Page 1

4.6K 240 27
                                    

🍒🍒🍒 🍒🍒🍒

🍇💦 💦🍇
*ALKHAIRI NA*
🍇💦 💦🍇

_JANUARY 2019_

📝 _Written by DEEJA_ 👄

_Bismillahi rahmanirrahim_

*PAGE 0⃣1⃣*

*SHAGARI*

Kaman yanda kowa ya sa ni mafi yawan mutanen dake rayuwa a garin fulani ne, daga bak'ak'e har farare sai dai kuma mafiyawansu bak'ak'en fulani sun fi yawa a k'auyen. Gida ne d'an babba kad'an wanda yake da watar tsakiyar fili, sai dai a kallon fari zaga gane masu rayuwa a cikinsa ko na kad'an basu had'a hanya da tsafta ba, saboda yanda gidan yake kaca-kaca uwa gurin da dabbobi ki rayuwa. Gefe d'aya shirgen tulin bolane wanda shi ya k'ara taimakawa gurin haukata gidan, ga shirgen tsumma karan dake warwatse a gidan, wa'anda suka cakud'e da kwanukan cin abinci wa'anda suka barbaza ta ko'ina a gidan, wata 'yar yarinya na hango raku6e a filin gidan wacce a k'iyasce ba zata wuce shekara goma sha biyu ba a duniya, rarraba ido kawai take tana kallon tsakiyan filin gidan kawun nata, wanda shararsa ya zame ma ta ibada k'ara ware idonta tayi ganin yanda aka haukata filin gidan wanda mutum zai iya rantsewa da Allah tun tarihin gina gidan bai ta6a ganin sharaba, sai dai ina kulli yaumin ta Allah sai an masa shara tasss, wacce da gangan ake haukata sa saboda kawai a bai wa wannnan 'yar matashiyar yariya wahala......... Tassssss saukar marin da aka falla ma ta ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin tausayin kanta da ta fad'a.

"Wato dan uwarki ba zaki tashi kiyi aikin da kikasan rashin yinsa kaman rasa numfashin ki ne a gidan nan ba ko?" Wata guntuwa kakkaurar mata ce ke magana, lokaci d'aya jikin wannan yarinyar ya d'auki wani irin k'yarma tashi tsaye tayi cikin yanayinta na sanyi ba tare da tace komai ba ta d'au 'yar tsintsiyar da ake sharan gidan ta shiga aikinta, koda ta samu ta kammala sharan ba sai an gaya maka a mugun jigace take ba tulin kwanukan dake jiranta ta shiga wankewa wa'anda ko babbar mace ta wankesu tabbas za a jinjinawa bajin ta irin ta ta. Gama wannan wanke-wanken ke da wuya naga an watso ma ta tulin kayan yara wanda tsaban datti kace daga cikin k'asa aka fitar dasu, tayar da kanta tayi ta dubi wacce ta jefe ta da kayan, nima mayar da hankalina nayi in da naga ta kallah abinda zai baku mamaki ba macen da ta sanyata shara bace wata ce daban, matar da ke tsaye a gabanta sai wani kallon wulak'anci da k'ask'anci take jifan yarinyar da shi.

"Maza kiyi sauri ki wanke min kayan nan ki je ki kai min markad'ena sauri nake in d'aura sana'a ta." Matar ta fad'a tare da juyawa baya abinta tayi tafiyarta, yanzun ma yarinyar ba ta ce komai ba shirun dai tayi sai wasu siraran hawayen dake fita daga gurbin idonta, bayan hannunta ta sanya tare da share hawayen, wa'anda aikin banza ne dan kuwa k'ara zubowa kawai suke, guga ta sanya a cikin rijiyan dake gabanta ta yanyo ruwa haka ta shiga wankin tana janyo ruwa tana wankewa, a haka har ta samu ta gama wankin kayan yaron dake d'auke da kashi da majina, shanya kayan tayi a igiyar dake d'aure a tsakiyar gidan kallonya ka d'ai zaka y ka gane a mugun gajiye take a hankali ta janyo ruwa ta wanke hannayenta da k'afafuwanta sai fuskanta da ta wanke, wasu mataccin silifas d'inta ta sanya a hankali ta fara tafiya zuwa k'ofan d'akin Amina tsaye tayi ba tare da ta furta ma ta komai ba harara Amina ta banka ma ta cikin takaici ta furta.

"Wannan shegiyar wannan shegiyar munafukar yarinyar bansan a ina ta kwaso wannan bak'in halin ba, yanzun ma magana bazaki iya yi mun ba toh ga markad'en nan na jiranki ke ce dai zaki kai sa koda a ce mutuwa zaki yi a can, banza mai halin solo6iyar saunar uwarta." Matar ta fad'a tare da jefa ma ta naira ashirin kud'in markaden d'aukan kud'in tayi da kwanon markad'en ta juya ta fita tana hawaye sosai take jin ciwo da k'unci duk lokacin da aka zagi mahaifiyarta wacce ko ganinta bata ta6a yi ba, amma a haka take so da k'aunar mahaifiyar ta ta, bata tsaya ko'ina ba sai gurin Idi mai markad'e, layi ta shiga har ya kai gunta ana gama mata markad'enta ta dawo gida, inda aka d'aura ma ta dafadukan da take siyarwa wanda ba a 6ata lokaci gurin dafata ba nan aka dank'ara ma ta roban tallanta ta fita ba tare da taci komai a cikinta ba dama idan da sabo ta saba da hakan.

ALKHAIRI NAWhere stories live. Discover now