ALLU TA TONO GARMA

9 0 0
                                    

Fawaz yayi matukar fusata kan abinda Muhsin yayi masa na tozarci, shigowa gida yayi ko sallama babu kai tsaye ya wuce dakin sa ganin yadda ya shigo ya sanya mahaifiyar sa ta bi bayan shi kujerar dake gefen katifar sa ta janyo ta zauna sannan tace Fawaz lafiya ka shigo ko sallama babu? Lafiya lau Umma to naji meke damun ka naga ka shigo rai a bace ko dai fada kukayi da wani? A'a Umma ai ni kin san bana fada da mutane kawai kai na ke ciwo to ka samu magani ka sha? A'a to ka hanzarta ka samu magani ka sha ga kuma ga abincin ka a kitchen to Umma zan kokarta ya fada yana lumshe idanu ita ma bata tsawwala ba ta fice.

Tun bayan kama Bilal da akayi mahaifiyar shi da kuma kanwar sa Ummi suka shiga tashin hankali dan ma Fawaz yana taimaka musu ta bangaren kayan abinci amma duk da haka farin ciki yayi kaura a gidan ita Umma kullun cikin tagumi da hawaye sai Ummi ce me tausarta gudun kada ciwon ta ya tashi. Fawaz ne ya shigo gidan su Bilal da sallama Ummi ce ke faman aiki a tsakar gidan cikin sakin fuska ta amsa gami da fadin sannu da zuwa Yaya ga gurin zama a'a ki barshi kawai saurin nake ina Umma? Ta je gidan Kawu Manu amma na san ta kusa dawowa ka dan jira ta a gaskiya sauri nake ga wadannan ya ciro kudi daga aljihun sa yace ga wannan idan ta dawo ki bata kudin da aka samu kenan amma insha Allah zan nemo sauran dai-dai lokacin Umma tayi sallama cikin ladabi Fawaz ya gaishe ta kuma ya shaida mata duk yadda suka yi Muhsin tayi matukar mamakin abinda ya Faru ganin irin abotar dake tsakanin Bilal da Muhsin amma da ta tuna yadda kudi ke sauya mutum sai ta daina mamkin lamari. Umma tace ka kwantar da hankalin yanzu daga gurin kawun ku nake a kan batun sai da gona ta a samu a fito da Bilal to Umma Allah ya bamu nasara Umma ta da Ameen daga bisani suka yi sallama.

Sajen ne ya shigo office din D.P.O bayan ya sara masa D.P.O yace ina jinka yallaboi akwai wanda ya zo yana son ganin ka yana son gani na? D.P.O ya maimaita da alamun mamaki a fuskar sa OK je ka shigo da shi bayan minti biyu sai ga su shigo bayan sun gaisa kuma ya bashi izinin zama sai ya tambaye shi abinda ke tafe dashi mutumin yace sunana Ayuba kuma nine P.A na senata Bello na zo kan batun case din Salim inaso a bani belin sa tunda ya fara magana D.P.O ke kallon har ya kammala sannan yace Malam Ayuba a gaskiya case din Salim babba ne kuma muna bincike a kan shi har yanzu sabida haka ba zamu baka belin sa ba kayi hakuri Ayuba P.A yayi murmushi yace yallaboi ba hana ku bincike zan yi ba amma ina ganin ai bai dace ace 'dan babban mutum kaman senata yana kwana a cikin wannan gurin mai cike da kazanta ba ga wannan sako daga sanata jakar kudi P.A ya ajiye a kan teburin dake gaban su, menene wannan kuma? Wannan yayi kadan ya sani na saki mutum biyu mutum biyu kuma waye cikon na biyun kuma yallaboi? D.P.O ya mike sannan yace kai ne cikon na biyun ka gaggauta kwashe wannan tarkacen ka bar office din nan kafin kai ma nasa a kulle mini kai, a gaskiya yallaboi kada kayi kuskuran shiga rigima da sanata sabida zaka yi da na sani domin zaka iya rasa aikin ka kuma kana da iyalai ko dan su... get out of my office!!! D.P.O ya fada yana nuna masa hanyar ficewa a sanyaye P.A ya fice.

Hajiya Bilkisu ce ta shigo dakin Alhaji ganin bai fito ba hakan yasa ta bi bayan shi "Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un" kalmar da ta biyo bayan sallamar hajiya kenan cikin hanzari hajiya ta karaso inda yake kwance tana girgiza shi amma idanun sa sai sama suke wayar sa ta laluba ya fara kiran Doctor Habib cikin tace Dan Allah Doctor kayi sauri Alhaji zai mutu ok ganinan zuwa yanzu Doctor ya bata amsa. Bayan kamar mimtina talatin da zuwan doctor ya kammala duk abun ya dace yayi ya kuma kara jaddada musu ka'idojin da zasu kiyaye kuma a samo masa duk abunda yace yana bukata dan gudun kada zuciyar Alhaji ta buga dan ciwon yayi tsanani sosai daga bisani yayi musu sallama.

Fawaz dai ta bangaren sa yana ta fafutukar ganin ya samu kudi amma abin ya fassara babu yadda zai yi dole ya koma wajan mahaifiyar Bilal ya sanar da ita, Umma tace ka kwantar da hankalin ka kawun ku ya sai da gona ta gobe insha Allah Ummi zata amso kudin sai ka kazo ka kar6a, ko ba komai zuciyar Fawaz ta dan yi sanyi da jin wannan maganar.


Ta bangaren D.P.O dake zaune a office din sa yana duba wani file wayar sa ne ta hau ruri ganin sunan CP ya bayyana a fuskar wayar ya sanya shi saurin dauka gami da kamewa yana fadin Morning Sir! Daga bangaren CP kuwa ya amsa da easy kana ya dora da ka kama dan senator Bello ko? Yes sir to ina umartan ka da sake shi but sir muna tuhumar shi kuma bamu kammala investigation ba, bana son jin wata magana kawai ka bi umarnin da na baka OK sir. Sam D.P.O baya jin dadin katsalandan da CP yake yi masa lokuta da dama akan aikin sa amma babu yadda ya iya dole ya bi umarnin sa aka sani Salim.

Firdausi ce ke kwance bisa makeken su tana ta faman chating da ganin ta kasan babu abinda ya dameta, Nusaiba kawar ce ta fado dakin kamar an jaho ta Firdausi tace haba Nusy ya zaki shigo daki KO sallama babu? Nusy ta dan harare ta tace Firdausi yaushe kika Musulunta har kika fara wa'azi bani da labari tayi maganar da alamar zolaya, karasowa Nusy tayi ta zauna bakin gadon tace yau kuma garan kika samu kodai nura ne? Firdausi tace haba ai ni yanzu na wuce ajin Nura bana harka da kanan yara, dai-dai lokacin Humaira kanwar Firdausi ta shigo dakin shiru sukayi gami da zuba mata na mujiya har ta kammala abinda take ta fice ko kallon su batayi ba, Nusy ta kalli Firdausi tace ita kuma wannan Ustaziyan me akayi mata take cika tana batsewa? Uhumm rabu da ita wai ita nan tana cikin damuwar rashin Moofy to ni meye ruwana suje can suyi ni gaba ta kai ni gobarar Titi haba Firdausi bai kamata kiyi haka ba Moofy kema yayar ki ce kuma hannu Firdausi tasa alamar ta saurara sannan tace Nusy kada ki bata mini rai kema kawai mu cigaba da abinda ke gaban mu hannu da kafada Nusy ta daga game da fadin any way yanzu tashi ki shirya mu shiga gari to ko ke fah amma kyazo ki kara bata mini rai ana zaune kalau.

Kamar yadda Umma ta sanar da Fawaz zata sai da gona haka kuwa akayi an samu kudi ki manin dubu dari takwas, Fawaz yayi matukar farin ciki, ficewa yayi daga gidan bai zame ko ina ba sai shagon abokin su Safwan inda yake aikin chajin waya. Bayan sun gaisa sai Fawaz yace da Safwan wata bukata ce ta kawo ni gurin ka ina fata zaka taimaka mini OK Allah ya bani iko yi maka , kan batun Bilal ne mako mai zuwa za'a shiga kotu kuma bamu da lawyer shine nake neman taimakon ka ko akwai wani lawyer da ka sani Safwan ya dan yi alamar tunani daga bisani yace eh to kasan neman lawyer zancen kudi ne akwai 'yan kudi a hannu za su kai kamar dubu dari takwas a razane Safwan ya dube shi ya kuma mai-maita dari takwas! Ya dan ja numfashi yace sannan yace ka tabbata suna tare da kai? Eh gasu Fawaz ya fiddo kudin daga aljihu OK tunda akwai kudi zan baka address din wani lawyer insha Allah zai taimaka maka Fawaz yayi godiya suka yi musabiha ya nufi office din lawyer, kamar Safwan jira yake Fawaz ya tafi a hanzar ce ya fiddo wayar sa ya latsa wata lamba ya kara a kunnu sannan yace Gwaska a bishi akwai kudi ku tabbatar ba kuyi kuskure ba daga bangaren Gwaska ya amsa da angama Oga. Ai kuwa Fawaz bai yi aune ba yaji an doka masa sanda a ka faduwa yayi kasa sumamme Gwaska da yaran sa suka debe kudin suka yi gaba suka barshi nan kwance.

Ta bangaren Bilal kuwa 'yan sanda sai kara jibgar sa suke yi duk da sun turo lamarin wa kotu amma bata sauya zani ba kamar yadda ya fada tun farko bai san wanda ya sace Moofy ba hakan yake ta mai-maitawa, kullum cikin kuka yake amma bana ukubar 'yan sanda ba na bacewar abar kaunar sa ga halin kunci da damuwwar da mahaifyar sa ke ciki yasan tabbas suna cikin matsala.

Alhaji ya farfado amma da sunan Mufeedat ya farka duk da jarumta da yake so ya nuna amma hakan ya fassakara sabodi Mufeedat itace 'yar da yafi kauna fiye da duk abinda ya mallaka a duniya. Kuka sosai hajiya ta shiga rerawa ganin yadda mujinta ya koma tana fadin wlh Bilal ka cuce mu Allah ka saka mana zaluncin Humaira ce ta karaso ta hau rarrashin ta tana fadin ki daina kuka momy insha Allah zamu ga Aunty Moofy kuma kin san wannan kukan da kike zai iya karawa Daddy radadin ciwon shi Humaira ki barni nayi kukan ko na samu sauki a zuciyata .

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 19, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ALLU TA TONO GARMAWhere stories live. Discover now