EPISODE FIFTHY THREE&FIFTHY FOUR

162 20 0
                                    

EPISODE:53&54

Sai da su Juda suka share kwanaki biyu cikin gidan kaso kana aka fito da su bayan doguwar bincike da aka yi aka gano ainihin tarihin wacce ta taho ta ɗauke yarima Ziyan sannan aka bincika aka ga cewa su waɗannan ɗin,wasu matafiya ne da basu san komai ba yawon su kaɗai suke yi a duniya daga wani ƙauye suke..
  A ranar da aka fito da su sai da Callee ta bige wani ɗan sanda cikin fushi da ɓacin rai ta haɗa sa da bango tana faɗin sai sun dawo mai a karo na biyu dan yanzu ba shi suka ma zuwar ba..
  Jan ta ƴan uwan ta suka yi akan tayi haƙuri ta zo su tafi,..
  Halayyar nasu ma tsorata mutanin wurin yake haka duk yadda suka motsa dai an bi su da kallon ƙasƙanci,duk suna sane amma da yake abin da ya fito da su daban sai suka ƙyale akan kawai su koma ga Baccus su haɗa kai da shi su tunkari masarautar Ottoman duk ko ma me zai fanjama ya fanjama amma wannan tafiyar wahalar ta ishe su..

  Kamo hanya suka yi suka nufi inda aka ajiye masu dawakan su duk rai ɓace suna ji suna gani sun yi asarar kwanaki da dama ga tsarabar rashin nasara da ta same su abin dai bai masu daɗi..
  Yadda ake masu kallon aliens suma haka suke kallon mutanin a matsayin aliens abin tsoro dan tunda suke a rayuwar su da suka taso basu taɓa ganin bindiga ba haka motocin da suka gani basu taɓa ganin sa ba dama dama Agneta da Fianna suna iya shaidawa dan fah yarima Ziyan ya dage sai da ya kawo masu jajayen kunnuwa yankin kuma a motar su suke kwana haka zalika shi kan sa wasu zuwan nasa yakan taho da motar toh shi kaɗai suka sani mai mota bayan shi basu san komai mai kama da motar ba..

  Suna kan tafiyar su zasu nufi hanyar da suka fito sai Balik yayi wani magana da ya saka su reasoning da shi
  "Ni kam ban san me ke cikin wannan gari ba da duk aka gwada amfani da sihiri amma bai yi ba sannan muka yunƙura mu kare kawunan mu da makaman mu amma duk basu mana aiki ba sannan in fah kun lura,kaf mutanin ƙasar nan shigar su ba irin tamu bane sannan ɗabi'un su ya Bambanta da irin tamu ɗabi'un wannan shi ake kira da _Bambancin Ƙasar_"??..
  Kasaƙe Berenice tayi sannan ta gyaɗa kai tana faɗin
  "Yaya na kana da tunani sosai,ka san abin nan ya daɗe yana dami na a kai na amma furtawa ne kaɗai ban yi ba sai gashi kai ka furta a zahiri,nima ina ganin kamar wannan ake kira Bambancin Ƙasar"..
  Karɓe maganar Fianna tayi tana faɗin
  "Yanzu abin yi kawai shine,me zai hana mu canza ɗabi'un mu zuwa irin nasu,a gani na fah,dan kun ga ai ba iya mu ke cutuwa ba a cikin yaƙin nan,mutanin dake zaune a ƙasar nan ta Sultan da abokanan sa duk suna cutuwa,duba da yadda Juda ta mana narrating ainihin labarin addini har ta ce islam na da sharuɗa da dama sannan an yi ƙiyastin al'adu da addinai sun sami ra'ayoyi iri ɗaya dan haka mutum ke iya haɗa biyun yana rayuwa da su,sai nake ganin kamar in muka zauna tare da mutanin nan muna iya zamowa sanadiyar fallasuwar Sultan Baal-Hamon,kun dai san ba wai ba'a kai ilimi ƙasar bane,a'ah,shine dai ya canza komai hawar sa kujerar mulkin nan,shi ya lalata komai dan an ce ba dan shi ba toh da ba haka muke rayuwa ba kuma tunda kuka ga mun yi amfani da sihirin mu amma bai amfanar da mu ba toh ina ga kawai mu zauna tare da mutanin nan mu saba da su mu sanar da su gaskiyar lamarin nan in ya so sai su biyo mu mu tafi tarekun ga in sun tafi suma ai ba lallai bane sihirin Sultan yayi aiki a kan su ba tunda su ɗin wasu irin mutani ne,ya kuka gani"?..
  Nannauyar ajiyar zuciya Juda ta sauke sannan ta gyaɗa kan ta tana faɗin
  "Fianna,kina da kaifin tunani sai dai matsalar,,,"sai tayi shiru sai duk suka sauko daga kan dawakan nasu suka nufo ta itama ta sauko ta tsaya haɗe da ɗora hannun ta a waist ɗin ta tana mai hurar da iska waje kafin ta cigaba
  "Ina tsoro,,hala ma Sultan ya rigada ya gama da tarihin ƙanwata,kun ga duk ku,naku matsalar ƙanƙani ne akan nawa matsalar,mahaifiyar mu na can na mana fatar kariya,tana fatar ganin na koma gida tare da ƙanwa ta,and here i am,leaving in the bondage of the Sultan,ya zan yi da rayuwa ta?i have to go and search for my aunts,my two aunts,i have to create peace in my own land,Babylon,i have so much to balance but i am unable because of this strange Sultan,ya zan yi da rayuwa ta"??..
  Wato tunda Juda ta fara zayyano kalaman ta sai Callee tayi shiru ta natsu tana sauraron ta dan tun da sule tare da Juda bata taɓa faɗa masu sirrin ta ba sai yau,wato tana da tarihi ne kusan irin nata dan itama tana son nemo families ɗin mahaifiyar ta kamar dai yadda Juda ta faɗin ne..
  Kamar an mare ta sai ta ɗago idanun ta ta saka cikin na Juda da yanzu ta juyo dan ganin me Callee ke yi..
  "Ya sunan aunts ɗin naki Juda"?da mamaki duk suka kalle ta sai ta amsa mata da
  "Aunt Daliyah da aunt Yahaira,sunayen su kenan kuma su suka rabu da mu suka rabu da ahalin mu sakamakon aure da ya ɗauke su tun lokacin bamu kuma ji daga wurin su tun mahaifi na na neman su gashi yanzu ya mutu sai ni alhakin nemar su ke kai na dalilin haka ma ya sa kuka ga duk na damu in ga komai ya faru ya wuce"!!cikin hanzari Callee ta tari numfashin Juda
   "Ban san ki ba ban kuma san ya aka yi sunan mahaifiya ta ya zo daidai da na aunt ɗin ki ba da ƴar uwar ta dan nima sunan yar uwar mahaifiya ta Yahaira kuma suma aure ne ya rabo su da ahalin su basu kuma jin labarin su ba sai daga baya da suka tafi inda suka taso a nan suka ci karo da zancen barin du yankin sakamakon yaƙin da Sultan Baal-Hamon ya aika a yi a wurin sannan da saka hannun mutanin masarautar Babylon ɗin"!!da sauri itama Juda ta kalli Callee ta ce
  "Ya sunan waɗannan ahali na mahaifiyar ki"?gaban ta na faɗi tayi tambayar sai Callee ta amsa mata da
  "Mahaifiya ta tace sunan mahaifin su Artegal Ted,sunan babbar yayan su kuma Baadi Artemas iya abin da na sani kenan"!!ai a wani irin mugun kiɗimewa Juda ta janyo hannun Callee tana ƙoƙarin shafa fuskar ta..
  Sai suka zamo abin kallo ga su Fianna da abin ya ɗaure masu kai ganin kamar jini ne ke son bayyana kan sa sai dai suka natsu dan jin inda labarin zai kai..
  Hannun Juda na ɓari ta shafo fuskar Callee tana faɗin
  "Callee...ni...ni..ni ce,.ni ce ɗiyar Baadi Artemas kuma shine babban wa ga ƙannin sa biyu,Yahaira da Daliyah ban sani ba ko daga ahali ɗaya suka fito ba amma suma sunayen su kenan sai dai ban sani ba ko jini ɗaya na fito tare da ke"!!?..
  "Kallon ta itama Callee tayi tana nazarin kalaman ta sai wata dabara ta faɗo mata sai ta tambayi Juda
  "Shin,mahaifin ki ya taɓa shiga matsala a masarautar Babylon har aka saka sa a bursinar koyar da hankali na tsawon satittuka"??saurin gyaɗa mata kai Juda tayi sai ta kuma tambayar ta
  "Shin ya taɓa tsaron sarkin Babylon har ya aka mai sharrin cewa ya haukata dokin yaƙin sarki wanda yayi sanadiyar ɗaure sa da aka yi"??baki na ɓari ta gyaɗa ma Callee kai tana faɗin
  "An yi haka Callee an yi haka wanda sanadiyar sa ne ma ya sa mahaifi na ya sami damar auren mahaifiya ta"!!!tun kafin ta ida maganar Callee ta kuma tarar ta da
  "Sunan ta gimbiya Hadara"??da mamaki Juda ta gyaɗa mata kai tana faɗin
  "Ya aka yi kika san haka Callee"?.ajiyar zuciya kawai Callee tayi tana jin daɗin haɗuwa da wani ɓangare na rayuwar ta kuma jinin ta..
  Rungume Juda tayi tana faɗin
  "Bambancin jini da bare kenan Juda,wani abin mamaki shine tunda muke tare da ke tsawon kwanaki bamu taɓa sani ba amma sai gashi yanzu out of the blue mun gane cewa mu ɗin jinin juna ne,am happy"!!sai da sauran suka ji kamar su taya su kukan farin cikin da suke yi..
  Sai da abin ya lafa sannan suka tsaya dan tsayar da magana ɗaya dangane da batun abin,tunda ko ba komai abin ya zo ma Juda da sauƙi dan yanzu ta gano ƴar uwar ta ta san kaso sittin ya ragu cikin kaso ɗari na matsalar ta..

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now