*MIJIN BAHAUSHIYA* Shin ina tarin soyayyar da ya ke nuna min a baya ya tafi yanzu? Shin ina kula da tattalin da yake bani a lokacin da muke soyayya kafin ya aure ni? Shin ina tsantsan tausayi da mutuntawa da yake nuna min? Shin ina tausasan kalamai masu yaye baƙin ciki da dasa farin ciki da annushuwa a zuciya suke? Canza mini shi aka yi, ko dama ba soyayyar gaskiya bace ya sa shi aure na? Dama jikina kenan ya ke so ya aure ni? Wai haka dama auren yake? Hmmmm nasan waɗannan tambayoyin sun daɗe suna yawo a zukatan akasarin mata ma'aurata, kina son jin dukkanin amsoshin waɗannan tambayoyin? Kasance da littafin Mijin Bahaushiya, dama waɗansu tambayoyin da ban ambato ba. Wai ina matsalar take ne? Ina kuma mafita??? Kasance da Sumiee B./Oum Sumayya. Hakkin Mallaka :- Diamond Creative Writer Association (DCWA)