Chapter 1-2

73 4 0
                                    

༺༻🌹༺༻
࿙꧁꧂꧁꧂࿚
֍

*🇧​ᝪN ᝪN ᝪ...!*
[𝑹𝒖𝒇𝒆 𝑲'𝒐𝒇𝒂 𝒅𝒂 𝑩'𝒂𝒓𝒂𝒘𝒐]

࿙꧁꧂꧁꧂࿚
֍
༺༻🌹༺༻

*Տᴛ⌾ℛℽ & ᗯℛⅈᴛᴛℰℕ*
*ɮ̋ʏ̋✍*
෴ℛαвⅈ́'α𝙩 ѕвѕ෴
❨ცıɠ ɠᵃ̨ι❩

*©®-Aɴᴀ ᴛᴀʀᴇ Wʀɪᴛᴇʀs Assᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ ✍🏻*
▬▬▬▬▬▬▬▬▬▬▬
Jσเɳ ɱε σɳ ωαƭƭρα∂:@Bเɠ-ɠαℓ

𝑫𝑨 𝑺𝑼𝑵𝑨𝑵 𝑨𝑳𝑳𝑨𝑯 𝑴𝑨𝑰 𝑹𝑨𝑯𝑴𝑨 𝑴𝑨𝑰 𝑱𝑰𝑵 𝑲'𝑨𝑰, 𝑫𝑼𝑲𝑲𝑨𝑵 𝒀𝑨𝑩𝑶 𝑫𝑨 𝑮𝑶𝑫𝑰𝒀𝑨 𝑺𝑼𝑵 𝑻𝑨𝑩𝑩𝑨𝑻𝑨 𝑮𝑨 𝑺𝑯𝑼𝑮𝑨𝑩𝑨𝑵 𝑴𝑼 𝑭𝑰𝒀𝑨𝒀𝒀𝑬𝑵 𝑯𝑨𝑳𝑰𝑻𝑻𝑨 𝑩𝑨𝑲𝑰 𝑫'𝑨𝒀𝑨 𝑺𝑯𝑰 𝑵𝑬 𝑨𝑵𝑵𝑨𝑩𝑰 𝑴𝑼𝑯𝑨𝑴𝑴𝑨𝑫 (𝑺.𝑨.𝑾), 𝑾𝑨𝑵𝑵𝑨𝑵 𝑳𝑨𝑩𝑨𝑹𝑰𝑵 𝑵𝑨 𝑩𝑶𝑵𝑶𝑵𝑶 𝑲'𝑰𝑹𝑲'𝑰𝑹𝑨𝑹𝑹𝑬𝑵 𝑳𝑨𝑩𝑨𝑹𝑰 𝑵𝑬, 𝑵𝑨 𝒀𝑰 𝑺𝑯𝑰 𝑩𝑨 𝑫𝑨𝑵 𝑪𝑰𝑵 𝒁𝑨𝑹𝑨𝑭𝑰𝑵 𝑾𝑨𝑵𝑰 𝑲𝑶 𝑾𝑨𝑻𝑨 𝑩𝑨, 𝑵𝑨 𝒀𝑰 𝑺𝑯𝑰 𝑵𝑬 𝑫𝑶𝑴𝑰𝑵 𝑵𝑰𝑺𝑯𝑨𝑫'𝑨𝑵𝑻𝑨𝑹𝑾𝑨 𝑭𝑨𝑫'𝑨𝑲𝑨𝑹𝑾𝑨 𝑮𝑨𝑴𝑰 𝑫𝑨 𝑻𝑼𝑵𝑨𝑺𝑨𝑹𝑾𝑨. 𝒀𝑨𝑫𝑫𝑨 𝑵𝑨 𝑭𝑨𝑹𝑨 𝑺𝑯𝑰 𝑳𝑨𝑭𝑰𝒀𝑨 𝑨𝑳𝑳𝑨𝑯 𝒀𝑨 𝑺𝑨 𝑵𝑨 𝑮𝑨𝑴𝑨 𝑺𝑯𝑰 𝑳𝑨𝑭𝑰𝒀𝑨.

*🌹ℙaℊℰ❏☞1-2*

Dandazon al'umma ne cike a wannan waje, ko ina ka waiga dubban mutane kad'ai kake gani, hayaniya da hargitsi ya ishi kowa, batun tafiya kuwa kowa bangazar d'an uwan tafiyarsa yake.

Wata doguwar mata bak'a na hango wadda ba za ta gaza kimanin shekaru Talatin da biyu ba, sanye take da doguwar riga bak'a da hijabi bak'i, hannunta na dama rik'e yake da wata tsaleliyar yarinya fara kyakkyawa mai kimanin shekaru goma sha d'aya, ya yin da hannunta na hagu ke rik'e da wata k'atuwar leda bak'a me nauyi.

Tafiya suke cikin sauri duk da irin cikowar da ke wannan waje hakan bai hana ta fincikar hannun yarinyar ba, har sai da suka isa dai-dai wajen wani dattijo tukunna suka tsaya, yarinyar na nurfarfashi alamar gajiya.

Wata k'atuwar leda dattijon ya d'auko ya mik'a wa wannan mata ya yin da ta karb'a sai ta kuma had'a su waje guda da d'aya ledar dake hannunta na hagu ta rik'e su a hannu d'aya, sannan suka ci gaba da tafiya.

Duk da irin nauyin kayan da take ji hakan bai sa ta ajjiye kayan ta huta ko kuma ta saki hannun yarinyar data rik'e ba, har sai da suka isa bakin titi tukunna ta saki hannun yarinyar ta maida kayan hannunta na dama dan ta samu ta huta, ta rik'e yarinyar da d'aya hannun na hagu.

Sun juma a tsaye tana jiran abin hawa, sakamakon duk wanda ta tsayar sai ya ce ba zai je inda ta kwatanta masa ba, da k'yar dai ta samu wanda ya amince da zai kaita inda take so ta je.

Cikin k'ank'anin lokaci mai 'Napep' ya isa inda ta k'watanta masa, duk da irin nisan da wajen ke da shi, hakan bai sa ya b'ata lokaci wajen kai su ba har suka isa. Dai-dai k'ofar wani gida ya kawo su wanda yake da farin 'gate', babu fenti, sauka suka yi sannan ta sallame shi ta d'ibi kayanta kana ta ja hannun yarinyar ta rik'e suka shiga ciki.

Sallama take yi amma babu wanda ya amsa dan haka suka k'ara yin gaba sannan suka hango wani 'gate' d'in suka shiga, nan ma ta sake yin sallama a karo na biyu amma babu wanda ya amsa, sai da ta jera sallamar kamar sau uku a karo na hud'u ta ji an amsa, dan haka sai ta shiga ba tare da jiran iznin shiga ba, su ka ci gaba da tafiya har suka hango wata k'ofa.

Tun kan su k'arasa bakin k'ofar d'akin wata mata me jiki ta fito tana kallonta ta fara washe baki suka kalli juna sosai na wasu 'yan dak'ik'u kafin ta basu izinin shiga ciki, duk da haka ba ta saki hannun yarinyar da ta rik'e ba tana rik'e da ita daga bisani kuma Matar ta basu damar shiga cikin d'akin.

Gida ne babba wanda ya ke makeken gaske sai dai kuma babu kowa ciki face wannan mata da ta fito.

Shigarsu cikin d'akin ke da wuya tun kan su zauna matar ta ce "Idan na fad'a dai-dai ke ce Halima wadda aka ce za ki zo yau da misalin sha biyu na rana?" Halima na murmushi ta ajjiye kayan da ke hannunta gefe guda, sannan ta saki hannun yarinyar ta nemi waje ta zauna tare da cewa "K'warai kuwa baki b'ata ba ni ce, ina fatan ban makara ba, dan na yi mamakin yadda na iya gane gidan duk da cewa wannan shi ne zuwana na farko".

Duk wannan maganar da su ke yi yarinyar na tsaye ba tare da ta zauna ba, har sai da Halima ta kalleta tukunna ta nemi gefe guda ta zauna. Matar ta kuma cewa "sai dai kin haura lokaci domin kuwa yanzu sha biyu da rabi da minti biyar dole sai dai ki dawo nan da misalin k'arfe hud'u na yamma, kafin wannan lokacin ak'wai gida da zan k'watanta miki za ki fara zuwa sannan ki wuce, sai dai ki samu ki tafi yanzu dan kar ki je ba ta nan. Idan kin je ki ce Laure ce ta turo ki", kafin ta ce wani abu
suka jiyo hayaniya tamkar daka sama, yarinyar da ke gefe guda a rakub'e duk ta tsorata.

Halima ce ta fara magana "Ina fatan dai lafiya? domin na ga unguwar babu kowa amma kuma yanzu na jiyo hayaniya kar dai ace wani hargitsin ne ya tashi?" Laure ta ce "Ki kwantar da hankalinki babu wani abu kawai ki tashi ku wuce yanzu zai fi", nan dai suka yi sallama da Halima ta k'watanta mata inda za ta je, sannan suka wuce bayan ta kama hannun yarinyar ta rik'e.

Ko da suka fita ba su ga alamar motsin kowa ba duk kuwa da irin hayaniyar da suka ji, dan haka suka d'auki hanya wadda za ta kaisu ga samun abin hawa, domin wajen shuru ne babu alamar motsin kowa bare a yi tsammanin samun abin hawa, sai fili da ciyayi.

Tafiya ce me nisa wadda ba ka iya hango k'arshenta.

Suna cikin tafiya suka hango wani 'keken Napep' babu kowa ciki, dan haka Halima ta yi gaggawar tsayar da shi, bai sauraresu ba ya wuce, suka ci gaba da tafiya, da gani yarinyar ta gaji amma Halima ba ta bari ta huta ba, suna cikin tafiya suka kuma ganin wani me 'keken Napep' d'in da sauri ta kuma tsaida shi nan dai ta ci sa'a ya tsaya ta kwatanta masa inda zai kaisu sannan suka shiga ciki.

Tafiya yake tamkar wanda zai bar gari bai tsaya ko ina ba har sai da suka isa k'ofar wani gida me jan k'yaure wanda ba yabo ba fallasa shi ba k'arami ba, kuma ba babba ba, ta sallami me Keke ya wuce su kuma suka shiga ciki, tun kan su k'arasa ta mik'a wa yarinyar kaya d'auri guda ta rik'e duk da irin nauyin kayan da yarinyar ke ji haka ta rink'a k'ok'ari dan kar su zube har ta isa bakin k'ofar zauren k'arshe, sannan Halima ta karb'i kayan ta rik'e da kanta, ta kuma kama hannun yarinyar ta rik'e.

Suna shiga kai tsaye wani sashi ta nufa wanda babu kowa ciki babu kuma motsin kowa duk da gidan ba wani me girma bane amma kuma yana da fasali domin an yi masa kwanoni iri daban-daban, dan wanda bai san gidan ba tsaf! zai iya rikicewa, ko ita kwatancen da aka yi mata ya sa ta rink'a ganewa.

Sai da suka shiga ciki sosai sannan suka hango wata dattijuwar mata zaune a kan kujera kamar me jiran isowarsu. "Sannu Halima" kalmar da tsohuwar ta furta kenan cikin muryar tsufa wadda za ta haura kimanin shekaru saba'in ko tamanin a duniya, ta kalli yarinyar da ke rik'e a hannun Halima ta ce "Wannan ita ce Rumaisa?" d'aga kai kawai Halima ta yi alamar Eh! Ita ce kafin ta shiga cikin falon da ba shida haske sosai ta zauna tare da yarinyar. Sai da yarinyar da aka kira da Rumaisa ta durk'usa k'asa ta gaishe da dattijuwar sannan ta shiga ciki.

Dube-dube kawai yarinyar take alamar ba ta tab'a zuwa gida irin haka ba sai a wannan lokaci.

Suna shiga Halima ta fara k'ok'arin cire mayafi tare da ajjiye kayanta gefe guda.

Dattijuwar matar da ke zaune ta mik'e ta shiga falon hannunta ruk'e da kofi da ruwa kalar d'orawa ciki ta bawa Rumaisa ta ce ta sha, Rumaisa ta karb'a sabida tsananin k'ishin ruwan da Rumaisa ke ji ya sa ta yi saurin kurb'ewa, dattijuwar ta yi murmushi cikin muryar tsufa ta ce wa Halima "Bana so ki zo ki yi da kin sani anan gaba idan har kin amince da hakan babu wata matsala" "Halima ta ce "Babu wata matsala ni na amince da ko ma mene" Tsuhuwar ta k'ara cewa "wad'annan su ne kayan da kika je kika karb'o?" Halima ta d'aga kai alamar su ne, tsohuwa ta ce "za ku iya tafiya zuwa lokacin da Laure ta sanar da ke", Halima ta kad'a kai ta bar kaya ta ruk'e hannun Rumaisa suka mik'e suka fita............✍🏻


*_𝐘𝐚𝐰𝐚𝐧 𝐂𝐨𝐦𝐦𝐞𝐧𝐭 𝐘𝐚𝐰𝐚𝐧 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠.......👌🏻_*


🌹☞ℬıɠ ɠᗅ̨ι *¢ɛ✍🏻*

BONONO...! [𝑹𝒖𝒇𝒆 𝑲'𝒐𝒇𝒂 𝒅𝒂 𝑩'𝒂𝒓𝒂𝒘𝒐]Where stories live. Discover now