Ni Da Aminiyata

18 1 0
                                    

*Ni Da Aminiyata*
Na
*Fatima Saje*

Bismillahir-rahmanir-rahim, dukkan godiya da yaɓo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai komai wanda cikin amincewarsa ya bani ikon fara wannan rubutu. Salati marar adadi ga fiyayyen halitta manzon rahama sallallahu alaihi wasallam.

Fatan Alkhairi gareku 'yan uwa da abokan arziki harma da sauran al'umar musulmai baki ɗaya. Ina matukar farin ciki da bibiyar rubutuna da kuke yi ba tare da gajiyawa ba.

Har kullum tsokacinku na da matukar mahimmanci a gareni, kuma ba zan gajiya ba wajen dakon shawarwari, gyara ko korafi daga gareku.

"Ni Da Aminiyata" labari ne daya faru da gaske ma'ana (True life story), sai dai na canza wasu ababe kamar suna da kuma salo.
Ban fara wannan rubutun ba sai da na samun lasisin yadda daga gurin wacce labarin ya shafa. Ban yarda ayi amfani da rubutu na ba, batare da izini na ba.

❤

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

❤......👩👨👩......❤

"Maman nawwara kin fiye saiɓin fita unguwa wallahi, tun ɗazu na shirya ina jiranki amma haryanzu baki gama ba!"  Maman Nawal ta faɗa.

"Yi hakuri please, saura kaɗan na gama kin sannifa abun gaggawa baya yiwuwa dani. Kuma haryanzu akwai sauran lokaci ba zamu makara ba in sha Allahu." inji maman Nauwara.

"Hm ai na san akwai lokacin amm kuma wanda zai kaimu unguwar baida lokacin jiranmu."

"Subahanallahi! Kar dai Baban nawal ne zai kaimu?"

"Kwarai dagaske, kuma yanzu haka yana mota yana jiranmu."

Ni Da Aminiyata Where stories live. Discover now