DA page 11

1K 44 0
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

07081095452

Page 11









Hannuna yakamo yana tafiya yana mita inaga nan gaba saikinfi karfina idan nayi sake yarinya sai jarabai tsiya
Wama yasani ko duk kokarina baki gani shiyasa kike barina ina kida da rawata to yau xaki san namiji kike Aure jarabatun banxa ya watsani kan gado yaxare rigansa ya afkomin
Yanada kyau nafahimtar dashi abunda yake tunani bashine burina amma bai ban wannan damarba yacigaba da yanda yasaba ba wani wasa daya iya shidai kawai daya Dan yamutsani ya nemi kofa ya afka to burinsa yacika yana gamsuwa xai bingire gefe yaita barci
Nikam ban iya kwanada najasa hakan yasa wata rana nai karanbanin tadasa yai wankan tsarki Ashe Rabon nasamu marine ya tsinkeni da mari yakorani falo waibaisan gulma baitashi yiba koda nikesashi yin wankan to xai gyaramin xama shibai daukan iskanci
Tunawa da hakan yasa na xiro kafafuwana na sauka nashige nayo wankana ganin banajin barci na jawo sabuwar wayata nafara duddubata naga yanda take
Masha Allah Ashe babbace Dan haka cikin seconds na bude WhatsApp sai dai banda number kowa a online cikin Sauri na dauko Dan book dina danake aje number kawayena nafara xubawa a wayan kafin kace mi naga samada kawata goma a online cikin farin ciki nafarama Kawata Hafsat magana tare da kora mata jawabin yanda mukai da mamansu daxun
Ta turomin Dan emojin nan nai xaro idanuwa da gaske Huwai kinxo amma Amadu baisan kinjeba ko
Namaida mata da baisaniba satar kafa nayi har gidan Zainab naje
Tasake maidomin emoji mai nuna jinjina kanki yafara wayewa kawata Amadu yaita kansa kuwa
Na maida mata da nima mai alamar dariya

Saiga sallamai Zainab yan matan Amadu ya daren ne

Lafiya lau yan matan Anas ya Babynmu fatan bakya takura masa

Dariya tayi Angonne yaji dadin harka yabaki tukuicin waya Huwai

Baki raboda xolaya to Babane daxun yaban ita shine nabude WhatsApp nima naga abunda kuke gani

Aikuwa xaki gani yanxu xansakaki a group dinmu  *Mijina Aljannah ta* da *Filin Littattafan Hausa Group* akwai karuwa sosai da sosai a cikinsu duk wata damuwarki xaki samu shawarwari sosai aciki
Idan kuma karatune harsai kingaji da karantawa sannan uwa uba ga xaki koyi yanda xaki hada kayan harka masu kyau da inganci

Woow Dan Allah Zainab yi sauri kisakani Dan irinsu nake buqata daman
Fatandai babu namiji acikin groups din
Habadai group din matan Aurenefa tayaya xakiga maxa ciki
Ai matane kawai kawata suma wadanda suka San kansune aciki
Sosai naji dadin hakan
Saigani tsulum cikin group din *Mijinah Aljannah ta* nayi sallama nagabatar da kaina a matsayin  bakuwa daga Samarun Zariya

Kankace me harmun saba sosai da matan cikin group din Wanda nafara karanta abubuwan gyaran mace kala kala wani sakon yashigo
Ina dubawa naganni a group din *Filin Littattafan Hausa* shima nai sallama na gabatar da kaina a cikinsa
Ban ankaraba naga karfe 11:15 na dare cikin sauri nakashe data nabi lafiyan gado sainaji namanta da komi da Allajinah yaimun barci mai dadi hardasu mafarkai masu dadi

Washe gari da wuri natashi nai gyare gyarena nai wanka nafiddo wasu matsiyatan kayana Riga da wando nasaka nakama gashina nai baya dashi naxuba turarena na koma falo naxauna jiran Allajinah yatashi yasiyo break Dan haryau bansamu wannan damarba yace shiba mai kudi bane Dan haka koko da kosai ne sai randa naci sa a yasiyo biredin Dari to ranai motsi kadan xaice anci biredi sai zakwadi ake
Axuciyata nace abunka da shine cimar safen gidanmu

Sai wajen Tara yafito yana cika yana batsewa nakallesa Allajinah ina kwana lafiya kiyi sauri kiyi girki Dan yau Yusuf xaidawo daga makaranta kikai can gida da dare naxo mutafo yasakai yafice abunsa

Nikam tunani nake waye wannan Dan gatan da Amadu kefadan naisaurin girkin tarbaisa
Inkinje kyagani inji wata xuciyar

Banbata lokaciba nagama dafa jalop din shinkafa taji kayan kamshi da magi naxuba masu nashirya na tafi gidansu Amadu

Bawani nisane sosai ba da gidana Dan haka a kafa naje muka gaisa da innarsa taimun sannu anan nema nakejin Ashe Yusuf din Qaninsane Dan kanin Babansane amma anan ake riqonsa Babansa yarasu

Wajen shabiyu na rana naji maganar Inna na yan makaranta har an iso madallah dai Abu yayi dadi
Nai maxa najawo hijab dina dake kan gadon inna nasaka na gyara xamana naci gaba da latsa wayana inaganin pic din dasuka bude na WhatsApp dina
Da sallama yashigo na ansa batare Dana kallesaba ya wuce yafada kan gadon yana wash inna nagaji sosai Dan nayi tafiyar kasa

Kara damqe wayana  nayi ban kuma dagona kallesaba saida naji inna nacewa ga matar yayankafa Huwailatu kungaisa
Cikin rashin sani nadago ido muka hada ido dashi na sauke kaina kasa ina murmushi
Lah da gaske kike Inna matar Brother ce
Kaikasani nidai aikaji abunda nafadama ninasan wani boroxa kuma tai tsaki tafice

Sannu matar brother shine kokiyimun sannu daxuwamako
Gaskiya nayi fushi bakiso dawowataba inagako
Nidai murmushi kawai nake Dan bansan mixan ceba
Inna tashigo aifa yanxu xaka dameta da surutun nakaba kaje kaci abincima ya gagara kuma baiwar Allah nan ita tai wahalan maka girkinnan tunda uwar safiya
Yanxu kuwa innarmu xan wanka sainaci girkin matar Brother naji intaci maki
Kadai kaisu inkayane ban iya abunda ka iyabani tasake fita

Bayan yai wanka yaxauna kofar dakin inna yafara cin abincin
Inna wainikau ba ance Buhari ya rufe bodar shinkafa ba

Ba innaba harni saidana Dan dara
Inna tace Allah yataimaka baikaiga rufewaba Huwailatu ta girkama taka
Duka muka saka dariya
Ai rabona dacin irin wannan girkin harna manta Dan haka matar brother aiki yasameki kwanona yakoma gidanki xanma fadama Brother
Nidai dariya nake
Inasan mutum mai fara a da tsokana alamace ta baida damuwa

Tundaga ranai Yusuf yadawo gidana da cin abincin rana da dare 

Nafahimci Yusuf mutunne marai damuwa Dan duk sanda yaxo xamu yini yanataban labarun bandariya ahankali nasaba dashi agefe guda kuma duk randa yaxo bannan idan nadawo yaita fada kenan

Wallahi fitarki na konamin rai

Dakin San abunda ke faruwa dabaki fitar da kike

Waike bakijin komi inkika fita kikabar gidanki da mijinki

Kamar yau Dana gaji nace Waimike faruwane kaketa wannan tada jijiyar wuya

Dakinsan abunda kefaruwa da bakiyi wannan dariyaiba

Natabe bakinace kagafa yayanka ketilasta fitarnan tawa nima baso nakeba wallahi
Yaxubamun ido shine kesawa saikin fita nace wallahi kuwa yaxanyi to

Yadanyi Jim yace akwai Allah amma kema kijaraba kinfitar idan yace kifitan mana
Nai dariya to kafarsa kafata kuma saiya mun kashedin karna kuskura nadawo saiyaje mutafo
Kuma dakake maganar indawo innafita kwanaki gidansu kawata Hafsat naje amma saida yagane yaita masifa kamar yadakeni narasa waya fada masa Dan Hafsat bata xuwa nan gidan balle nace gunta yaji

To kidai ankare danbanajin dadin . . . . sallamai da Hafsat tayice tasa yaishiru
Tashigo taxauna munata dariya
Amma Hafsat bakida kirki rabonki da gidannan tun biki
Kedai ai sha ani kinsan gidanmun kulle yai over kamar wata matar Sure
Dago kansa yai yakalleta sai sannan itama nagata kallesa raxana nagani qarara afuskanta shikuma kallon mamaki naga yana binta dashi
Hafsat ga Uncle Kanin maigidanne
Nadubesa nace Uncle ga Hafsat kawatace Aminiyata  tun kawancen yarinta
Ina magana inata dariya amma naga yawani daure fuska yamike yabar gidan itakuma dukta sha jinin jikinta nima sainaji banji dadin abunda uncle yaiba mataba nace kodai kinsanshine Hafsat

Tai ajiyan xuciya bansan Qanin Amadu bane muka hadu rannan yaimun magana naimasa wulaqanci
Nai dariya kodanaji shiyasa yaimaki hakan Ashe Dan uncle akwai kirki
Tamiqe xan wuce daman saboda tsoguminki nabiyo gidan Zainab xanma biya yanxu bayanda banba amma Hafsat taqi xama danhakana bata kyautar turarenda uncle yaban tatafi

Shin da gaske abunda ya hada Hafsat da Uncle Yusuf kenan ko ko da wata akasane yan uwah

Nagode taku Haupha

0708109545

DA AURENAWhere stories live. Discover now