TA MAIGARI

3.5K 107 23
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀

          *TAME GARI*
              
                 *NA*
     *KHADIJA USMAN*
       (Real  ta maigari)

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

1️⃣_2️⃣

   "Na rantse da Allah bazan yadda ba sai an biyani niƙana" Yarinyar ta faɗa tana gunjin kuka.

    "Kin isa ma, wallahi kika sake kika je kika faɗawa innata, yaseen sai kinci ubanki "cewar dije dake ƙara tattake garin dake zube a ƙasa.Sannan taci gaba da faɗin,
  " kuma an ɓarar din duk ranar da kika ƙara cemin dijangala tame gari tuwon gidanku ma zanje in ɓarar wallahi".

   Su Shatu dake gefe suna kallo ba damar suyi magana dije taci uwarsu, dan haka sukayi gum ko yi haƙurin sun kasa faɗa. Hafsi kuwa sai rizgar kukanta takeyi ,dan tasan yau idan taje gida kashinta ya bushe gurin delu, dan saita mata dukan mutuwa kuma tasa ta nemo mata wani garin, Koda ta tuna ai saita ƙara bare baki.

    Dije ce ta kalleta tace ,"wai ke uwar me nayi miki da kiketa min wannan kukan ,danma ban faffasa miki baki ba hegiya me idon gyada".

   Shatu ce ta ƙaraso kusa da ita tace "kin san Delu dukanta zatayi idan taje gida kin san dai ba imani ne da ita ba".
  Shuru Dije tayi na dan wani lokaci, kamar wadda ta tuna wani abun sannan kuma tace,
  " toh kinga ke kika jawo wa kanki tunda kika tsokane ni, amma kiyi haƙuri kinji ,tahi nasan yadda zamuyi amma sai kin bani haƙuri".
  Da sauri Hafsi tace" Dan Allah kiyi haƙuri".

"Toh naji ya sunana?"

  "Anti dije".Hafsi ta faɗa da sauri.

  Wani farin ciki ne ya mamaye zuciyarta, dan tana masifar son sunan nan na ƴan binni,dan haka da sauri tacewa Hafsi ,got,o muje gidanmu in baki dawar ki ƙara kai wani niƙan".

  Da sauri Hafsi ta miƙe dan tasan ko yanzu takai niƙan sai ta ci ubanta,saboda jimawar da tayi, dan haka da sauri suka nufi gidansu  Dije. Koda suka je Dije bata ɓoyewa inna saudi komai ba, aikuwa ta basu dawa suka kai niƙa,har gida Dije suka raka Hafsi aikuwa delu kamar ta ari baki taita jarabar ta, dayake ƴan dukan basa kusa, sun dai samu rabon zagi amma bata daki Hafsin ba.

*************************
     Mota ce Ƙirar honda Accord LC  ta shigo cikin garin Gawo ,kasancewar rashin kyawun hanyar ga kuma da alama wanda ke cikin motar yasha tafiya. Mutum biyu ne ciki matasan samari kyawawa, daka gansu kaga waɗanda hutu da nera suka zauna a wajen.

    Tuƙi yakeyi kamar wanda aka yiwa dole, kafin ya waiga ya kalli ɗayan yace cikin kasalalliyar muryarsa.
   "Habeeb wlh nagaji dayawa ,na matsu mu qarasa cikin garin nan in yada zango kan gadon tsohon nan ".

   Wanda aka kira da Habeeb yayi murmushi kafin yace" hmm! kaima kenan ,bare kuma ni dana sha tafiya kwanan nan, gashi yau ma son ganin wannan me ran ƙarfen yasa na biyoka".

  "Kai dai bari !ai wannan tsohon inaga roƙon Allah yakeyi mana, shiyasa bama iya ɗaukar lokaci bamu ganshi ba, ko daddy ma fa kullum shi batun shi baba malam, kusan koyaushe yana kan hanya".Cewar Habeeb daya ƙarasa maganar Yana Mai gyara zamansa sosai a gefen Mai zaman banza.

"Toh Allah yaja da kwana dai".Naseer ya faɗa yana Mai ƙara maida hankalinsa ga tuƙi.

"Ameen ya Allah".Habeeb ya kuma cewa.

*****************************

TAME GARIWhere stories live. Discover now