Shin wai ni yau bari na tambayeki. Shin wai Hameedu ƙafar Habu Maharbi ya cire ko kuwa ta Bawa? Shin wai Hameedu dukiyar Ladi ya cinye ko kuwa ta Bawa? Shin shi Bawan me yake zame miki ne banda miji? Shin akwai wani jini guda ko da na halittar kaza ne da kika dasa a tsakaninki da Bawan? Kai! Ko kuwa akwai halittar mutum irin wacce uwar Halliru ta bashi, shin ko kuwa banda abinda na sani akwai wani abu tsakaninki da Hameedun..!?" Sai anan ta cira idanuwanta sama ta dube shi a yayin da wata kwalla guda ta sauko daga kurmin idonta...
4 parts