Page1-2

575 31 3
                                    

💞💞💞LAILAH💞💞💞

STORY AND WRITTEN BY

AISHA MA'ARUF
GIMBIYA AYSHU💞💞💞

SHORT STORY

WHATPAD Aishamaaruf1

ELEGANT ONLINE WRITERS

Page1-2

Bismillahir Rahmanin Rahim

"Lailah na saman kujera tana kallon wani series na Indian mai Suna (kaddaran Rayuwa)",sai kanwar ta Husna ta shigo tace Aunty Lailah,na'am mai yafaru,Husna tace yaya Abba na kiran ki,kice mishi bana nan, da toh Aunty Husna ta amsa fita tace batanan,yaya Abba yace to in ta dawo kice mata nazo,da toh yaya ta amsa sannan ta koma ciki tagaya ma Antyn ta abin da yace"tsaki Lailah ta ja sannan ta dauke kai",Mama da ta fitowan ta daga kitchen kenan ta hauta da fadan akan me zatace batanan sai tafara mata fada,daga baya ta sassauto tace Lailah!,"na'am mama",mai yasa kike ma Abba irin Wannan abin,bai dace ba samsam,wulakanci bai da kyau wallahi,yanzu inya dawo Dan Allah ki amsa mishi saboda naga duk san da yazo sai kin bada uzuri,haba Lailah ki gyara dan Allah,mama wlh bana son yaya Abba mama........ ta karasa maganar ta tana fashewa da matsanancin kuka ta shige daki tana kuka sossai,kusan minti sha biyar ta dauka tana kuka kafun barci yayi nasaran dauke ta............

Mama kuma na daki tana tunanin yanda zata bullo ma alamarin nan da ya shamata kai, ta kamo Wannan ta daura,ta kamo wanchan ta kwance tananan zaune ta kuma jin sallaman Abba,kiran Husna tayi tace taje ta duba Wanda ke sallama,da toh Husna ta amsa sannan ta juya ta fice daga dakin,bude kofan tayi taga yaya Abba ne,gaida shi tayi sannan tace ya shigo,da a'a ya amsa mata sannan yace kawai ta kira mai Lailah,da toh kawai ta amsa mai ta juya,dakin Aunty lailah ta nufa dan bata parlor,knocking tayi bayan an bata izinin shiga ta bude kofan tare da yin sallama,gai da yayar ta ta tayi kafin ta dora da fadin Anty Lailah yaya Abba na kiranki,shiru Lailah tayi kaman bata ji ta bahhh!............. Kara maimaita mata abin da tace tayi,"Dan Allah wuce ki bani wuri naji,ta fada tare da jan wani dogon tsaki",juyawa Husna tayi ta fice daga dakin tana murguda Baki,fita tayi daga palor ta same shi zaune kan daya gaga cikin kujerun dake compound din,bayan ta karaso kusa da shi tace"tana zuwa yaya",murmushin daya bayyana kyawawan hakoran shi yayi yace"to kanwata nagode sossai,ya fada yana mika mata kudin dake hannun shi" murmushi kawai husna tayi tace ka barshi yaya nagode,"hada rai Abba yayi yace common amsa jare",hannu biyu Husna tasa ta amsa tana mai godiya,"sai da Lailah tagama jan aji da bata lokaci kafin ta fito",tana fitowa ta mai sallama sannan ta gaishe shi a dakile,amsa mata yayi da kulawa,daga haka batace komai ba taja bakinta tayi shuru ta daure fuska "uwa uba taga mutuwan ta",yace "Lailah mai laifina dan nace ina sonki,karki manta masoyi yafi makiyi, ki tausaya mun Lailah,zuciyata na azabtuwa da soyayyarki,dan Allah ki soni ko kadan ne my princess,"dago kanta tayi ta kalle shi ta dauke kai bata ce komai ba",yace talk to me pls my princess,I don't like your silent,"dagowa tayi tace mai zance ma dan Allah,nace maka bana sanka,ni ba soyayya bane a gabana,karatu nake yanzu ka fahimce ni dan Allah,ta karasa maganar ta tana fashewa da matsanancin kuka harda majina tana shasheka", zuba mata ido yayi yana kallon ta,"a zuciyar ta ko cewa tayi kayi hakuri yaya Abba,babu macen da zata ganka ta kika kana da kyau,kudi,ga hankali,ga natsuwa,uwa uba ilimin Addini dana boko,amma kashhhhh.......... bazan iya sonka ba saboda zuciyata ta dade da bari na,tana tare da wani,shi kadai ne a ciki,bazan iya San wanin sa ba,kayi hakuri yayana.................." maganar shine ya dawo da ita hanyacin ta,"yace dan Allah kiyi hakuri ki daina kukan nan pls,kayi hakuri zan jiraki har ki kammala karatun ki in dai Wannan zai saki farin ciki toh ni zan miki,farin cikin ki shine nawa, is that Okh for u,ya karasa maganar shi da murmushi a fuskan shi,"dago kanta tayi tana murmushi tana hawaye ta kada mishi kai alamun ta yarda ta amince",to share hawayan ki ki bar kukan kinji my princess,"hannu ta share hawayen idan ta tassss!",janta da hira ya fara yi tun tana shuru tana nokewa har ta fara bashi amsa,hira ce ta barke a tsakanin su,suna cikin hiran sukaji kiran sallan magrib,kallan cute face din ta yayi yace"sai gobe my princess",Allah ya tashemu,"da Amen ya amsa ya wuce", ita kuma ta shige ciki taje tayi alwala tayi sallah,bayan ta idar tayi azkar na yamma bayan ta gama tafito parlor inda ta samu daddy ta ya dawo,ta duka har kasa ta gaishe shi ya amsa da fara'a sossai yace yar daddy ya kike,ya karatu,tace lfy lau daddy ya aiki daddy,yace Ahamdulillah daughter,hira suka fara sai ga mama da Husna sun sauko,gaishe da daddy Husna tayi,daddy ya amsa tare da cewa autana ykk,ya karatu,tace lfy lau daddy ya aiki daddy,Alhamdulillah autana mama kuma ta mai sannu da dawowa,daddy ya amsa tare davcewa ya gida da yara mama tace lfy lau Alhaji ya aiki Daddy yace Alhamdulillah maman yara murmushi kawai mama tayi daga haka sukafara hira har akayi kiran sallan isha daddy yaje masallaci mama kuma taja yaran ta sukaje sukayi nasu bayan duk sun idar suka sauko jiran dawowan daddy a dining area,after 5min daddy ya shigo ya samesu a dining area yaja kujera ya zauna sai Lailah ta tashi tayi serving kowa bayan sun kammala duk suka koma parlor Suna kallo daddy kuma na aiki a laptop har 10 kafun duk su ka tashi dan su je su kwanta, mama taje dakinta ta shirya kafun taje turaka,a bangaren Lailah kuma bayan tayi wanka tayi alwala ta kwanta ta fara aikin ta na kullun wato tunani, ba ita ta samu yin barci bahh sai 1:00am barci ya dauketa Asuba tagari.......

Kubiyoni dan karanta cigaban labarin.

Comment and share.

💝💝💝.

💞💞💞LAILAH💞💞💞(COMPLETE) Where stories live. Discover now