HAKKI NE 1

838 27 5
                                    

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
       *HAKKI   NE*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

_Zahra surbajo_

*Bissimillahirrahmanir rahim.*

_wannan littafi me suna asama k'irk'irarran labarine,ban yishi dan wani ko wata ba in kunji abun da yay dede da rayuwarku arashine_

_Abun da ze zamo alkhairi Allah ya bani ikon rubutawa,ya kaudani daga akasin hakan_

*Sadaukarwa ga Hauwa'u Muhamnad Danjuma Nbs keffi,Alherin Allah ya kai miki*

*1*

"Na rantse da girman Allah duk shegen da ya kuma dukarmin d'a a layin nan se yasan ya daka,uban wa ya haifamin yaran da zan zauna ay ta dukarmin"cewar hajiya inna dake ta faman zage zage atsakar layi,makwabta duk sun leko suna kallonta.

Seda tayi masifar ta iya masifa sannan ta kad'a kanta ta koma cikin gidanta dan ta rarrashi d'an nata da aka daka agurin wasa shi da yara yan uwansa.
      A zaune ta samu yaron yana wanke fuskarshi datasha kuka.karasawa kusa dashi tayi  ta dafashi tace,"kai ma ne modibbo ko kadan baka biyo halina ba,da ka biyo halina to wlh da kudi akace suyi ma haka bazasuyi ba,dan san da zakaci ubansu wasani"

Yaron d'an kimanin shekaru goma shabiyar,D'ago ido yayi yakalli mahaifiyar tashi yace cikin taushin murya,"inna to meye ribar yin fad'a da mutane kullum,be da wata fa'ida"ya fadi yana kokarin mik'ewa.

"Dalla can jani talau kawai,ay sekaje kaita bari ana jibgarka,"cewar inna cikin jin haushi.

Murmushi yayi sannan yace cikin ladabi"inna ta takaina Allah yabar min ke,batun gaskiya inna,gwanda daban rama ba sabida kinga su mada kowa yasan basa ji,in mukayi rigima cewa za'ayi tafiyata d'aya dasu shine kawai yasa na hakura"

Kwafa inna tayi sannan tace"can ta cakalkale maka,Shiyasa mutallib ke burgeni be barin ta kwana,ni b'ace min da gani sullutu kawai'"

D'an rusinawa yayi yace"Allah ya huci zuciyarki inna ta"yana gama fad'i yasa kai ya wuce zuwa d'akinshi.

Muje zuwa.

Surbajo for life.

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
      *HAKKI NE*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

Zahra surbajo

*Dedicated to Hauwau muhammad danjuma nbs keffi*

*2*

Modibbo tunda ya shige d'aki yake share kwalla dan inda sabo yasaba da fad'an na innar tasa.

Mutallib ne yashigo d'akin da saurinsa rai ab'ace ya k'arasa gun d'an uwan nasa yace yana huci"Dan uwa naji ance su mada sunma taron dangi sun dokeka agun wasa da gaske ne?"ya tambaya yana huci.

A hankali Midibbo ya kalli d"an uwan nasa yace"da gaske ne mutallib amma ay na barsu da Allah"be jira yagama jin meze ce ba ya juya da gudu zuwa waje yana fad'in"Wlh basu daki banza ba duk shegen daya kwana lafiya shiyaso"
   Inna na zaune taga shigewarshi da gudu,ay bata tsaya d'aukar mayafi ba ta biyo bayanshi da gudu tana gyara d'aurin zaninta tana fad'in"maza jarumi na,me share kuka na,karka barsu seka rama masa maza ka kwato kimar gidanku"

Shiko mutallib tunda ya falla dq gudu seda ya isa majalisar su mada,duk wanda ke gurin seda ya kwasheshi da mari,nan ko sukayo kansa,cikin ikon Allah basuyi galaba akanshi ba har aka rabasu,ya juyo ya dawo gida.

A k'ofar gidan yasamu inna tsaye tana masa abunnan da akewa k'auraye"chau chau nawa,Alkah de ya biya yan maza,"murmushi yayi yace"naci uwarsu inna"

Jan shi tayi zuwa cikin gida tana murna,modibbo koda suka shigo cikin gidan be fitoba zaman shi yayi.

*FARKON LABARI*

आप प्रकाशित भागों के अंत तक पहुँच चुके हैं।

⏰ पिछला अद्यतन: Feb 09, 2021 ⏰

नए भागों की सूचना पाने के लिए इस कहानी को अपनी लाइब्रेरी में जोड़ें!

HAKKI NEजहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें