WATA DUNIYA P 11&12

7 0 0
                                    

.⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️

⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️

LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
(ƳAR GATAN MAMA)

Marubuciyar......

A WANI GIDA
RAYUWAR MU!
MAGANIN KAR AYI!
nd now...... 

⚔️WATA DUNIYA⚔️

⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga  shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

NA SADAUKAR DA WANNAN LABARIN GABA ƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ALLAH YAJA DA RAI YAƘARA LAFIYA AMEEN.

⚔️🌍⚔️🌍⚔️
SHAFI NA 11&12
⚔️🌍⚔️🌍⚔️

Na sadaukar da wannan shafin baki ɗayanshi gareki AUNTY SAILUBA Allah yabar ƙauna😘😘Son So fisabilillahi😍😍.
Comment ɗinki nasani nishaɗi😘😘⚔️⚔️⚔️.

⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️

Gaba ɗayansu suka juyo atare suna kallonta jin tambayar da tayi.MUSLIMAT ce tai karaf ta kalleta tare cemata......

"Shin bakiji bayanin da akayimiki game da girman iyaye bane kike wannan kalami akan mahaifinki?ko kuma har yanzu baki gane bane ba"

Murmushi GIMBIYA ZULMAT tayi mai sauti wanda saida fararen hak'oranta suka bayyana kana ta kauda kai daga kallon MUSLIMAT tamaida kallonta ga SARAUNIYA SINIYYA tace ..... 

"Yake shugabata! Alfarmar canzamin masauki da kikace zakiyi ɗazu inamai tabbatar miki dana samu masaukin da nakeson zama"

Kallonta SARAUNIYA SINIYYA tayi tare da maidata mata murmushi mai sauti sannan tace.....

"Ina ne masaukin naki ya baƙuwata?"

"Inda JARUMI MUSLIM yake da zama nan ne masaukin naw....."

"A'uzu billahi minash'shaiɗanir'rajeem! Kin saɓa lamba,domin baki faɗi abinda zai yuwuba sam! Inaso tun wuri kijanye ƙudurinki akan MUSLIM domin zuciyarsa bashi da gurbin da zai ajjeki acikinta,zuciyarsa tawa ce ni ɗaya babu wajan ajjek....... "

MUSLIMAT ce tsaye kan ZULMAT tariƙe ƙugu tana haki kamar wadda tai tseren doki.

Wata sassanyar ajiyar zuciya ZULMAT ta sauke yayinda ƙasan zuciyarta ke ayyana mata wasu abubuwa game da MUSLIM dama ita kanta MUSLIMAT ɗin,ƙasa ta sake yi da kanta tare dasa hannunta tana jujjuya zoben azurfar dake maƙale aɗan yatsanta.

SARAUNIYA SINIYYA kam cike da ɓacin rai takalli MUSLIMAT tare da faɗin.......

"Ashe daman baki da hankali? Meyasa bazaki magana cikin tausasawa ba? Kifita daga nan kibamu guri bamason mukuma jin wata magana daga bakinki.......

⚔️🌍⚔️🌍⚔️
Cike da ƙwarin gwiwa NUJBEER ƊAN NAJABURU ya amsa tare da bin wani bafade suka nufi inda aka bashi amatsayin masaukinsa.

Bayan tafiyarsa SARKI KAMALUD-DEEN yai shiru inda ƙwak'walwarsa tashiga kaikawo game da lamarin wannan tsoho,a haka dai zaman fada nayau yatashi jiki asanyaye domin shi lamarin tsohon yafirgita shi,kallon waziri sarki yayi tare da faɗin.....

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 01, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

WATA DUNIYAWhere stories live. Discover now