PAGE 51&52

217 25 0
                                    

🌸 *HASEENAH*🌸

      Story &written
                By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303

Follow me on wattpad@Aysherabbakar

*Long Live Pml*

*51~52*

Kar6ar paper tayi ta duba ta gani, d'agowa tayi tana kallon shi, shima ita yake kallo, mik'a mata biro yayi ta k'ar6a, sake kallon takardar tayi ganin ya rubuta " what's ur name?"

Kasa bashi amsa tayi, ita bata rubuta ba sannan ita bata bashi takardar ba.

A tunanin shi bata gane abinda ya rubuta bane, sake kar6ar paper yayi ya rubuta " ya sunanki?"

Ganin ya rubuta mata da Hausa ya sata murmushi ta k'ar6a ta rubuta" am Haseenah"

Mamaki ne ya kama shi wato dama bata da niyar bashi amsa ne?

Dariya yayi sannan ya rubuta mata" nice name"

"Thanks" ta sake rubuta mishi sannan ta mik'a mishi ta mik'e ta barshi nan zaune.

Binta da kallo yayi ganin tayi hanyan d'akin ta.

To meyasa ta tafi?

Shima mik'ewa yayi ya bar wajan ya fice waje dan shirye shirye.

Kai tsaye gidan Dr Abeed ya nufa nan suka fice tare, wajan processing asibitin Haseenah suka 6ata lokaci, bai dawo ba sai bayana la'asar.

Lokacin kuwa Haseenah ta gama had'a musu lunch, shi ake jira.

Yana shigowa sama ya wuce ya watsa ruwa sannan ya fito suka ci abinci.

Hira suka cigaba dayi, can ya dubi Ammi sannan yace" Ammi kinsan sunan 'yar taki kuwa?"

"Seka fad'a"

Ta bashi amsa as if she don't care.

Yace " sunanta Haseenah"

Da sauri Ammi ta dube shi Tace" ta yaya ka sani? Ko ta fara magana ne?"

"A'a, tanbayarta nayi a takarda nd she replied back"

Da kyau.

Ya sake cewa " she has a nice name ko Ammi?"

"Yea she do"

Ita dai Haseenah kallon su kawai take.

Da ta gaji ma tashi tayi ta bar wajan.

Sameer ne ya sake cewa" Ammi daga ganin ta bata da surutu"

"I think so"

Ta bashi amsa a tak'aice.

Ana kiran la'asar duka suka mik'e suka fice Ammi kuma ta shige ciki.

Lokacin da Haseen ya bar wajan malam iro me gadi kai tsaye gida ya wuce, dan gaba d'aya jikin shi yayi sanyi ganin yanayin sauyin halin Saratu.

Amma sai ya dena mamaki da ya kula Mummy ba abunda zata mata balle ta kwa6e ta.

Yana Isa toilet ya wuce ya watsa ruwa ya fito yaci abinci sannan ya kwanta.

Mummy Zuwaira ce zaune gaban Abban su, ganin yanda ta nutsu da alama maganar me amfani suke yi.

Dubanta yayi sannan yace" Zuwaira naga kaman akwai abinda yake tafe dake ko menene?"

Gyara zama tayi sannan tace" Abba dama kan rasuwar Halima ce, to nasa dai a fara bincike har a gano abinda ya faru"

Shuru yayi ya zuba mata ido sannan yace

" wannan maganar duk bashi da amfani, duk binciken da za'ayi ba dawowa zasuyi ba, sannan inma da hanun koma wanene a ciki nine mahaifin ta, dan haka dan Allah duk muyi hak'uri a bar maganan, addu'a kawai suke buk'ata, dan haka Allah shi zai bi mata hakkin ta, kuma shi zai isar mana, tunda kikaga nayi shuru da maganar to Kuma haka nake so kuyi hak'uri ku bar wa Allah"

Shuru tayi bata sake cewa komai ba, dan dama tasan tunda taga yayi shuru  to tasan abunda zai biyo baya kenan.

Nan yaci gaba da mata nasiha da kuma bata baki har zuciyar ta yayi sanyi, amma ita ba haka taso ba.

Ba yanda ta iya haka ta dawo gida jiki a sanyaye.

Kiran Haseen tayi ta sanar dashi yanda sukayi da mahaifin nata.

Har zuciyar shi ba haka yaso ba, dan yaso ya koya wa Mummy hankali wannan karon, cikin takaici yace" shikenan Mummy, me hali baya fasa halin shi"

Nan sukayi sallama yace zai zo gida ya same ta.

*4 days later*

Yau saura kwana biyu jirgin  su Haseenah ya tashi, dan haka komai da su Ammi zasu buk'ata ta kammala musu, Sameer ma ya d'au hutu wajan aiki dan yace tare zasu tafi.

Mahmud ne dai yace babu inda zashi, dan zama shi kad'ai ma a gidan yace yafi mishi.

Ana gobe zasu tafi Ammi tasa Haseenah ta d'auko kayanta kala biyar, dan tace bazasu d'au Kaya da yawa ba in zasu buk'aci wani abu sa siya a can.

Ita dai Haseenah taga ana ta shiri amma batasan ina za'aje ba, to ina zasu Kaita?duk hankalinta ya tashi, kallo d'aya zaka mata kasan bata cikin nutsuwar ta.

Da sassafe Ammi ta gama had'a musu breakfast, da yake jirgin k'arfe goma zasu bi, tun tara suka gama komai, Sameer ya zuba musu kayan su a Boot sannan suka fito.

Har bakin mota Mahmud ya raka su, hugging d'in Ammi yayi kaman zeyi kuka yace

" Ammi wish u safe arrival, Dan Allah ku dawo da wuri"

Harara ta zabga mishi ta ture shi tace" sakeni da Allah, da kanaso mu dawo da wuri ai zaka bimu"

6ata rai yayi yace" to Ammi Ni mezan je nayi?"

"Ban sani ba"

Ta bashi amsa sannan ta shige mota.

Kama hanun Haseenah tayi suka shiga tare ta rufe k'ofar.

Sameer ya shiga wajan driving, duban Mahmud yayi yace" kana tsaye kana kallon mutane waze dawo da motar?"

Tura baki yayi yace" to bro Baga driver ba"

Shuru ya mishi Bai sake kula shi ba, ganin haka ya sashi ya bud'e motar ya shiga.

Kai tsaye airport suka nufa, basu samu wani hold up ba da yake weekend ne.

9:45 sun isa da sauri sauri suka gama komai,a tare suka shiga jirgin, yayinda Mahmud kuma yake waving musu hannu har suka shige..

Duk kuma sai yaji babu dad'i.

Jiki sanyaye ya juya ya shige motar ya kama hanyar gida.

10am sharp jirgin su ya d'aga zuwa turkey.

To sai dai yanzu muce Ammi, Haseenah da Sameer safe flight🛫.

Plx vote nd comment

For comments only 08144932303

HASEENAHWhere stories live. Discover now