BAƘIN KUMURCI

11 0 0
                                    

*BAƘIN KUMURCI.*

*GASAR MATASAN MARUBUTAN HAUSA.*

*RUKUNI NA GOMA SHA ƊAYA*

*JIGO:CIN AMANAR ƘAWANCE/ABOTA*

*LABARI,RUBUTAWA*
    *MARYAM ISMAIL MAJIDAƊI*

*SHAFI NA FARKO*

    Bismillahirrahmanur raheem

Motace keta tsala gudu a saman shimfiɗaɗɗan titin dake unguwar Barheem cikin jihar katsina,cikin motar Matasa ne su biyu wanda zasuyi sa'annin juna.sanyayyar waƙa ce ke tashi daga cikin motar,wani kyakyawan saurayi ne ke tuƙin  cikin shigarsa ta manyan kaya ,ya murza hula a kansa,duk da yana zaune hakan bazai sa ka kasa gane dogo bane.yana da faffaɗan ƙirji yayin da ya haɗe da murɗaɗɗiyar surar jikinsa da kai tsaye ba zaka kirasa siriri ba,jikinsa yana da kauri ga asalin kyawu irin na fulanin usul Mujaheed kenan yaro ɗaga ga Alhaji Aliyu.Saurayin dake gefansa kuwa fari ne tas amma bashi da ƙiba ,dogo ne kuma yana da kyawu daidai misali Sameer kenan babban Amini tun yarinta ga Mujaheed.
    kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa yayi ƙirar Gucci tare da sakin siririn tsaki yace"bansan ya akayi na daɗe haka ba,na tabbatar Zalirat tana can tana jirana."Murmushi Sameer yayi yace"kayi a hankali mu dai karka kada mu,i dai kasan ko ƙarfe nawa zaka kai Zalirat zata jiraka,hanta da jini."ya ƙarashe maganar yana yiwa Mujaheed hararar wasa.ƙwafa kawai Mujaheed yayi be sake cewa komai ba har sai da ya shigo cikin farfajiyar makarantar tasu Zalirat.Zaune take ita kaɗai a ƙarƙashin wani babban bishiyar mangoro dake shuke a cikin makarantar,hango Motar Mujaheed da tayi yasa ta saki lallausan murmushi tare da miƙewa,Zalirat kyakyawar budurwace ajin farko ,bata da tsawo sosai sai dai tana da kyau na ɗaukar hankali gata fara tas,irin matan nan ne da akewa laƙabi da masu zubin coca-cola.Sanye take cikin doguwar riga ta atamfa irin mai faɗi ɗin nan,sai ta yane kanta da mayafi ƙarami sosai shigar tayi bala'in ansar jikinta,cikin takun ƙasaita ta ƙaraso gaban motar tare da ƙwanƙwasa gilashin motar.Ƙasa da gilashin Sameer yayi yana lasar baki kamar wani tsohon maye,ba yau ne rana ta farko daya fara ganin Zalirat ba amma duk lokacin daya sakata a ido sai yaji wani abu ya tsarga masa tun daga diddigen ƙafarsa har zuwa ƙoƙon kansa.Ganin Sameer yasa taɗan ware dara-daran idanuwanta tace"A'a gaskiya da sakal,ina Yayan nawa yake?."Washe baki Sameer yayi yana jin kunnensa yana ansa kuwar ɗaɗɗar muryarta yace"Zalirat!,ina kuwa zan kaisa?,wanda kinsan da kin ganni tamkar kin gansa ne,kinsan ko barci baya da ikon rabamu."Jinjina kai tayi cike da gamsuwa tace"wannan haka yake Husainin mu,ai ku Abotar taku ta manya ce,tun da nake ban taɓa ganin masu kusanci irinku ba."Isowarsa kenan a wajen riƙe da leda fara a hannunsa,fuskarsa sake yace"Rabin jikina,ai wannan Abota kawai ki kalleta,a duk Duniya baya ga iyayena bana jin ina son wani abu bayan Sameer dake ɗin nan,Sameer sirrina ne kuma ni yanzu ina masa kallon Ɗan'uwa na jini,Sameer ya zama wani sashe na jikina abun alfaharina kuma."Nisawa Sameer yayi yace"na zama jigonka ko ka zama nawa?,kaine ka mayar dani mutun lokacin da nake yawo a titi ina garari bana da maraba da almajiri,kaine zance ka zama wani ɓangare na jikina."Dariya Zalirat tayi har ramin dake kwance a kumatunta suka lotsa(Dimples)tace"Allah ya barku a tare Aminan juna,yanzu muje kada mu kuma ɓata wani lokacin."sosai Mujaheed ya tsura mata kyawawan idanuwansa yana kuma jin wata irin tsantsar soyayyarta na fizgarsa.Waro ido Sameer yayi yace"ku cinye juna kawai akan irin wannan kallon haka,me kukewa sauri ne?,ina ce ƙarshen satin nan ne auren naku?."Juya ido Zalirat tayi tace"dama a rage ya dawo gobe."Ta ƙarashe maganar tana rufe fuskarta da tafikan hannayenta alamun kunya.Hmm kawai Mujaheed yace ya ranƙwafo tare da miƙa mata ledar hannunshi ,ƙarɓa tayi tare da godiya.Da kansa ya buɗe mata motar ta shiga ya rufe kafin ya zagaya gefan mai zaman banza ya shiga Sameer ya fara jansu suna kuma fira tamkar wasu ƴan ukku.Zalirat suka fara ajiyewa kafin yakai Mujaheed gida sannan ya fita da motar Mujaheed ɗin akan zaije ya dawo,kai tsaye gida ya wuce,ɗakinsa dake cikin zauren gidansu ya shiga tare da rufo ƙofar,kasa zama yayi yana ta juye-juye a tsakar ɗakin yayinda yake faman tunani kala-kala a ransa,da ƙarfin gaske ya kaiwa bango naushi yace"Dame ya fini!?,me yasa kullun sai ya samu abu kafin na samu,na gaji da zama ƙarƙashinsa!."ya ƙare maganar da tsantsar fushi.haɗiye yawu yayi masu masifar ɗaci sannan ya kuma ficewa da sauri kamar wanda aka wa allura.
   Gudu yake shararawa kamar zai tashi sama,be tsaya ko ina ba sai offishin Alhaji Aliyu wanda ya kasance babban ɗan kasuwa ne,ko kaɗan masu tsaron wurin basu tsayar dashi ba ya wuce saboda sanin alaƙarsa da Alhaji Aliyu.ƙofar offishin ya tura bakinsa ɗauke da sallama,Wani farin Dattijo ne zaune cikin shiga ta alfarma kallo ɗaya zaka masa ka hango tsantsar kamarsa da Mujaheed.Siririn farin gilashin idonsa ya cire yace"Barka da zuwa Ɗana Sameer ka shigo mana".Fuska sake Sameer ya shiga har ƙasa ya duƙa ya gaishe da Abba kafin ya zauna a kujera yace"Abba wurinka nazo."Gyara zama Abba yayi yace"To Sameer ina sauraranka Allah yasa dai lafiya?."Ƙasa yayi da kai yace"Abba akan Mujaheed ne,abun yafi ƙarfina shiyasa nazo gareka,Abba Mujaheed ya canza gaba ɗaya na kasa gane kansa,bashi da aiki sai neman mata da shaye-shaye da yake neman ɗaurawa kansa,tun ina masa faɗa harna gaji,ko kaɗan baya saurarata ,ni kuma bazan iya zama ina kallo rayuwar Ɗan'uwana ta gurɓata haka ba,yanzu haka maganar da nake maka yana shirin ɗaukar wasu manyan ƙuɗaɗe naka ,wanda in har baya da ƙuɗi yakan ɗauki abun koma waye ya sayar dan yasha wani abu ko ya bawa Mata,Abba kada ranka ya ɓaci akan wannan amma dai kayi bincike ka samu ya dawo hanyar daidai".Sameer ya ƙarashe maganar hawayen munafurci na ambaliya a kan fuskarsa.Dafe kai Abba yayi yace"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un!,wanne irin bincike zanyi wanda ansan yarda kuke da Mujaheed?,na tabbatar bazaka taɓa masa ƙarya ba,nasan kuma kai mai karesa ne a duk halin daya shiga,sai dai ka sani Sameer bazan taɓa dauƙar wannan shashancin ba, kai kasan halina bana magana biyu,kuma insha Allahu zanyi abunda ya dace a kai."Duƙar da kai Sameer yayi yace"Abba dan Allah karkace ni na gaya maka,bana so zumuncinmu ya lalace ni Mujaheed tamkar wani haskene dake haska rayuwata".kai kawai Abba ya jinjina yace"tashi kaje,ba abunda zai samu zamantakewar ku".Kuɗi ya ibo ya bawa Sameer masu yawa,godiya yayi kafin yabar wurin zuciyarsa fal farin ciki,kai tsaye wurin Mujaheed ya wuce.
    Umma ce kawai a falon,cikin sakin fuska tace "Yarona barka da zuwa,tun ɗazu naga Mujaheed nake cewa to yau kuma ina aka baro mun Sameer ɗin?".kai ya sosai yace"Umma naje gida ne",sosai suka gaisa kafin ya wuce saman bene ɗakin Mujaheed,kare da waya ya sameshi a kunne suna waya da Zalirat,bayansa ya harara kafin yace"yanzu dai Matarmu lokacina ne gaskiya,a barmu mu zanta.juyowa Mujaheed yayi ganin Sameer ya kwanta  gefan gado yasa yayi sallama da Zalirat ya dawo kusa dashi yana kallonsa ƙura masa ido yayi yace"Amini bakaci abinci ba."Be jira cewarsa ba ya janyo kulolin da aka jera masa na abinci ya soma zuba masa,shinkafa ne da miya da naman kaji haka ya cika filat ya miƙa masa sannan ya zuba masa lemu yace"Bismillah."Zaune ya tashi ya soma cin abincin yana kuma nazartar abunda ya kamata yayi a gaba kuma.shikam Mujaheed kallonsa kawai yakeyi yana jin tsantsar son Aminin Abokin nasa.

   *INA MASOYAN JORDERH,YAU GA RANAR NUNA MATA SOYAYYA TAZO KU FITO ƘWANKU DA ƘWALƘWATA KU MATA VOTING DA KUMA KARANTA GAJERAN LABARINTA MAI ƊAUKE DA DARUSSAN RAYUWA DA ƘALUBALE,DAN GIRMAN ALLAH DA MANZONSA IDAN KIN KARANTA KIMUN SHARING*

Вы достигли последнюю опубликованную часть.

⏰ Недавно обновлено: Aug 12, 2021 ⏰

Добавте эту историю в библиотеку и получите уведомление, когда следующия часть будет доступна!

     BAƘIN KUMURCIМесто, где живут истории. Откройте их для себя