BABI NA D'AYA

159 3 0
                                    

[2/18, 10:08 PM]
💥💥💥         💥💥💥
❤❤❤          ❤❤❤

          *ALEESA*

💥💥💥         💥💥💥
❤❤❤          ❤❤❤

*DAGA ALK'ALAMIN*
*XARAH BINTMUHAMMAD*✍🏻
              *DA*
*SOPHIE GALADANCHI*✍🏻

          *DU'A FOR SUCCESS*✨ 

*"O ALLAH,LORD OF GABRIEL, MIKHAIL AND ISRAFIL, CREATOR OF THE HEAVENS AND THE EARTH,SHOWER OF THE UNSEE AND THE SEEN,YOU WILL JUDGE AMONG YOUR SLAVES CONCERNING MATTERS WHEREIN THEY DIFFER.GUIDE US BY YOUR PERMISSION TO THE TRUTH OF THOSE MATTERS WHEREIN THE DIFFER, FOR YOU GUIDE WHOM YOU WILL TO THE STRAIGHT PATH."AMEEN*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
 

              *PAGE 1*

Wata Mota ce k'irar Mercedes benz G wagon ke tafe a hanya a hankali ta doshi unguwar maitama dake Garin Abuja around 2:30pm,wani katafaren gida Naga motar ta dosa Wanda ko a cikin unguwar ma babu gidan daya kai shi haduwa,tsari,kyau,girma da kawata gidan sosai da sai kace ba'a nija ba.

Tun kafin motar ta k'arasa bakin gate d'in gidan driver ya fara dannan oda,ai ko da sauri gate man ya tashi da sauri ya bud'e gate din yana jiran k'arasowar su.

Suna shiga harabar gidan direct parking lot driver ya yi parking,Bayan ya fito ya yi sauri ya zagaya ta b'angaren Mai zaman banza ya bud'e mata door d'in motar.

Bayan ya bud'e mata motar ya yi sauri ya matsa gefe d'aya ta yanda zata fito,kaman bazata fito ba can Sao ga k'afafunta ta sak'alo waje tana wani yamutsa fuska kaman wacce taga wani Abun k'yama.

Bayan ta fito daga motar ta kama hanya zata shiga cikin gidan,har zata shiga main parlor din gidan sai ta juyo tace da drivern "sani na bar skul bag d'ina a Mota ka shigo min dashi cikin gda" yace OK hajia angama,sannan ta shiga daga ciki.

kukan shagwab'a ta shiga dashi tana dira k'afafu a k'asa kaman wata yarinya k'arama,taji shuru, Koda ta waiga ba kowa a parlorn se k'arar TV dake tashi,katafaren parlorn ne Wanda yaji kayan k'awa sai kace a k'asar waje,komai na parlorn white and ash ne,wasu manya manyan kujeru ne ke cikin parlorn har set uku,duka kayan dake cikin parlorn k'irar kayan dubai ne,yaji kayan more rayuwa kamar ba gobe ,canta lura cewa ba kowa ciki sai ta wuce direct d'akin ta.

"Palo ne da d'aki, kujerun Palon har sun fi na Palon farko had'uwa, k'uryar d'akin ta Shiga Bayan ta zame  d'an kwalin dake Kanta, Wani makeken gado ne na hango cikin D'akin Wanda kana ganin shi kasan naira ta yi kuka a wajen,d'akin ya k'awatu da kayan ado masu tsada, komai dake d'akin milk color ne, tana shiga d'akin ta fad'a Kan bed din tana kuka,tana cewa "am tired of this school wallahi,kullum school mutum bayada hutu gaskiya ni na gaji, Bari daddy ya dawo fada mishi zan a fitar dani gaba d'aya cos bazan juri zuwa ba."

"Tana nan tana kukan nata na shagwaba taji an turo door din d'akin nata,da sauri ta d'ago kanta Dan ganin Mai shigowa,mahaifiyar ta ce kawai sai ta k'ara fashewa da wani matsanancin kuka tareda da mik'ewa tsaye ta fad'a jikinta,"lafiya ALEESA meke faruwa ne kike wannan kuka haka sai kace wacce akama mutuwa?" ta janyo hannunta suka zauna Kan bed,ALEESA tace cikin kukan shagwaba "momy na gaji da zuwa school d'innan wallahi,ace kullum mutum baida hutu tun safe ka tashi ka shirya ka tafi school ba zaka dawo gida ba sai around 2pm koma fiye,kuma Dana dawo ko Gama hutawa ba zanyi ba za a ce in fito ga malam yazo min karatu, haka zanta rayuwa kullum ba hutu",ta k'arasa fad'ar maganar tare da cinno bakin ta gaba.

Momy tace "haba auta me kike so ki maida rayuwarki ne?ace duk Abnda zai amfane ki bakiya so,duk cikin frnds naki Kinga wacce take son maida yaruwar ta baya kaman ke?lafiya lau suke zuwa skull su dawo haka islamiyya duk zuwa suke,Amma banda ke bokon ma nema yake ya gagare ki na islama din kince bazaki Iya xuwa skull ba aka Nemo miki malamin dake zuwa har gida yana koya miki but u re still complaining cewa an takuraki,why? Ko kinaso Jawad ya dakeki?".

Girgiza kai Aleesa tayi  saboda tasan Jawad baya d'aga mata K'afa b'angaren karatu, dakansa ya nemo dorina Mai baki biyu yaba malaminta dake koya mata karatu a gida idan taki maida hankali ya zaneta.

Suna cikin wannan maganar aka yi nocking din D'akin aka shigo momy tace yauwa gwara da Allah ya kawo ka ma,da suri AlEESA ta d'ago kanta tare da da zare manya manya golden eyes d'inta.

Jawad ne ya shigo, d'akin ya bi da kallo takalmi da Safa a k'ofar d'aki dama tun a Palo yaga D'ankwali a k'asa.

"kin saba duk lokacin da malam yazo sai ya jira an zo kiranki, daga  yau karki sake barinshi a tsaye, ki tashi kiyi abinda zaki yi kafin ya iso".

Ya kalli mahaifiyarsu yace "momy ina tunanin maida yarinyar nan islamiyya gaskiya, banga tana karatu yadda ya kamata ba".

Girgiza masa kai kawai ta yi alamar ta yadda saboda tun farko baiso aka cireta da islamiyyan data keyi ba, bai k'ara magana ba ya fita.

Tana tsoronsa shiyasa ta mik'e ta shiga toilet momy ma fita tayi daga d'akin.

Toilet d'inta ma abin kallone, k'ofar shiga wurin wankan control takeda, famfon dake cikin Jacuzzi d'in abin kallo ne, nidai banga wurin da ta danna ruwa ya fara fita ba na daiga fitar ruwan, ta daidaita zafin ruwa Bayan ta zuba turaruka masu kamshi aciki, shiga ruwan ta yi bayan ta warware gashinta daya zuba har bayanta, remote control naga ta d'auka ta danna, koda na juya ashe TV ne a wurin, lumshe idonta tayi tana jin yadda zafin ruwan ke ratsa jikinta.

*muje xuwa*........

ALEESAHWhere stories live. Discover now