PAGE 35&36

257 24 3
                                    

🌸 *HASEENAH*🌸

Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303

Follow me on wattpad@Aysherabbakar

*Long Live Pml*

*Dan Allah ina me bada hakuri na jina shiru da akayi na wasu 'yan kwanaki, hakan ya farune sakamakon rashin wuta da aka samu, na gode sosai da dakuwarku da kulawarku kaina, wa'yanda suke kirana da masu bina pc na gode sossai expecially meerah novels, I love u guyx much much Allah bar zumunci*

*35~36*

Wuta ne ya bi Haseenah sakamakon buɗe k'ofar da tayi, da sauri ta ja da baya haɗe da salati.

Haseenah na jin salatin Umman ta amma ba halin fita dalilin zafin wuta da hayak'in da ya cika d'akin, tun tana jiyo ummah har taji shuru.

Zubewa tayi wajan tana kuka tana faɗin " wayyo ummah na wayyo Aaman"

Tari ne ya turnuk'e Haseenah, kafin kace meye itama wuta ya mamaye d'akin ta.

Hakan yayi dai dai da dawowan Abba daga masallaci, Mummy na ganin shi ta daka tsalle ta hau kurma ihu tana birgima, ihun tane ya tada Saratu daga barci.

Da gudu ta fito dan ganin abinda ke faruwa, ganin wuta na tashi a side d'in Ummah ya sa Saratu ihu tana faɗin" Mummy Umman Haseenah a ciki"

Abba ko ganin wutan na dad'a tashi ya sashi fita da gudu dan neman d'auki.

Watsa ruwa ake da k'asa amma kamar fetur ake dad'a zuba wa.

Hakan yasa wani mak'wabcin su kiran fire service.

Mummy Zuwaira kuwa tunda tayi asuba ta kasa zaune ta kasa tsaye, haka haseen ma, shi mafarkin Haseenah yayi ta faɗa rijiya.

Hakan yasa shi kasa nutsuwa ya d'au makullin motar shi ya nufa gidan.

Isowar shi yayi dai dai da isowar Mummy Zuwaira.

Ganin mutane cike a gate d'in gidan ga motar fire service yasa Mummy Zuwaira firgice wa.

Haseen kuwa cike da tashin hankali ya fara ture mutane yana kutsawa ciki Mummy Zuwaira na bin shi a baya.

Ganin wuta na tashi wajan su Haseenah yasa Haseen rugawa da gudu ya nufa ciki.

Ganin ana ta shek'a ruwa ya sashi waigawa yana duba Ummah da Haseenah amma baiga kowa ba.

Mummy ya gani can gefe tayi zaman 'yan bori daga ita sai d'aurin k'irji kanta ko d'an kwali babu fuskanta sha6e sha6e da hawaye da majina tana ihu tana faɗin " wayyo Ni na shiga uku ku ceto rayuwar bayin Allan nan"

Nan Haseen ya fahimci abinda Mummy ke nufi.

Da gudu ya nufa wajan da nufin shiga nan aka rik'e shi, fisgewa yake yana faɗin" ku kyale Ni in shiga in fito da su tunda ku kun kasa ceton rayuwar su"

Rik'e shi sukayi suna faɗin ya nutsu amma ina baima san suna yi ba, ganin basu da niyan sake shi ya sa Haseen fashewa da kuka yayi zaman dirshan.

Mummy Zuwaira kuwa zare ido take tana faɗin" ina k'anwata take? A ina kuka barta? Ku matsa in fito da ita"

Abba ma firgici ya hana shi magana, zare ido kawai yake yana sharce zufa.

Da k'yar aka samu aka kashe wutan.

HASEENAHWhere stories live. Discover now