SHI NE AJALINA

5 1 0
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
       *SHINE AJALI NA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Story and writing by✍🏻
    *MARYAM ISMAIL*
       (MAJIDADIN KAINUWA)

*SADAUKARWA GA*
     *FATIMA ISMAIL*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

  Page 1

Tsaye take bakin famfo rike da bucket a hannun ta,sai wasa take yi da ruwan da ta diba a ciki,yarinya  ce da ba zata gazawa shekara sha   takwas ba(18),barumaya ce fara ce tas kallo d'aya zaka mata ka gane tsantsar kyawun ta,tana da tsayi amman bata da kiba.jin tsawar Ammi yasa tayi sauri ta juya tana raba ido da jin abunda take fad'a"yanzu abunda kika tsaya yi kenan?,idan na sameki anan ko zaki gane,duk ruwan dake cikin gidan yayi maki kad'an ko?,sai kin fito nan"ta kare maganar tare da juya apartment dinsu .
Rau rau da ido Nauwarah tayi tana kallon bucket din gaban ta da tunanin yama za'ayi ta dauke shi,fitowar Minal yasa tace "please help me with this" tana nuna bucket din.
"Ke dama ae komai baki iyawa,sai shegen son jiki,daga yau ma bazan kuma taimaka maki ba" Minal ta fada tana daukar bucket din,kama mata Nauwarah tazo yi,hararar wasa ta mata tace"daga mun hannun ki a wajen malama"bata jira cewar ta ba tayi ciki abunta.daga baya ta biyo ta tana tafiya kamar kwai ya fashe mata a ciki.
Ammi dake zaune parlo tana cin Apple tace "Lallai Amina ke da kanki kuke kara bata yarinyar nan,sai ki kai mata dakin ta to"
Tana ajiye ruwan ta fito da sauri tana tsoron kar Momynta ta ganta a apartment dinsu Nauwarah tasan me zata iske a gida idan ta koma nasu.
Da sauri tayi gudu ta fada balcony tana raba ido data hango motar Momy ta shigo gidan,wani banzan kallo Nuren ya bita dashi Wanda yake fitowa daga part din zuwa waje rike yake da laptop a hannun sa matshi ne kyakyawa ajin farko be jira me zata ce ba yayi hanyar Apartment din kakarsu da sallama a bakin sa ya shiga d'akin zaune ya same ta akan Chair tana karewa Khaleel ruwan masifa Wanda ko kulata yaki yi balle yasan me take fad'a da ido kawai ya kafeta tace"yo Allah na tuba me ake da irinku shege me idon mayu,wallahi kurwata kur a nafi karfin ka,yauwa Nuren shigo kaga dibar Albarkar da wannan munahikin yake mun".
Murmushi kawai Nuren yayi ya karasa ya zauna ya bawa Khaleel hannu suka gaisa yace to "Inno ae kunfi kusa keda d'an naki,ko na shiga anjima kunya zaku bani,naga kun shirya"
Tabe fuska tayi tace"kai dallah rufamun baki,ae yau munyi na har a bada,kai daga nace yaci abinci shine fa yake mun jaraba,karma Allah yasa kaci"
"Wai bazaki shiru haka nan ba" Khaleel ya fada
Shiru tayi ganin Nauwarah ta shigo ta zauna kusa da ita,"to me akayi maki kuma kika zauna kina haki haka".
"Inno wankin school nayi fa,dukna gaji Allah"
Sakin baki tayi tana kallon ta shekeke tace"wankin ne ya saki haki haka wallahi kinji haushi lusara kawai"
Turo baki tayi tana hararar Inno kafin ta mike ta koma kusa da Khaleel tace"Yaya yaushe ka dawo?"ta kare maganar tana rike hannun shi,kura mata ido yayi bece komai ba yanajin dukan zuciyarsa na tsanan ta lumshe ido yayi cikin murya me kama da rad'a yace"ba jimawa"
"To Yaya ina ice cream dina?"
"Ke bar nan ,kin damu mutane da shegen surutu ,wallahi zan b'allaki yanzu ba jimawa" Nuren ya kare magana a zafafe.
Kallonsa kawai Khaleel yayi ,yayi mata alama da tayi shiru,tuni idon ta ya kawo ruwa tana kallon sa.
Dafe zuciya zuciya Aisha tayi Wanda tunda Nauwara ta shigo take biye da ita,tana kuma jin tsantsar tsanar ta a ranta ,ko kad'an da tana da hali bata so kowa ya kusanci Khaleel amman tasan abu ne mai wahalar samu a gare ta,shine farin cikinta shine abunda zuciyar ta ke matukar so da kauna sai dai kash bema san tanayi ba.ficewa tayi daga wurin ta koma part dinsu tana kokarin boye damuwar ta.
Wata rade ce ta shigo gidan,matashin saurayi ne ya fito daga motar kallo daya zaka masa ka gane tsantsar kamarsa da Nauwarah zubawa gidan ido yayi kafin kai tsaye ya wuce Apartment dinsu Nauwara ya Shiga  da sallama bakin sa,Ammi ta ansa tana fitowa daga kitchen ta tsaya tana karewa Al-ameen kallo tace"ah saukar yaushe ?,bako sanarwa?,to ae ka kyauta"
Murmushi kawai yayi yace"Ammi ina wuni"
Ta ansa da "lafiya", Sosa kai yayi yace" Ammi Nauwarah fa"
"Aekin kenan tana wurin kakarku ae"
"To bara naje yanzu kuwa"da Sauri ya fito ya nufi Apartment din Kaka tunkan ya shiga ya fara kiran" My life ,My life"
Wani irin dagowa Nauwarah tayi tana zuya ido,da gudu tayi hanyar fita dakin ta fada jikin Al-ameen tana kyalkyala dariya da fadin"oyoyo My life"
Shafo fuskar ta yayi yace"kina nan abunki ,ko missing dina bakya yi"
Zaro ido tayi tace"tab Allah Yaya Al-ameen nayi sosai,gashi baka fada mun zaka dawo ba"
Rike hannun ta yayi suka shiga daga cikin dakin yace"y'ar tsohuwa me ran karfe, ana nan ana ja"
Tsuke fuska tayi tace"da Uwarka kake ae,wallahi Aminu ka fita ido na,to har Ubanka Saiya rigani mutuwa kamaji"
Gaisawa sukayi dasu Nuren kafin Khaleel ya fita yabar dakin zuwa Apartment dinsu na Mazan gidan.
Kallon ta Momy takeyi daga sama har k'asa tace "wallahi Minal watan cin ubanki ne ya tsaya a gidan nan,kaji y'ar iskar yarinya ,wato bazaki daina shiga part din can ba,wai ko dai Fatima ta Haifa ki banda labari,kiji kannanki kinga Suns zuwa can?wallahi tunda dai ba kanwar uwarki bace toki rabu da ita" tana kaiwa nan tayi sama zuwa dakin ta tana sababi.
Da sauri ta fita ganin Nuren zai wuce tace "Yaya Nuren"
"Ni mun bata fa,dama kin daina kula ni"
Zaro ido tayi tace"Allah bazan kara bafa,na daina gudu daga yau"
Murmushi yayi yana duban Minal din yace"see ur mom tana kallonki ta sama"
Batayi kuskuren duba sama ba ta runtuma da gudu zuwa part din In no
  Comments zaisa na gane ya maku saina ci gaba.
  Majidadi✍🏻

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 12, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SHI NE AJALINAWhere stories live. Discover now