Chapter three

8 0 0
                                    

Kusan duk wani wanda muke da hadi dashi yazo mana gaisuwa har da abokan kasuwancin baba duk sunzo danma wasu bazan iya tunasuba, mutane sukayi ta shigowa sunayi mana gaisuwa wasuma bansansuba wasu kuma ba ganesu nakeyiba dan idan za'a yankani bazan iya cewa ga wadanda sukazoba Dan hankalina ba'a kansu yakeba.

Bansan yadda akayi aka samu abinci a gidanba ni dai naga ana ta zubawa mutane abinci ban tambayaba ba kuma acemin ga da yadda aka samu ba, duk dangin baba dana inna sun iso wasuma tare dasu akayi jana'iza, goggo hafsa kanwar baba itama tazo daga kano haka sauran yan uwansu da dangin Inna duk sunzo sai dai duk wannan dangin da suka zo ba ta tamu sukeyiba burinsu su raba abinci su kuma ci, tunda dai aka gama wannan koke koken na farko shikenan aka wuce wajen sai kuma hira da bada labari kala kala.

Tunda akai rasuwar kullum za'a kawo abinci daga makota ko gidan Yan uwa, mutane zasuyi taci suna hada hadarsu kamar ba mutuwa akaiba mu da aka yiwa mu kadai mukasan anyi mutuwa, goggo hafsa itace akan kuloli sai Wanda taga dama zata bawa har fada ake da ita duk da abincin gashinan har yawa yakeyi.

A lokacinne na tuna wani abu Dana taba ji na kuma yadda dashi, mutanenmu idan zaka shekara kana binsu kana rokonsu su taimaka maka da abinda zakaci ko da kuwa bashine ba zasu bakaba amma da ita dai yunwar zata kasheka sai a dafo abincin da zai iya ceton rayuwar taka a kawo wai sadaka alhalin idan ladan suke bukata su baka su ceci rayuwarka yafi lada fiye da su bawa yan zaman makoki.

Duk Kuma wannan rabon abincin da akeyi babu wanda yayi kokarin ko ya tuna da cewar bamuci abinci ba, babu Wanda yace bari yazo ya dan lallaba mu mu sakawa cikinmu wani abu kowa ta kansa yakeyi, Muslim ne kawai yake runtse idonsa daga kallon banza da tuhumar da mutane keyi masa idan ya shigo ya tsallako matan dake tsakar gida ya shigo bamu abinci, kullum zai samo mana wani abu mai dan ruwa ruwa ko tea, youghut, fura ko kunu wanda dai zamuji dadin ci zai kuma tasamu a gaba duk mu ukun sai ya tabbatar munci daidai wanda jikinmu bazai jigataba sannan zai fita hakama su Muazzam a waje zai tabbatar sunci shi da al'ameen kafin ya kyalesu duk da dama su koyaushe yana tare dasu.

Ranar uku akayi musu addu'a a masallaci da Kuma nan cikin gida an kuma yi sadaka a kayan da bansan daga ina sukeba ni dai na gansu kawai, yamma nayi kowa ya watse sai goggo hafsa da baba lawan kawai shima matansa da 'yayansa sun tafi gida saura shi kadai zuwa anjima zai tafi tunda shi gidansa anan dutse yake gida gubu.

Washe gari da sassafe goggo hafsa ta gama shiryawa sai ga baba lawan ya shigo zasuyi sallama, Ina dakinsu Muazzam a kwance abinda yanzu ya zamemin jiki na jiyosu a tsakar  gida suna magana Ina jin basusan ina dakinba dan dan matsowa sukayi daga can namun, baba lawan yace "wai hafsa naga kin gama hada kaya banji kina batun tafiya da wadannan yaranba" bana kallon fuskarta amma nasan yamutsa fuska tayi sannan tace "ban gane me kake nufiba wadanne yara?" Baba lawan yace "yarannan mana ko kina nufin ni zan daukesu gaba daya? Haba baiwar Allah ki duba yawan nawa yayan mana" tace "to bawan Allah ni kana nufin da nake karkashin wani ni zan dauki yara har nawa na kara masa akan nasa? Ai banyi masa adalciba Kai dai da kake providing for your family Kai kake da ikon kara yawan family members dinka baniba" baba lawan yace "amma dai kinsan sunyimin yawa ko? Beside Zulaihatu ta girma kina zuwa ki samu wani anan kanon ki hadata dashi tayi aure suma su Saudatun gaba daya yaushene zaki aurar dasu" cikin whisper-yelling tace "au kana nufin ma ni zan aurar dasu? Tabbas din bazan dauka din ba kenan" duk sukayi shiru da alama kowa tunanin mafita yakeyi.

Wani hawaye ya zubo daga idona  wai yau mune ake neman kai damu kamar wasu shirgi.

Can baba lawan ya nisa yace "to ga shawara" goggo hafsa tace "inajinka Allah yasa ba akai na dai nauyin zai kareba" baba lawan yace "ke garajene dake ki bari na fada mana kafin kiyi mita" tace "ai nace inajinka fadi" baba lawan yace "why not mu barsu anan gidan duk abinda Allah ya hore sai mu kawo musu? Tunda Kinga Zulaihatu ta girma zata iya rikesu sannan Muazzam ma yayi girman da zai zame musu kamar security baza'ace mun barsu ba namijiba mu kuma duk abinda muka rarumo sai mu kawo musu ko yaya kika gani?" Daga jin muryarta kasan murmushin farin ciki takeyi ba zata dau wani nauyiba tace "Kai amma shawarar nan taka tayi sosai kaga sai mu dinga kawo musu dan abinda zasuyi amfani dashi ba tare da mun dorawa kanmu wani aikiba" yace "yauwa ai dama nasan zakiso wannan shawarar tawa" ni kaina da nake nan nafison shawarar tasa dan nafison a ajiyemu a gidanmu gidan ubanmu yadda babu mai takurawa rayuwarmu amma na tabbata duk inda mukaje sai rayuwa ta fita daga kanmu munji inama dai mubi iyayen namu, sannan idan wani waje zamuje sai an rabamu anan kuwa muna tare wannan ma damace na samu ta yadda zan iya kula da kannena yadda ya kamata.

ZulaihatuWhere stories live. Discover now