai rike mata kafadu da sauri ta fizge kanta daga hannun Goggo Marka tana faman sakin wani wahalallan numfashi hawaye sai ambaliya suke mata a fuska.

Sake kai hannu tayi zata rikota a daidai lokacin cikin nata ya sake juyawa wata irin zabura tayi gami da wancakalar da ita gefe guda kan ta ya hadu da gadon karfen dake gefen su  da sauri ta ja da baya tana riko goshinta don sosai ta bugu lokaci guda wajan ya kumbure sosai duban Hafsat ta shiga yi idanuwanta suna kawo kwalla gabadaya ta gama rikicewa kanta gabadaya ya gama shiga duhu tunda Hafsat ta fara

nakudar nan a tsaitsaye hankalinta ya kai kololuwa ba ta san lamarin zai kai ga haka ba wai yau Hafsat ce za ta haife musu abin kunya ɗan shege na gaba da fatiha ba ta taba dana sanin wannan lamarin da kaico ba kamar yau zuciyarta gabadaya ta gama karyewa da tashin hankali bata san yarda za tayi ba bata san wa za ta kai wa kukan ta a daidai wannan lokacin ba kowa ya juya musu baya

musamman Abulle da gabadaya ta dauke musu kafa ta daina bi ma ta kansu ga gidan yanzu ita kanta kunyarsu take yi ta rasa dalili ko da yake ita kadai ta san abin da ta aikata a garesu sosai take jin zuciyarta na kara karye da komai na duniyar ma.

Ihun da Hafsat ta kuma yi ne ya sanyata dawowa hayyacinta dubanta ta shiga yi a tsaye take sai faman ya kice kayan jikinta take yi tana jifa dasu laɓɓanta cikin baki sai faman cijesu take yi kamar ba a jikinta ba idanuwanta a rufe da sauri Goggo Marka ta ja gefe ganin al'amarin ya girmama waje tayi da hanzari tana faman hada hanya Umma ce ta fito ta dubeta ganin yanayin da take ciki ya tabbatar mata ba lafiya isa tayi gareta tana riko hannayenta ba abin da jikinta ke yi sai karkarwa.

"Habeeba Ban san abin da ke faruwa da Hafsat ba ga ta can cikin dakin sai fizge-fizge take yi".

Zaro idanu tayi tana ambaton innalillahi wa inna ilaihir raji'un da sauri ta saki Goggo ta nufi daki durkushe ta same ta sai faman nishi take yi ga wani mahaukacin gumi da ta hada gabadaya tayi jagaf! duban kasan ta tayi ganin ruwa na kwarara ya tabbatar mata haihuwa ce da sauri ta fice ba tare da ta taba ta ba can ta hango Goggo sai safa da marwa take yi hannu aka hakan yayi matukar bata mamaki yau kuma girgiza kai tayi gami da komawa daki mayafinta ta dauko ta yi hanyar waje.

Tana sanya kai kofar gida ta hango su da sauri ta yo baya tana mai da numfashi ita gabadaya ta manta ma Mariya na waje lekawa tayi a daidai lokacin ita kuma Mariya idanuwanta na kallon kofar gidan don ta ga lokacin da Umma ta fito ta koma da sauri ya fito ta tayi da hannu sannan ta koma cikin soron sai faman kai kawo take yi don yanayin da ta ga Hafsat a ciki yayi matukar tsorata ta ba abin da ta tuna sai lokacin

UKU BALA'I (Completed)Where stories live. Discover now