Khaleefa bazan b'oye maka ba, kamar yadda al'adun mu suka banbanta, haka tsarin tafiyar da rayuwar muma ya banbanta, mahaifina ya kasance mutum mai tsanani da magana d'aya, shiyasa bana ja da dashi akan komai na rayuwa don wahala zanyi a banza kuma bazai fasa abinda yayi niyyah ba, a dunk'ule Ina nufin ko Zan had'iyi zuciya na mutu a gidan mu ba za'a tab'a bari na auri mutum mara asali irin kaba.