SUMAYYA
Ban taɓa zuwa asibiti ba tunda nake a rayuwata ba, mu 'yan gargajiya ne, sai dai karon farko dana je asibiti shi ne abu na biyu daya ƙara ruguza rayuwata. Na shiga ɗimuwa, na yi nadamar da ban taɓa yin irinta a rayuwata ba, wani lokacin idan na kalli kaina sai naga kamar ni kaɗaice Allah ya jarabta da mummunar ƙaddara...