EPISODE ONE&TWO

901 70 8
                                    

⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION
-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-       
               
   BAMBANCIN ƘASA
  {Battle to reach}

Book By:SIYAMAIBRAHEEM
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM
بسم الله الرحمن الرحيم
Sadaukarwa zuwa gare ki Hauwa'u Maman Zee consider This book to be urs ❤

EPISODE:1&2

   Babu abin da ke tashi a wannan dokar dajin face muryoyi da kukan tsuntsaye haɗe da dabbobin da ke keɓance a muhallin su,tun daga nesa ake sakar da maɗanni(arrows)wanda yake fitowa ta ko wani ɓangare ba tare da ya dakata ba domin kuwa zuwa suke kamar ana ruwan su ta ko wani ɓarayi na dokar dajin nan...
   Gudu yake amma tana bin sa kamar dai gudun fanfalaƙi,agaji da ceto yake nema amma ita kam burin ta shine ta cimmai dan ta ƙarasa ida ƙudirin ta a kan sa..
  Kamar ƙiftawar ido,yana juyawa da nufin fakewa a bayan wani babbar bishiya dake da wani irin dandamali kawai sai ya ji cakaf,,an kai mai damƙa mai ƙarfin gaske haɗe da matse sa da bishiyar...

  Nishi yake yi kamar wanda ran sa zai fita,so yake ya numfasa kafin ya mata bayanin inda ya fito da kuma waɗanda suka aiko sa sai dai yin hakan ya ƙagara dan kuwa bata ba sa wannan damar ba sakamakon saka mai takobin ta da tayi a wuyar sa ta yadda ta san ko hauka yayi bai isa ya musanta abin da zata tambaye sa ba...

  Idanun ta cikin nasa wararrun idanun da suka nuna alamar tsoro firgici da nadama,..
  Yana ɓari yana haki maganganun sa na ɗaukewa ya taro iya kuzarin sa ya furta
  "Kar ki kashe ni ina da iyali,ina da mata ina da yarinya ƴar ƙanƙanuwa wacce bata fi shekaru huɗu ba,ki min rai ki taimake ni,ki mayar dani masarautar da aka aiko ni ba tare da kim min lahani ba,in kika min hakan ni kuma na maki alƙawarin ba zan sake bin hanyar da maƙiyin ki ya bi ba ya mai girma sarauniyar mayaƙa"...

  Tun da ya fara jero mata jawabi take bin sa da kallo,kanzil bata ce da shi ba har sai da ya kai madakata sannan ta fara bin jikin sa da wasu irin ƙazamin kallo kafin daga bisani ta tofar da yawu ta gefen sa..
  Mayar da duban ta tayi gare sa tana son sun haɗa idanu da shi..
  "Ka ce in maka rai in bar ka ka koma inda aka turo ka"?ta mai ta tambayar tana mai ɗage giran ta biyu sama haɗe da ƙure sa da idanun ta..
  Cikin sauri da ɓarin jiki ya amsa mata da kai,ai kuwa sai ya ji saukar mari mai zafin da sai da ya saka sa ɗauke wutar wucin gadi sannan ys dawo daidai ya buɗe bakin sa ya amsa mata..
  Ƙara danne takobin tayi a wuyar sa tana kallon sa sannan ta ce
  "Ni ce doluwa"?ko ina na jikin sa na ɓari ya amsa mata ta hanyar girgiza mata kai a lokaci ɗaya kuma ya tuna abin da ta tsana kenan wato a girgiza mata kai sai yayi saurin amsa mata da
  "A'aa a'aaaa sarauniya ban ce ba"saurin tarar numfashin sa tayi tana faɗin
  "Toh ni na ce kenan"??a firgice ya girgiza kai sai ya kuma amsa mata da baki
"A'a sarauniya a'a"!!wani irin shu'umin murmushi tayi wanda ya narkar da wannan mutumin da ke hannun ta,ya sadaukar dan muddin ta riƙe ka ta maka wannan tambayar sannan ta ida da wannan munafukin murmushin toh tabbas abu na gaba da zata yi shine raba maka kan ka da jikin ka in ko bata raban ba toh zata maka lahanin da sai ka gwammaci da ma kan ta cire tun tashin farko...
  Bai gama wasi wasin sa ba ya ji abu mai kaifi ya kawo mai hari kenan ajalin sa ne ya buɗe mai ƙofa..
Fil ta gille mai wuyar,..jini ne ke bulbula kamar an ɓalle kan famfo,ƙaƙari ya shiga yi yana yin sama da ƙasa kamar an saka mai abin jijjiga jiki,matsawa gefe tayi tana kallon sa har ya faɗi ƙasa wanwas tun yana jan iska yana gwalalo idanun sa waje har dai ya ɗauke wuta ɓat ya daina juyi..

  Takowa tayi gare sa yana kwance matacce ta saka hannun ta a tsakankanin kan sa da ke lilo da wuyar sa ta riƙo jijiyar da ke reto tsakankanin wuyar da kan ta kai mai wata irin fizga wanda yayi sabadiyar rabewar wuyar nasa da kan sa..

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt