PAGE 63-64

80 16 0
                                    

💞💞💞LAILAH💞💞💞

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU 💞💞💞


ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚


WANNAN PAGE DIN   SADAUKARWA NE GA MASOYA NA ABIN ALFAHARI NA💞💞💞


PAGE 63-64


__________________________Washe gari sai da Lailah ta makara,ba ita ta tashi ba sai karfe 8 na tsafe,tashi tayi da Addu'a a bakin ta,hannu daya tasa ta rike kan ta saboda wani irin sarawa daya Yi,hawaye Mai zafi ne ya tsauko daga idan ta,hasken ranar data gani ta windan tane yasa ta tsaurin kallon agogon dakin ta,zaro Ido tayi tace "innalilahi wa Inna ilaihi rajiunnn" mikewa tayi tsaye zata nufi bayi,wani irin jiri ne ya kwashe ta,tsaurin rike bango tayi Kuma ta rike kanta da dayan hannun,kuka ta saki sossai,ita tunda aka haife ta Bata taba jin ciwon Kai irn wannan ba,sai da tayi minti uku a haka kafin ta Fara dafawa a hankali tana bin bango har ta shige bayi,jingina tayi da bango ta kunna hita,bayan ruwan yayi zafi ta hada ruwan wanka,wanka tayi hadi da Alwala da tsarki,Bata fi minti 15 ba ta fito daure da towel,bango ta dinga bi har ta Kai wardrobe din ta budewa tayi ta dau wani plane dogon riga Mai Dan kauri Dan wani tsanyi tsanyi  take ji,pant din ta ta dauka da hijab ko bra Bata dauka ba saka kayan tayi sannan tasa hijabi,darduma ta shinfida ta zauna sallah tayi a zaune Dan bazata iya tsayawa ba,ta na idar da sallah ta kwanta a darduma tana tsauke nunfashin wahala,ji take duniyan na juya Maya,ta rasa Mai ke damun ta,ba abin da k fita a idan ta Banda hawayen tautsayin kanta,tun da ta kwanta Bata fito a dakin ba har karfe 10:00 da mama taji shiru ta aiko Husna ta dubo Maya Lailah,ko da Husna ta shigo dakin samun Lailah tayi a kasa ta dukunkune tana barcin wahala,kana ganin ta zakasan ta ci kuka har ta gode Allah,Dan wani irin ja fuskan ta yayi balle ma hancin ta,abinka da farin mutun,tsayawa Husna tayi a bakin kofan ta kasa karasawa ciki,wani hawayen tautsayin Antyn tane ya zubo daga idan ta,takawa ta farayi a hankali har ta nufi inda Lailah k kwance,sungunawa tayi a kusa da Lailah,hannu tasa ta share hawayen daya zubo mata,hannu tasa ta taba jikin Lailah, jitayi yayi wani irin mugun zafi har abin ya Bata tsoro,da tsauri ta mike ta nufi parlor tana tsauka bibbiyu tana Kiran mama Anty,sai hawaye kawai take,ta Isa inda mama take ta fashe da kuka ta rungume ta tace mama "LAILAH"   fashewa tayi da kuka sossai,hankalin mama ne ya tashi sossai,tace k ki gayamin bansan shashanci,"zuciyar mama ko Banda bugun fargaba ba abin da yake,Dan a yanda taga Husna zuciyar ta yayi mugun tsinkewa" ki gayamin Mana me haka,Mai ya Sami Lailah,Jan magana Husna tayi tare da share hawayen idan ta tace,Bata da lafiya sossai,Dan tsaki mama taja tana ture ta, Dan ita tazata wani Abu babba be ya faru,dakin Lailah din ta nufa da tsauri,tan bude kofan ta Fara Kiran sunan lailah ko motsi Lailah batayi ba,"mama naganin haka hankalin ta in yayi dubu ya tashi,Dan tasan Lailah batasan nauyin barci" jijjiga ta ta farayi a rikice,tana Kiran sunan ta tun tanayi a hankali har ta Fara Yi da karfi,Husna da k baya ne ta fashe da kuka tana sulalewa kasa,ko Mai ta tuna,sai ta mike da tsauri ta nufi bayi,ruwa ta debo a cikin wani da karamin roba,ta dawo a rikice,yayyafa Mata ruwan ta farayi Amman shiru kake ji,kwarara Mata duka ruwan tayi a jiki,"wani irin ajiyan zuciya Mai karfi Lailah ta tsauke tana kokarin bude idan ta Amman ta kasa saboda nauyin da Suka Mata,bude Baki tayi a hankali tace Kai na ki taimaka min" fadawa jikin ta Husna tayi tana fashewa da matsanacin kuka tace Anty Dan Allah karki tafi ki barni wlh zan shiga cikin wani Hali inasan ki Allah ta karasa tana kuka tana rokon ta,Dan riketa Lailah tayi Bata ce komi ba Dan Bata iya magana bakin ta na Mata nauyi,mama ne ta katse su day fadin k dagata Dan Allah karki karasa min ita,tashi Husna tayi jin mama tace Kar a karasa ta,dagata mama tayi ta cire Mata hijabin jikin ta,tace mama na Mai k damun ki ne,shiru Lailah tayi ta kasa magana,kimin magana Mana mamana,hannu Lailah tasa ta taba kanta kawai,gane Mai take nufi mama tayi,dagata tayi daga kasa ta dauke ta zuwa bayi tayi Mata wanka sannan ta dawo da ita daure da towel,da yake bata da wani weight sossai shiyasa mama ta iya daukan ta,zaunar da ita tayi a kan gado ta jingina sannan ta dauko Mai ta shafa mata, drawer ta bude ta dauko Mata dogon riga mara nauyi sossai da pant,mika mats pant din tayi, hannu Lailah tasa ta amsa tasa daga zaunen da take,bayan tasa mama ta saka Mata dogon rigan sannan ta dagata ya tsauka kasa,umurtan Husna mama tayi data kawo Mata ruwan tea Mai zafi,fita Husna tayi daga dakin ta nufi kitchen,wurin flask ta nufa tako ci sa'a akwai ruwa a ciki,daukan cup da spoon tayi da tsauri ta dauriye,tsiyaye ruwan zafi tayi acikin kofin ta dauka ta Kai dakin Lailah sannan ta dawo ta dau kayan tea ta nufi dakin da shi,tana kawowa mama ta hada ma Lailah shayi Mai kauri sossai,fifita Mata shayin ta farayi da spoon har yadan huce kadan,dura Mata shayin ta farayi tana lalashi,da haka dai aka samu ta Sha Rabin cup,Dan gabadaya bakin ta Babu test,ko shayin ma ta Sha ne kawai Dan taga yanda hankalin mama ya tashi sossai Kuma batasan tana shiga rashin hankali,a huge cup din mama tayi sannan tace tana zuwa,dakin ta ta shiga ta dauko Mata maganin ciwon Kai Mai suna "SUDREX" da ruwa balla biyu tayi ta Mika Mata da ruwa,amsa Lailah tayi tasha,sannan ta Mika ma mama kofin,amsa mama tayi ta ajiye shi a side drawer,kwantawa mama tace tayi sannan tasa bargo ta lullube ta dashi,Zama mama tayi tayi tagumi tana kallan ta, murmushi Lailah tayi sannan tace mama bakomi na ji tsauki, murmushi mama tayi tace Allah ya Kara tsauki ya Miki Albarka,mamana nasan abin da ya ja Miki ciwon nan Dan Allah kiyi hakuri Kar ki zuba ma daddyn ki kasa a Ido duk da nasan bazaki aikata ba, murmushi daya fi kuka ciwo Lailah tayi tace insha Allah mama, farin cikin ku shine nawa,mama ne tace mamana Mai yasa bakisan Abba ne,"girgiza Mata Kai Lailah tayi tace bakomi mama" akwai Wanda kike so ne,"jin maganan kawai Lailah tayi daga sama,kulle idan ta tayi takasa cewa komi"mama na ganin action din ta tasan tabbas akwai Wanda take so,kallon ta tayi da kyau tace Lailah tanbayan ki nake kin min shiru,"bude idan ta tayi Amman ta kasa kallan mama Dan kunyya,kokarin tashi tayi Amman mama ta Hana ta,kwantawa tayi ta kulle idan ta sossai sannan tace ehhhh mama akwai"kallan ta mama tayi Baki bude tace"Amman Mai yasa Baki taba Gaya min ba", "shiru Lailah tayi na Dan mintina sannan tace ji nayi baba yace bazai min aure ba sai bayan nagama makaranta shiyasa,ta karasa hawaye Mai zafi na zuba daga idan ta" shiru mama kawai tayi tana kallan ta Dan ita Babu abin da zata iya Yi yanzu,Mai gidan ta ya riga da ya yanke hukunci,Babu Wanda ya Isa ya chanza shi sai wani ikon Allah,Mai yasa baki fada ba tun farko,yanzu dai ba abin da zan iya Yi mama na Amman dai bari mugani zan gwada ko Allah zai sa a dace,gyara Mata bargon mama tayi ta rufe ta da kyau,kiyi barci mama na ki huta Dan Allah bansan Kuna sa ma kanki damuwa,bansan wani Abu ya same ki kinsan ku kadai ne gare Ni Dan Allah,ta karasa magana fuskan ta da Dan damuwa, "murmushi Lailah tayi tace Insha Allah mama bazan sa ma kaina damuwa ba",da Allah yasa mama ta amsa sannan ta nufi hanyyan fita a dakin,"tun bayan fitan mama barci ya kasa daukan Lailah, wayan ta ne ya dau Kara tana daukan wayan taga kawar tace k Kira, murmushi tayi sossai tana daga kiran,bayan sun gaisa Lailah tace mutanen Dubai an dawo,dariya kawar ta Mai suna zainab tayi tace wlh na dawo awana biyu ma da shigowa 9ja wlh,Alhmd barka da dawowa, toh Ina tsarabar mu,dariya zainab tayi tace tsarbar ki na nan,I in ban Miki tsaraba ba na shiga uku, murmushi Lailah tayi tace 9 ma ba uku ba,dariya sukayi a tare gaba daya,zainab ne tace matar s,ya s,da hmmmmmmm Lailah ta amsa,zainab ne tace ban gane hmmmm ba ki min bayani Dan Allah,k dai bari wannan maganan bana waya bane,zai kinzo gida Zaki Sha lbr,iko yau yau San zo,k bari ma ki gani yanzu zan shirya na taho, dariya Lailah tayi tace mayya sai aukin jin lbr k dai Allah ya shirye ki,da Ameeen zainab ta amsa tace naji dai,ni dai sai nazo,toh shikenan Allah ya kawo ki lfy,da Ameeen zainab ta amsa tana katse wayan.aje wayan tayi tana murmushi,tunanin halin da take ciki ne ya fado mata a rai,hawaye ne ya taru a idan ta,hannu tasa ta share shi tana Jan hanci,tana cikin tunani wayan ta ya dau ringing,dauka wa tayi taga Yaya Abba ne k yawo akan screen din,wani irin kololon bakin ciki ne ya tokare zuciyar ta,dogon tsaki taja sannan ta kifa wayan a kan gado,miss call hudu yayi Mata a na biyar din ne ta amsa tana wani ciccin magani,sallama ya Fara Mata,amsa mishi tayi a dakile,tan bayan ta yayi ya take da mutanen gida,Nan ma sama sama ta amsa Mai da lfy lau,"shiru yayi na Dan lokaci kadan kafin yace naji daddy yace an bani k Kuma za'a da lokaci Nan kusa ba za'a ja Shi ba" I tun da ya Fara maganan taji jin ta da ganin ta ya dauke,wani duhu duhu take gani,kunnen ta ko dummmmmm! Kawai take ji,sai da ta shafe minti 10 a wannan yanayin kafin jin ta da ganin ta Suka dawo Amman ba duka ba,wani irin kadawa idan ta yayi yayi jajawur,ga hawaye a ciki sai kyalli idan yake,bude Baki tayi ahankali kaman ansa mata abu a makoshi tace Mai kace banji da kyau ba,"shiko da saukin hali ya Kara maimai ta Mata cikin sanyin murya,Dan daga yanda tayi maganan yasan akwai damuwa",Yana Gama maimaita mata ko ta katse kiran, cire wayan yayi a kunnen shi Yana kallon wayan,ji yayi jikin shi yayi sanyi sossai,tun da yake bai taba San wata mace ba bayan lailah,yayi iya kokarin shi Dan ganin ya cire ta a zuciyar shi Amman ya kasa,Zama yayi a gefen gadon shi ya rike kan shi da hannu biyu,ji yayi kan shi na wani irin tsarawa.


💞💞💞LAILAH💞💞💞(COMPLETE) Where stories live. Discover now