Feedynbash Stories

Refine by tag:
feedynbash
WpAddbatulmamman
feedynbash
WpAddbatulmamman

6 Stories

  • RA'AYIN ZUCI... THE OPINION OF THE HEART  by zm-chubado
    zm-chubado
    • WpView
      Reads 417
    • WpPart
      Parts 8
    Tun a ganin farkon da muka yiwa juna zukatanmu suka amsa alaƙa mai ƙarfi ta samar da gurbinta a cikin zukatan mu. ba tareda nayi Aune ba, bijirowar YUSUF ATTAHIRU cikin rayuwata tayi nasarar yin fatali da duk wata nutsuwa da ubangiji ya Adana a cikin zuciyata. Tun da ga wannan rana sai ya kasance babu wani ɗa namiji da nake mafarkin na ƙare rayuwata da shi sai ɗan Attahiru.... Burin rayuwata ya cika kamar yanda nayi fatan ya kasance. sai dai, abinda nayi katari da shi a karkashin inuwar Aurensa ya zame mini abin tunawa na iya tsahon rayuwata, duk da irin tarin kaunar da ya cika zuciyata dashi, hakan bai hanani fuskantar Kalubalen Rayuwa daga danginsa ba.....
  • GIYAR MULKI by zm-chubado
    zm-chubado
    • WpView
      Reads 135
    • WpPart
      Parts 2
    Akwai wata iriyar giya da idan mutum ya sha take gusar da imani, barasa ce amma ta mulki, wadda ke sa zuciya ta manta Allah, ta manta iyaye, ta manta duk wata alaƙa balle a samu ɗigon halacci da jinƙai. GIYAR MULKI labarin Alhaji Shamsu, ɗan siyasar da mulki ya rufewa masa idanu, ya aikata abin da duniya bata taɓa ji ba irinsa ba ko a zamanin jahiliya. Ya sadaukar da mahaifiyarsa Talatu, mace mai tsoron Allah da gudun duniya, duk a kan kujerar da ba shi da tabbacin mallakarta. A cikin tsananin rufewar idon neman mulki Shamsu ya faɗa cikin rijiyar zunubi. lokacin da Giyar Mulkin ta sakeshi sai ta barshi da zubar da hawaye da nadama mara amfani.
  • DA NA SANI by zm-chubado
    zm-chubado
    • WpView
      Reads 601
    • WpPart
      Parts 1
    wasu lokutan ƙaddara kan faɗawa Ahalinmu bawai don gazawarmu ba sedan kawai Allah ya jarraba imanin mu kamar yanda ya faɗawa Jameelah!! koma fiyeda hakan, a zaton mu mallakar miji me tarin dukiya da tangamemen gida da mota shine morewar rayuwa da jindaɗin duniya sedai wasu lokutan sam ba haka abin yake ba ta wata fuskar ma haɗarin dukiyar yafi talaucin illah da tashin hankali inji Jameelah
  • GANGAR DUHU!  by zm-chubado
    zm-chubado
    • WpView
      Reads 375
    • WpPart
      Parts 10
    Rayuwarsa a lulluɓe ta ke da duhun da ba na dare ba, ba shi da kowa sai mahaifiyarsa wadda ke azabtuwa da tarin jarabobin da ke bibiyarta, cikin ko wani irin gida akwai haske amma a cikin nasu gida babu sai tarin baƙin ciki da ƙuntatuwa. Ibrahim Wajagal ya zama gangar duhu mai jefa tsoro a zukatan Al'umar Unguwarsu da kewaye, sannan ya zama murɗaɗɗen ɗa mai sanya mahaifiyarsa hawaye! Soyayya ta zame masa ciwo, ya yin da tausayi ya koma hukunci. Mahaifiyarsa ta rasa zaɓi, a tsakanin ƙauna da fushi wanne zata ɗauka? addu'a za ta yi ko ƙorafi? Haƙiƙa tana buƙatar sauƙi da haske a cikin duhun da ya cinye mata ɗa. Duk da cewa wani duhu ba a haskaka shi da fitila, sai da hasken addu'a da haƙuri kaɗai!
  • MURADIN RAI! by zm-chubado
    zm-chubado
    • WpView
      Reads 4,881
    • WpPart
      Parts 14
    A tsakanin duniya biyu mabanbanta, ƙaddara ta yi kutse a tsakanin rayuka biyu. Duk a ƙarƙashin kalma ɗaya: "soyayyah!" Tunaninta da duk wata nutsuwarta sun karkata ne akan sama masa mafita da ga duhun ƙaddarar da ya yi masa ƙawanya, sai dai, da ga baya ta yi realizing cewa ta faɗa a tarkon son sa, soyayya mai tsanani ga Yusuf Hateym Al'qasrawi. kyakkyawan balarabe ma'abocin Addinin musulunci, saɓanin ita da ta kasance krista wadda bata gasgata kaɗaituwa Ubangiji mahalicci ba. Abu ne mai matiƙar wahala ta iya mallakar zuciyar Yusuf wadda ya jima da mallakawa Matarsa Yumnah Sulaiman El'ghanee, kyakkyawar Balarabiya mai kwarjinin musulunci. Doctor Chioma Nonso Chukuma, ta Fahimci ba zata iya karawa da Yumnah Sulaiman a zuciyar Abu'hateym ba, wannan ya sa ta ƙara ƙaimi domin yaƙi akan ƙudurinta. Musamman data fahimci babu gurbi da ya yi saura, wanda Yusuf ke jin zai iya mallakawa wata ɗiya mace a duniya...! 08102777485
  • SILAR KENAN by zm-chubado
    zm-chubado
    • WpView
      Reads 315
    • WpPart
      Parts 1
    Labarin Zuriya