01

26 3 0
                                    

*🌺RANA DUBU...🌺*   
*~A KINGDOM AND ROMANTIC LOVE STORY~*

_STORY AND WRITING BY_
*©️®️JAMEEY*

_M W A_

_WRITER OF_
*NIDA UWARMIJINA*
*BUƊARƊIYAR SOYAYYA*
*DA'IMAN ABADAN E. T. C*

_20/9/2023_

001

*MASARAUTAR MALI*

*2:30am*

Cikin kuka da zafin raɗadin haihuwa ta kamo hannun wata mata dake gefenta tana aikin hawaye,kallon ɗaya zakayi masu ka gane yanzun yanzun mai haihuwar tayi ta,dan ko uwa bata daɗe da fitowa ba,kuka take cin karfinta dan ko motsi daƙal take yin shi ga jaririn da yake ta kuka tun da ya fito duniya ta ɗauka tana mai kurama fuskarshi ido tausayinshi ne ya kamata ya shigo duniya mai cike da ƙalubale da kuma sarƙakiya iri iri..balle a inda a haifeshi gidan sarauta, gidane mai cike da qaddarori daban daban..ta tabbata idan har ta bar wannan yaron a wannan gidan mugayen mararsa imani ba zasu taɓa barin yaron yakai labari ba, saboda wani buri nasu marar taushe da kuma rashin imani da rashin tausayi da ya baibaye zukatansu..dan ba imani ne da su ba balle har zasuji tausayinshi,duba da durowarshi duniya kenan...Ba abinda suka sa a gabansu sai neman duniya da abinda ke cikin ta,dan sam basu tunawa da mutuwa balle kuma ranar tsiyuwa ranar kin dillacin amman tasan komai daren daɗewa gaskiya zatayi halinta dan ance *RANA DUBU* ta ɓarawo  *RANA ƊAYA* tak ta mai kaya,tana addu'ar Allah ya nuna mata *RANA ƊAYA* Ranar da gaskiya zatayi halinta,jona mashi nono tayi ya fara tsotsa ganin mudun tace zata barshi yasha nono to mutunen nan zasu iya dawowa su taddasu zare baƙin nonon tayi daga bakin yaron,kuka ya tsalla jin ta cire nonon waigawa tayi tana kallon matar da ke tsungune a gabanta kanta a ƙasa yake tana hawaye girgiza kai kawai tayi..a hankali ta buɗe bakinta sai kuma sauke ajiyar zuciya,murmushi ta sakar mata tana mai kamo hannunta ta ɗaura mata yaron samun hannunta tace.

"FATIMA"

Ɗago kanta wanda aka kira da FATIMA tayi tana mai kallon yaron da FAUZAJ RAHMA ta ɗaura mata a hannu, cikin rawar jiki da ƙarmar baki dan jikinta ba inda baya rawa tsabar tsorata da shiga firgici daƙyal ta iya haɗa yawau bakinta ta samu ta taitaro sauran natsuwarta tana cewa.."Na'am Allah ya ƙara maki girma da nisan kwana da lafiya yake ke uwar gajiyata  FAUZAJ RAHMA."Murmushi FAUZAJ RAHMA tayi tana sakar mata yaron tana cewa."na yarda dake Fatima kin wuce duk yanda kike tunani a wajena." Dan shuru tayi tana share hawaye masu zafi da suka zubo mata tana cigaba da cewa.."na tabbata duk kulawar da zan ba wanann yaron ke ma zaki ba shi,kuma duk soyayyar da zan nuna mashi kema zaki nuna mashi irinta koma fiye da ita,tarbiyar da nike mafarkin bashi kema zaki bashi ita har ma fiye da tawa..dan haka ga amana nan baki ki kula da shi ki mandashi ɗan da kika haifa da cikinki,kin san komai ba sai na tsaya gaya maki ba duk da kasancewar ki *HAKAZAUGA (BAIWA)* a gidan nan kuma ban san kowa naki ba, yarda dake da nayi da kuma tarbiyyarki zan baki amanar yaron nan karki maido shi masarautar nan har zai ya zama mutun ya mallaki hankalinshi kema ban ce ki sake dawowa Masarautar nan har sai ranar da *RANA DUBU* zata cika,ranar da gaskiya zata zama gaskiya ki gaya mashi baya da ƙurar da ya bari ki gaya mashi ƙalubalen da zai turƙara watan watarana."

Kuka sosai FATIMA ta fashe da shi tana zubewa ƙasa tana cewa.."Tuba nike yake uwargiyata tabbas wannan al'amari da ruɗu yake da kuma ɗaurewar kai,tabbas *KAZAUWAFA(YARIMA)* abun tausayi ne ace ranar da kazo duniya ko nonon mahaifiyarta baka tsotsa da kyau  ba a raba ka da ita,nayi maki alkwarin riƙe amanar da kika bani sai na saka maki hallaci da hallaci yake FAUZAJ(GIMBIYA)"..Haɗewa sukayi waje ɗaya suna kuka, cikin kukan FAUZAJ RAHMA take cewa.."Maza tashi ki tafi kafin su dawo nasan komai suke yanzun sun kusa isowa wajen nan jikina ya bani maza tashi ki tafi Allah ya tsareku da tsarewarshi." Rufe bakin FAUZAJ RAHMA keda wuya aka fara kwankwaso kofa, zabura FATIMA tayi tana yin hanyar baya da yake ba inda bata sani ba a cikin Masarautar Mali dan shekararta 20 tana aiki a cikin Masarautar a ƙarƙashin FAUZAJ RAHMA,tana shan wata kwana suna shigowa cikin ɗakin.

RANA DUBUWhere stories live. Discover now