18- Falalar Salatin Annabi

183 6 0
                                    



1- Mazon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:"Wanda ya yi salata daya agare ni, Allah zai yi salati goma a gare shi".

قَالَ النَّبِيُّ صلى الله عليه وسلم: ((مَنْ صَلَّى عَلَيَّ صَلاَةً صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ بِهَا عَشْراً)).

2- Kuma Mazon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Kada ku maida kabari na idi, ku yi salati a gare ni ko ina kuke, domin salatinku yana isa zuwa gare ni ko ina kuka kasance".

وَقَالَ صلى الله عليه وسلم: ((لاَ تَجْعَلُوا قَبْرِي عِيداً وَصَلُّوا عَلَيَّ؛ فَإِنَّ صَلاَتَكُم تَبْلُغُنِي حَيْثُ كُنْتُمْ)).

3- Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: "Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a wurinsa amma bai yi mini salati ba".

وَقَالَ صلى الله عليه وسلم: ((الْبَخِيلُ مَنْ ذُكِرْتُ عِنْدَهُ فَلَمْ يُصَلِّ عَلَيَّ))

4- Kuma manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: 'Allah yana da wadan su mala'iku matafiya a bayan kasa, suna isar mini da sallama daga al'umma ta'.

وَقَالَ صلى الله عليه وسلم:((إِنَّ لِلَّهِ مَلاَئِكَةً سَيَّاحِينَ فِي الْأَرْضِ يُبَلِّغُونِي مِنْ أُمَّتِي السَّلاَمَ)).

5- Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: "Babu wani wanda zai yi mini sallama face Allah ya dawo mini da raina na amsa masa sallamarsa".

وَقَالَ صلى الله عليه وسلم: ((مَا مِنْ أَحَدٍ يُسَلِّمُ عَلَيَّ إِلاَّ رَدَّ اللَّهُ عَلَيَّ رُوحِيَ حَتَّى أَرُدَّ عَلَيْهِ السَّلاَمَ)).

DUA BOOK OF OF A MUSLIMAH ( Hausa Version)Where stories live. Discover now