GIDADO BASHEGE BANE 1

837 18 3
                                    

*GID'AD'O BA SHEGE*
*BANE*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
NA
Zahra Muhammad Mahmud surbajo .
.
Space 1
.
*wannan littafin kirkurars nayi,banyishi dan wani ko wataba,so in wani abu yayi kama da rayuwarka arashine,a kiyaye juyamin shi ta kowacce siga


.
Ɗakin tarone me kyan gaske,wanda ke dauke da kujeru na alfarma.zagaye da wani tebur.

Mutanene kimanin mutum hamsin zaune akan kujerun kowa rai abace,yayinda wasu yanmata su uku ke tsugune agaban mutanen,daya cikinsu dauke da wani jariri se kuka yake tsalawa.

"Fatima Abubakar Radda,Hauwa'u Abubakar Imam,Amina,acikinku wlh idan baku fada mana dan waye wannan jaririnba,se na koreku dukanku a makarantar nan,taya zaa haifi yaro acikinku amman akasa gane wacce ta haifeshin"cewar chancellor na makarantar nasarawa state university wacce akafi sani da suna Nsuk.

Gaba ɗaya hankalin yanmatan inyayi dubu ya tashi,sabida dukansu suna level four hundred ne kuma final exam suke zanawa.

"Sir wlh ni ba dana bane,wlh banida wata alaka dashi,Fatima ce ta tsintoshi ta kawo mana shi dakinmu jiya da daddare,bayan haka ni wlh bansan komai ba game da yaron"cewar hauwau Abubakar imam tana share hawaye.

Amina ce ta tsananta kukanta,harda majina,inda tafara mgn.

"Taya mu da muke yanmata zaace wai mune kuma muka haifi yaro,nima wlh ba dana bane,sam banida alaka dashi,sede atuhumi ita fatiman data kawo yaron,danni wlh a idona ma gani nake tana kama da yaron"ta karasa maganar cikin kuka.

Allah sarki fatima baiwar Allah ware ido kawai takeyi,sabida ita tun farkonta bata iya magana me tsayiba hasalima wuya take bata,shiyasa su hauwau suka fita baki,

Tsawa vice chancellor ya yimata gami da cewa.

"zaki mana bayanin inda kika samo yaron ko bazakiyi ba?"

A daburce tace.

"Sir wlh ba ɗana bane,wlh banida alaka dashi,kwatakwata nima tsintarshi nayi jiya na fito fitsari zan koma daki naganshi cikin kwali ruwa na dukanshi yana kuka,shine na ɗaukeshi nakaishi ɗakinmu,amman wlh ba ɗana bane"ta karasa maganar tana kuka gamida jijjiga yaron dake ta faman kuka.

Shuru gurin yayi,kowa na nazari,inda su Amina da hauwau suka tubure sufa ba ɗansu bane,inda amina kai tsaye ma ta alakanta yaron da fatima.

Fatima se kuka takeyi,Tana rantsuwa akan tsintar yaron tayi amman sam anki amincewa da ita,sabida shaidar da aminanta suka bada kamar haka.

" sir watanni shida dasuka wuce fatima Abubakar Radda ta taba cemin watanninta uku rabonta da ganin aladarta,wanda har na bata shawarar taje taga likita,bayan haka bata cemin tasamu saukiba ko akasin hakan"cewar hauwau tana kallon fatiman.

"ke fatima anyi haka ko ba ayi ba?"cewar chancellor .

"eh anyi haka,sede na bari ne akayi hutu sannan naje asibiti dana koma gida aka bani magani kuma nasamu daidaituwar abun"cewar fatima tana kuka.

"Nima ta fadamin hakan,bayan haka kuma tazo tana fama da yawan ciwon mara,wanda lokacin,har cewa takeyi tanajin motsi acikinta,sannan lokacin tana yawan yin bacci dan so tari ko aji bata iya zuwa"cewar Amina tana kallon fatiman.

"Fatima anyi haka ko baayi ba?"inji chancellor.

Cikin matsanancin kuka tace.

"Duka anyi,sede motsi da nakeji a cikina danaje asibiti cewa akayi infection ne ke haddasa hakan,yawan bacci kuma lokacin banida lfy ne,ciwon mara ma danakeyi yanada alaka da infection din,ku yard dani wlh ni ba dana bane"ta rushe da kuka.

Has llegado al final de las partes publicadas.

⏰ Última actualización: Jan 31, 2021 ⏰

¡Añade esta historia a tu biblioteca para recibir notificaciones sobre nuevas partes!

GIDADO BA SHEGE BANE 1Donde viven las historias. Descúbrelo ahora