WATA QADDARAR

448 21 12
                                    

♦️♦️♦️
*WATA QADDARAR*
♦️♦️♦️

The true life story

*_Writing by: Chubaɗo_*

*_Da sunan Allah mai rahama maijinqai, salati da ɗaukaka su tabbata ga manzon tsira Annabin mu muhammad (SAW). Ya ubangiji yanda na fara lfy Ka bani ikon gamashi lfy._*

*_Wannan labari labarine na gaskiya ba qirqirarre bane ba, haka kuma banyarda a juyaminshi ta ko wace fuska ba ba tareda amincewa na ba🙅‍♀️_*

_Page: 1 to 2_

📖____ 11:30pm na Dare a New Barek dake Kafanchan ɗaya daga cikin Local govement ɗin dake cikin Jihar Kaduna, Sojojine sahu-sahu ko wanensu a ƙame yake ƙam tamkar an dasasu, kallo ɗaya zakayi musu ka fahimci kowan nansu ya karɓi horon yaƙi na musamman a gurin masu ruwa da tsaki akan hakan, wani matashi na hanga a tsaye bisa wani ƙayataccen tudu wanda aka tanada sabida tsayuwar shima ya ƙame ƙam a gaban wata tuta me daukeda kalar green and write wadda take kaɗawa a saman iska gwanin shi'awa, matashin ma'abocin cikar zati ne gamida kwarjini, sanye yake cikin Dakakkun kakinsa masu launi irinna jami'an tsaron ƙasar Nigeria wato (armey colour)

ƙafafunsa a rufe suke cikin wani murɗaɗɗen takalmi na musamman wanda aka tanada sabida masu alhaki akan hakan koma in kirasu da mazan faman ƙasar Nigeria (sojoji)

Mutum ne shi me matsakaicin tsayi gamida kwarjini, haka kuma be kasance a cikin jerin maza masu hasken fata sosai ba, sedai dukda hakan baza'a kirashi baki irin wuluk ɗinan ba, yanada gogewar fata sosai wadda take nuna ainihin irin gidan daya fito, tun daga kan murɗaɗɗen takalmin dake ƙafarsa nake nazarinsa har idanuna suka sauka akan tambarin dake maƙale a jikin ƙirjinsa me ɗauke da harufan sunayensa kamar haka, *_CAPTAIN HAMIYD ALQASIM MANUMFASHI,_* Kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci yanada ƙira irinta sadaukantaka, wanda hakan yasa a barikin sukeyi masa laƙabi da *_SARKIN GUDU_* Sabida jajircewarsa, shekarunsa bazasu gaza 35 ba,

Captain Hamiyd yanada jajircewa gamida naci akan dukkan abinda yasa a gabansa wannan shine mafarin nasararsa ta farko, lokacin dana matsa dab dashi don ganin ainihin fuskarsa sabida in samu damar ɗaukowa me karatu Rahoto akansa seda takarduna da Kuma birona suka faɗi ƙasa sabida ganin irin kwarjininsa, Captain Hamiyd be kasance a cikin jerin maza masu masifar kyau Sosai ba irin na mazan novel😂, amma dukda hakan yanada kyau irin wanda Allah yayi masa daidai da Zubin cikar halittarsa, fuskarsa a ɗauke take da madedaitan idanu gamida dogon hanci, sedai hancinsa yanada dan faɗi kaɗan wanda hakan yay daidai da zagayayyiyar fuskarsa,

Idanunsa basuda haske sosai amma sunada wani irin maganaɗisu a cikinsu wanda Allah ya ɓoye hakan a cikinsu, wanda yafi kamada baiwa ta musamman a taredashi captain Hamiyd ɗin, fuskarsa a ɗaure take Tamau babu alamar wasa kokaɗan A taredashi ya fara magana kamar haka," dukanmu nan mun sani cewar ba kwanciyar bacci bane ya kawomu nan, hakakuma ba rayuwar jindaɗi bace tasa muka bar ahalinmu muka kasance a nan ba face kishin ƙasarmu da kuma ceton Rayukan Al'umar dake cikin wannan gari, ya kamata ku fahimci cewar a kwai aiki gagarumi a gabanmu sabida tun kafin a kawoni garin _(Kafanchan)_ nakejin labarinsa da kuma Irin zubin taurin kan da Mutanan garin kedashi,

idan kuka kalli irin ɓarnar da sukayi zaku fahimci cewar a kwai wani ƙulli a zagaye dasu Wanda babu wanda ze iya kwanceshi balle ya fahimci wani abu a kansa face ƙabilanci da kuma son nuna fifiko akan addini, yaƙin kwana ɗaya da yini kawai fa sukayi amma seda suka samu nasarar yin kashe-kashen da ko'a garin JOS ba'ayi kamarsaba a lokacin da sukai yaƙinsu na farko!

don haka we have to very very carefull akan Christan's ɗin dake cikin garin nan sabida sunada masifar taurin kai fiyeda zatonmu (masu bautar yeso Almasiyu)

WATA QADDARARWhere stories live. Discover now