[5/20, 6:22 PM] 💄Meryerm Abdool💄: 🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇 *_HAD'UWATA DAKE_* 👉🏻🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇( _Base on love story_ )
*Written*
*By*
💄Meryerm Abdool💄
( _Siddiqa_ )© *PERFECT WRITERS FORUM*
*P.W.F**Page* 30&31
Duk yanda Haiydar yaso ya zillewa tafia zuwa Argungu ya kasa samun daman yin hakan saboda Dady yace ba excuse kowa sai yaje, dolensa ya hak'ura.
Siddiqa nauyin fad'an zuwan su Umar tayi saida Umar d'in ya kira Anas ya gayamai shi kuma ya fad'ama Ramlah ita kuma ta kira Aunty ta gayamata (ni kuma nace ina ruwan a aiki kare, kare ya aiki wutsiya).
Itakam Aunty daria ma abin ya bata ta kira Siddiqa tace "ke Baby abu sai kace Budurwar k'auye, ai kin kinajin kunyar mai martaba da mamansu Aysha ai kya gayamin ko? Ko nima kunyar tawa kikeji ne?" Boye fuskarta tayi da tafukan hannunta sannan ta kwasa aguje tayi d'akinta.
Daria kawai Aunty tayi sannan tayi bangaren mama ta gayamata zuwan surukan nasu, murmushi mama tayi tace "wannan zumudin haka kodai dama keda 'yar taki kun matsu ne?" daria Aunty tayi sannan tace "Aa ai zumudin na suriki nane shine ya sakota a gaba" "to Allah ya sanya Alkhairi sai a gayama mai martaba aji ta bakinsa" cewar mama.
"Ameen maman yara, hakan za'ayi sai da anjima idan ya shigo sai a fada masa" hakadai sukata firansu cikin nishadi kaman ba kishiyoyi ba sam ba kyashi a tsakaninsu zamansu gwanin birgewa.
Bayan mai martaba ya shigo da aka gaya masa cewa yayi da wuri haka, akace iyayen yaron ne sukace ya kamata ka kulla zumunci tun yanzu, saboda Dady ya gayama Umar kada ya nuna ya sansu yafison yayi ma aminin nasa bazata, shiyasa ba'agaya musu ainihin dalilin zuwan ba, cewa sarki yayi to ai ba komai Allah ya kawosu lafia, ai duk wanda yaso abinka ya gama maka komai.
Hakan kuwace ta kasance ahalin gidan Alh, Muktar Sadauki sun shirya tsaf sai tafia Argungu kowanne yayi gayu sosai, su Haiydar yau wankan shadda akayi da yace bai cika sakata ba daga juma'a sai sallah sai kuma daurin Aure, duk da haka ba karamin kyau yayi ba kalar brown ce shaddar amma light sai ya saka k'ube dark brown, shima kuma Umar milk color ya saka.
Dady kuma hadda babbar riga, Zarah da Hanan anion material pink sukayi yayin da momy ta hade cikin swiss less, haka suka fito gwanin sha'awa da motan Dady suka fita bayan sunyi Addu'ar tafia, Haiydar ne yaja motar, suka wuce security da gate man suna musu Allah ya kiyaye hanya.
Dady yace "gashi zamuyi tafian da ba'aso ta family gaba daya Allah dai ya kaimu lafeeya" kowa yace ameen.
Bangaren gidan mai martaba suma shiri sukeyi sosai, Mama da Aunty da suka shiga kitchen sai wasu barori dake dan tayasu, Siddiqa kin fitowa shiga kitchen d'in tayi saboda kada su mama suka tayi Rashin kunya, d'akuna ta gaggara sannan tayi ma su Rufaida shirinsu su jakadiya ma ba'a barsu a baya ba, falon saukar bakin mai martaba aka gyara can ne za'a saukesu.
Saida aka kammala komai aka gyara ko ina sannan suka shirya, atampa ce blue and yellow ta shirya cikinta batai wani kwallyaba amma tayi kyau sosai.
12:00pm suka iso, wangale masu get dogarai masu tsaron get sukayi sannan suka kwashi gaisuwa yayin dogaran fada suka k'arasa suka sanarda Sarki isowan bak'insa.
Ya Mubarak ne ya taresu da murnarsa dake shima ya iso jia, bayan sunyi parking sun fito, russuna wa yayi ya gaida Dady da Mommy sukayi musabafa dasu Umar, shima Dady hannun ya basa saida yad'an duk'ar da kansa sannan ya bashi hannu Dady yace "akwai Alkhairi a cikinta d'ana ko bakaso na samu ne" murmushi kawai yayi sannan su Zarah suka gaidashi yayi musu iso zuwa falon bak'i.

KAMU SEDANG MEMBACA
HAD'UWA DAKE
Fiksi Umuma story about stubborn and arrogant boy Haidar (D one) that come from a rich and power family, and that Maryam (siddiqa) a decent gal with good behaviour but not taking in respect from no one, so simple life and came from Royal family, 2 people meet...