chapter 15

20 2 2
                                    

      Assalamu alaikum warahamatullahi wabarakatuhu. Godiya a gareku masoyaana masu karanta littafina me suna nabila, nagode Allah yabar zumunci 🙏.

      Zakuga na Jima banyi update ba, kunsan idan akace mutum dan koyone sai a hankali😊.

     In Sha Allah yanzu na dawo zaku rinka ganin update akai akai in Sha Allah. Allah ya bani ikon rubuta abunda zae anfanemu baki daya.

Nagode😊.

------------------------------------------------------

        Waiwaye....

  Hmmm kausar kenan, ke aganin ki a makarantar nan akwai wata mace da zan iya soyayya da ita?

   Ah ah to ai shi so tsuntsun ne mukasani ko ya tashi daga kan waccan din ya fada kan wata a makaranta 😄

    Kema kinsan irin son danake mata banajin zan iya kula wata 'ya mace Koda bata a duniya.

   A a dai banason cika baki, irinkune ku dinga ma yaran mutane dadin bakin bazakuyi masu kishiya ba sai sun sakankance kawai ku tarwatsa masu jindadi

   Nifa bari na Fadi maka gaskiya, wallahi duk namijin da yazo gurina naji ya fara irin wannan zancen tini zan dakatar dashi saboda baesan gaibu ba.

     😄😄😄😄 Ai ke kausar ta daban ce, tunda nake a rayuwa bantaba ganin mutum straight forward irinkiba, rayuwarki tana birgeni, Allah dae ya hadaki da miji irinki ba irin mazan yanzuba dan wallahi mazan yanzu sae a hankali.

       Amn thumma amn dai.

   Da haka suka koma firar karatu saboda kusan koda yaushe aikinsu kenan.

    Abdul mutum ne me nacin karatu duk inda kaganshi to wani abun yake karuwa dashi, bae yarda ya zauna haka kawai aita hirar duniya ko gulmar ya'yan mutaneba.

     Yakance bashida karfin daukar hakin wani a wuyanshi.

    Wannan ne dalilin dayasa bashida wasu abokai a school sai wadanda za'a hadu a gaisa.

A hakane Allah ya hadasu da khausar, yarinya meson karatu, bata da girman Kai duk abunda ya shige mata duhu sai tayi tambaya kuma indai tasan kafita fahimtar abu to zata zo ka koyamata duk kankantarka.

     Wannan shine abundake burge Abdul game da khausar, ga sanin darajar dan Adam.

     Mutane da yawa a makarantar kallon masoya ake yi masu Amma asali ba wata soyayya sabone kawai da kuma hali da yazo daya.

    Ba wani sirri da suke boye ma juna, sukan nema shawarar juna a lokacin da bukatar hakan ta taso.

    Sai dai abu daya cikinsu ba wanda ya taba taka kafa yaje gidan dan uwansa duk da suna gari daya.

     Ana hakane har Allah yasa suka gama karatu gashi lokacin waya sai wane da wane, ita dai kausar gidansu akwai amma Abdul babu kuma kwata kwata dabarar ansar number bezo mashiba.

    Sun Sha kuka kamar an rabu kenan da hakane sukayi musanyar address da tunanin zasu rinka ziyartar juna lokaci zuwa lokaci.

    Jin shiru Abdul bezoba kuma tana ta mafarkin shi a yan kwanakin nan yasa take ta roki kishiyar mahaifiyarta alfarma akan ta roka mata malam wato mahaifinta akan zataje gidansu Abdul taji ko lafiya.

  Mahaifiyar khausar Allah yayi mata rasuwa tun tanada shekaru bakwai a duniya.

   Zamu iya cewa bata san dadin mahaifiya ba amma kuma mama kishiyar mahaifiyarta ta riketa kamar Yar da ta haifa.

   Duk da bata taba haihuwa ba hakan besa ta wulakanta khausar ba.

  Tana yimata duk wani abun da uwa ke yima yarta.

   Dake duk sunsan labarin Abdul din da irin rawar da ya taka a karatun khausar din sai ta amince.

   Washer gari kuwa tazo mata da daddadan labari na yardar mahaifinta akan taje taji ko lafiya harda yan kudin tsaraba.

   Da haka ta yanke shawara washegari da safe zata fita saboda tasan zata dan wahala kafin ta gano gidan.

   Washer gari tagama aikinta tsab ta shirya ta fita cike da dokin ganin Abdul duk da wani sashi na zuciyarta na Fadi mata ba lafiya yake ba.

  

      taku
Safara'u sa'ad

Kar kumanta comments, vote, like and follow me.

    Thanks

NABILAWhere stories live. Discover now