Part 1

36 2 0
                                    

*SAFNAH*

WRITING

BY

*UMMU FU'AD* (HUMKAM INCENSE)*

*SHIN KINADA LBRN WANNAN SHAHARARRIYAR MAI GYARAN JIKI DA TURARUKA MASU K'AMSHI DA DAUKAR HANKALI HMM YAR UWA YI MAZA KI GARZAYO GURIN HUMKAM INCENSE DAN SAMUN RABONKI*
"Na kasance yarinya Mai tsantsani rayuwa,ina da ilimin addini daidai gwargwado,Dan a gsky ina d'aya daga cikin mahaddata alqur'ani
Da akeji dasu agarin kaduna,mahaifina ba malami bane amma yana da riko da addini sosai,sannan mutum ne Mai so yaga yaransa sunyi ilimin addini Dana zamani,Mahaifina yanada tsananin gaske baya tab'a sake mana,in takaice muku da zaran ance Abban mu yadawo gida to fa ko tari Mai karfi bamu isa muyi ba,bare har yakaimu ga hayaniya,hakanne yasa muke tsananin tsoron sa,

"Sunan mahaifina Alh Saminu rigachikun! Matan sa uku na farkon Fa'iza,,tanada yara shida,Abdullahi,Suraj,Safiya,SulaimanSalis,Suhailat,sunan mahaifiya ta Zainab,auren soyayya sukayi da mahaifina har Allah ya azurta su day yara hudu,Shu'aibu,Saini Safnah,Salaha,Shuraihu,sai Dan autan sulaimu, sai ta ukun itace amarya mai suna Bilkisu ita kuma haihuwar ta hudu Sagir sadik Salman Salamatu,wadannan sune yaran da Allah ya azurta mahaifina dasu.

Safiya itace kan mu yazo d'aya duk da cewa na girme ta,Amma ajin mu d'aya saidai nafita kokari duk gidan mu,hakan yasa mahaifina ke Bala'in Sona,kuma yana nunamin,gurin ummin mu kuwa kwatakwata Bata nunamin kulawa,k'auna da kuma jink'ai,tana matukar tsauraramin wajan karatun alqur'ani hakan yasa nakejin sam-sam bata sona, banida wani lokacin wasa saina karatu inada karamin shekaru,a wannan lokacin da aka kaini wata islamiya,gwaji na farko da sukamin aji uku aka kaini kuma shine ajin manya 'yan mata jiga-jigai,ni kuwa a lokacin banfi shekaru goma a duniya ba, idan malamin mu yazo yana koyamin karatu nan da nan sai suga na iya,

hmmmm hakan yasa suke kaunata basu san cewa bak'ar wahala nake sha gurin ummin mu ba,muddin ta koyamin karatu nazo ban iyaba takan min bulala biyar a kowani gyara d'aya,takan Tara yaran gidan ta koyar damu dukan mu ahankali iyayen su suka hana su xuwa,da dare ina kallon kowani yaro na wasa yana kallo Amma banda ni Safnah inacan tana koyamin karatu,haka zalika da asuba kowa zai koma barci banda yan dakin mu,nayita ji a zuciya ta inama ace ba itace mahaifiya ta ba danaji dadina,inason naga cewa ina kallon fina-finai Amma ban isaba sbd gidan mu Babu TV wannan dokar Abbane,

A lokacin da na hada izuhu uku a makarantar mu,a gida inada bakwai,a boko ma ina kokari sbd bana wuce position 4 cikin 50 amma bantaba jin ummina tace Safnah kinyi kokari,ko kuma tace ina son yadda kike dagewa a makaranta,hmmm bansamu hakan ba,har kullum idan na kawo mata result dina saidai tace ke ko kunya ma bakyaji bakida kokari dalla dauka kikai daki,haka zan sa hannu na dauka jiki a sanyaye nakaishi daki,najira dawowar Abban mu,shikam har kyauta yakemin yace shiyasa nake sonki kinfi kowa kokari harda yayyinki,hakan yana sa naji dadi sosai,

Ku cigaba da bina danjin lbrn Rayuwata....

*shin kinada lbrn shahararren turaren Nan Mai suna Al'ajab wannan turaren yanada magani sosai kinsan cewa Yana ciko da HQ Yana matsi sosai Babu ruwanki da Sanya wani Abu Dan ya matse Miki HQ Al'ajab ya wadatar dake Yana maganin sanyi yanasa dandano Yana sirrika hajiya Al'ajab nasa namiji yaji wani dadi da gamsuws tattare dake 08132506044*

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 23, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

LABARIN SAFNAHWhere stories live. Discover now