1-End

16 2 2
                                    

SMARH❣️💥💥💥💥*
                     ~*(Neeynarh Love🌸)*~

_Daga Alk'alamin✍🏾_
~*N.M.S Love*~

*Alhamdulillahi! Alhamdulillahi!! Alhamdulillahi!!! Ya ubangiji da kai kad'ai na dogara kuma kai kad'ai ne nasan kake taimakona a dukkan littattafan da nake yi ya rahim ka dafamin kasa wannan littafin ya d'aukaka gurin jama'a, ya rahma ya rahim ya salam ya zuljalalu wal ikram🤲🏽🤲🏽🤲🏽Alhamdulillahi for everthing😭❤️*

_gareku masoyana wannan shine sabon littafina da fatan zai samu k'arb'uwa gurinku😭👏🏽 ina k'ara miko sakon gaisuwata gareku nagode sosai love you all❤️_

*Alk'alami yafi takobi🤺*

*Shafi na 1*

_Gajeran Labari_

Zaune take a kan kujera tana rik'e da wayarta tana typing d'in littafinta mai suna SAQAR SO duk da cewa bashi kad'ai ne littafinta na farko ba tayi su da dama a kalla zasu kai bakwai kuma a yanzun ma typing biyi take had'awa bayan saqar so tana rubuta wani littafi mai suna HAJNA alhamdulillahi duka litattafan nan da take yi sun samu k'arb'uwa gurin jama'a, domin kuwa duk wanda tayi posting a cikinsu tana samun comments sosai, Nasmarh kenan Kyakkyawa ce ajin farko sai ba fara bace irin bak'ak'en nan ne da ake kiransu da black beauty, babu ruwanta domin kwata-kwata a rayuwarta bata da girman kai amman kuma tana girmama kanta da kuma jama'a, bata cikin jerin marubutan da zaka gani suna wulak'anta mutane sam bata da wulak'anci.

Da gudu wata k'aninta Abdallah ya shigo ya fad'a kanta har sai da wayarta ta kusan fad'uwa, ta d'aka masa duka a baya sannan ta ce "baka da hankali ne da zaka shigo ta fad'o min a jiki, ko sallama baka yi ba".

Zama yayi a kusa da ita ya ji zafin dukan da tayi mas a baya dan haka sai da ya bari ta sakankance tana typing har ta kusan gamawa ta fusge wayar ya fita da gudu, ta bi sa ita ma da ya ga tana binsa kuma ya san idan ta kama shi ba zata yi masa ta dad'i ba ya saki wayar a kasa ta fad'i ya shige d'akinsa tare da kullo k'ofar ya saka mata key.

Ita kuwa Nasmarh takaici ya kamata domin da ta duba sai ta ga wayar bata fashe ba amman sakin ta da yayi a k'asa ya saka ta mutu, bak'in ciki ya kamata, har hawaye na kok'arin zuba daga idonta "yanzu shikenan sai k'ara sabon typing" tayi maganar cikin yanayin muryar kuka, wayar ta d'auka ta koma d'akinta duk da takaici ya gama cikata haka ta kunna wayar ta sake yin sabon typing amman wannan karan bata yi shi da yawa irin na d'azu ba, kuma ta k'udurce a zuciyarta idan ta kama Abdallah sai na lahira ya fisa jin dad'i (ni kuwa nace Love a dai k'ara hak'uri🤣).

Posting d'in shafin da tayi ta shiga yi a wattpad,whatsapp,telegram, instagram, facebook dama sauran guraren da ake yin posting d'in littafi ko minti goma bata yi da yin posting ba ta fara samun comments ta kowane gurin har da masu cewa a cigaba dan Allah, da masu cewa yau bata yi typing da yawa ba (ni kuwa nace Abdallah yayi aika-aika🤣), anan ta shiga yi musu reply a kan comments d'in ta d'auki kusan minti talatin tana abu guda, kiran sallar da taji ne na Sallar la'asar yasa ta tashi ta shiga toilet ta d'oro alwala ta dawo ta shimfid'a dadduma ta bi jam'i tunda daga gidansu ana iya jiyo kiran sallah sosai kamar a gidansu masallacin yake.

Tana idarwa ta shiga karanta Alkur'ani mai girma sai da tayi kusan minti talatin tana karatun sannan ta mayar da kur'anin cikin lokar da take ajiye shi ta koma kan gado tana cigaba da danna wayarta tana chatting da friends d'inta na makaranta.

A haka bacci mai nauyi yayi awan gaba da ita, sai bayan magriba ta farka alwala ta shiga toilet tayi ta dawo ta gabatar da sallar magriba, tana idarwa ta nufi Falo a zaune ta tarar da Mama a falo tana kallon wani film d'in hausa episode mai suna SHARI'AR SO, Nasmarh ta k'arasa tayi mata sannu da hutawa sannan ta zauna ita ma tana kallon, suna cikin kallon sai ga Abdallah nan ya fito falon ba kula da ita ba dan haka ta nufeshi da sauri ta kamashi tana cewa........................😂

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 28, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

NASMARH Where stories live. Discover now