4

2.5K 78 10
                                    

No. 4

WAIWAYE ADON TAFIYA.

          Malam Hashim musa shine asalin mai gidan. Babban malami mai tarin ilimi daya taka rawar gani a duniyar musulunci. Yasha gwagwarmaya ƙwarai da gaske na ganin ilimi ya yaɗu da faɗaɗa cikin al'ummarmu ta nagartattun hanyoyi.
       Kasancewar yayi gwagwarmayar rayuwarsa ta neman ilimi lokacin ƙuruciya a garin Jibiya ta jihar katsina sai ake kiransa da suna ɗan jibiya.
        Matan Malam Hashim ɗan Jibiya biyu kacal a duniya. Zainabu (Hajjo) sai Zulaiha.
     Ƴaƴansa Huɗu duk maza, kuma dukansu Hajjo ce ta haifesu, dan har Zulaiha ta koma ga ALLAH bata taɓa ko ɓatan wataba.
        Sooraj mahaifin su Nu'aymah da ake kira da Baba Malam shine babban ɗansa. Sai Rudwan mahifin Abdallah wanda shima yanada iliminsa sosai, amma shi yana kasuwanci ne, duk da suma su Baba malam suna kasuwancin. Sai Mustapha Mahaifin su Adawiya, shima dai malamine dan tare da Baba Malam suketa ƙoƙarin cigaba da ginin da mahaifinsu ya bari na yaɗa ilimi. Sai auta Musbahu, shine mahaifin su Yusrah, shima dai malamine, yanama addini hidima yana kuma business.
         Kamar yanda kukaji a farko gidansu Nu'aymah gidan manyan malamaine sananne, sannan kuma ƴan kasuwane na gaske, dan har sunada kamfanin dake sarrafa Mangyaɗa da kuma sabulu, suna kuma sufurin kayan masarufi sosai ta hanyoyi daban-daban cikin farashi mai sauƙi duk daga kamfaninsu mai suna ƊAN JIBIYA FAMILY.
          Kamfaninsu sanannen kamfanine dake da haja a lungu da saƙo na ƙasarnan sabida sauƙin kayansu. Sannan kuma sanannun malamaine da duniyar musulinci ke alfahari dasu a lungu da saƙo na ƙasarnan. Sunada manyan makarantun da ake koya ilimin addini zallah a cikin kano dama wasu jihohi maƙwafta, suna kuma da gidan marayu nasu na kansu da suka assasa domin ladan ya ringa isa zuwa ga mahaifinsu da ALLAH yayma rasuwa kusan shekaru ashirin da suka shuɗe.
     Family ne da alkairansu a bayyane yake wa duniya duk da suna ƙoƙarin ɓoye kansu dan kar asan sune keyi. To amma masu iya magana kance alkairi dankone baya faɗuwa ƙasa banza.

           Sooraj (Baba Malam) shine ya zame musu tamkar mahaifi bayan rasuwar Malam Hashim, ya kama ƴan uwansa ya dunƙule kansu waje ɗaya babu mai jin kansu sai ALLAH. Suna ƙaunar junansu matuƙa da mutunta juna. Komai nasu sai sun nema shawararsa kamar yanda shima idan zaiyi wani abu sai ya tarasu ya nema tasu duk da suna a ƙasa dashi.
       Tun mahaifinsu nada rai suka gina wannan gida daya kasance gari guda, dan malam Hashim ya mallaki filin ne tun anguwar babu wasu gine-gine kirki, da farkoma noma yakeyi a filin, sai da yaransa suka fara tasawa ya zagayesa yay massallaci da islamiyya, ya kumayi ƙaramin gida a ciki yana zaune da iyalansa. Bayan rasuwarsa arziƙin kasuwancinsu ya ƙara haɓaka sai suka gyarashi aka faɗaɗa massallacin da Islamiyyar, suka kuma ginama kowa sashensa inda zai zauna da iyalansa. A hankali harkoki na ƙara haɓaka musu suna sake gyara gidan har ALLAH ya kaisu ga wannan matsayin suka kasance cikin tsakkiyar birnin kano.

     Sooraj (Baba Malam) ya jima baiyi aure ba, dan sai da takai har Hajjo na nuna masa ɓacin ranta akan hakan, sannan yay auren zuminci da wata ƴar ƙanwarta mai suna Salamatu. Rana ɗaya aka ɗaura musu aure su Uku, shi da ƙannensa biyu. Mustapha (Abban Adawiya) da Rudwan (Abban Abdallah) Bayan aurensa da Salamatu ta haifa masa yara uku duk maza. Yayinda shima Rudwan matarsa keda yara uku a lokacin, Maza biyu mace ɗaya. Abdallah shine babba, sai Omar, sai Aysha. Amma Mustapha matarsa bata haihuba.
     Shekarar da Musbahu zaiyi aure a shekarar ne Matar Baba malam Salamatu da ƴaƴanta uku, sai matar Mustapha sukai haɗari a hanyarsu ta zuwa Jigawa suka rasu. Lokacin shi Rudwan matarsa na fama da laulayin ciki bata bisuba, sai yaran kawai. Dukansu ALLAH yay musu rasuwa a motar, Abdallah ne kawai keda sauran kwana a duniya. Shima dai ya bugu, dan yasha doguwar jinya kamar bazai rayuwaba ALLAH dai ya raya kayansa bayan yasha wahala. Gida ya koma babu yara ko ɗaya sai Abdallah kawai, sai kuma cikin jikin Momynsa.
      Ba ƙaramin tashin hankali suka shigaba a wannan lokacin, dan Hajjo yitai kamar ta zare dan kiɗima, gawarwakin jikokinta biyar da surukanta biyu da driver aka sallata a rana ɗaya kolaci ɗaya, haka aka jera kabirburansu abin tashin hankali😭. (Ya rabbi ka gafartama iyayenmu damu baki ɗaya😭🙏🏻).
     
       Bayan rasuwar matan su Baba malam basu sake maganar aureba har Momyn Abdallah ta haifi cikinta namiji, wanda aka maidama suna Omar, bayan kamar wata biyu da haihuwarta amaryar Musbahu ma ta haihu mace, ita kuma taci suna Jameela.
          Hajjo nasan su Baba malam su ƙara aure, amma kuma tausayinsu yasa ta kasa takura musu, sai dai ta cigaba da binsu da addur fatan samun mata nagari da zasu maye musu gurbin matansu. Ansha kawo musu matan aure har gida, musamman kasancewarsu malamai kuma masu kuɗi Alhmdllh. Sai dai basu taɓa amsaba, dan basu farfaɗo daga magagin rashin family ɗinsu ba.
       Bayan shekaru biyu da rasa iyalansu ƙwatsam ALLAH ya haɗa Baba malam da Firdausi (Umm) a wajen wani walimar yaye ɗaliban makarantar BUK. Tunda ya ƙyalla ido akanta bai ɗaukeba, duk inda ta shiga ta fita idanunsa a kanta, gashi babu damar mata magana saboda sune manyan baƙi a wajen, hasalima shine yay lecture wa ɗaliban mai ratsa jiki. Inda itama anan Umm ta mutu ason wanda tasan ko kallo batama ishesaba, amma kasancewarta mace miskila ta gaske, kuma mara son yawan magana sai ko a fuska bata nunaba.
     Kamar yanda Firdausi (Umm) ta mutu akan son Malam Sooraj Hashim haka babbar ƙawarta, aminiyarta Fauza (Addah) itama ta mutu akansa lokaci guda, sai dai itama ɗin dai bakinta bai furtaba, sai dai kasancewarta mace mai faranfaran da barkwanci dason jama'a sai taita yabashi har Firdausi ta gaji tai mata ƙorafin ta isheta. Dariya tayi a wancan lokacin, dan itace kaɗai ta iya zama da Umm kasancewarta mace mai bahagon hali, ga rashin son wasa, dan sam Umm bata da fara'a, bakuma tason yawan wasa kamar ƙawarta Fauza (Addah).
          Ahaka taro ya tashi lafiya Fauza da Firdausi na begen abinda basa tunanin zasu samu a zukatansu, sai dai kuma abinda basu saniba shine Malam Sooraj tunkam yabar makarantar yasa ake bibiyar masa Umm, har aka tashi kowa ya kama gabansa ana binsu a baya har gida anguwarsu. Mai bin nasu yana ganin inda suka shiga ya koma da baya yaje ya sanarma Malam Sooraj Hashim. Baba malam yaji daɗi matuƙa, bai kumayi ƙasa a gwiwa ba ya sake sakawa aka bincika masa mahaifin Firdausi (Umm).

SARAN ƁOYEWhere stories live. Discover now