01-05

33 1 0
                                    

*Kyakykyawa ce*

_A Bewitching Lady_

*By*

_Nafisa Aliyu_
_(Mrs Naseer)_

*Marubuciyar*

*Namijin zaki*🦁🦁
*FaccalaTah*_(The Home Breaker)_



🌎 '''MANAZARTA WRITERS ASSOCATION''' 📚🖊️
*M.W.A*

*Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________
*Note_* bamu yarda wani ko wata su juya mana labari ba tare da izinin mu ba

Page 0️⃣1️⃣⏩0️⃣5️⃣

"sau nawa zan gaya maka Muhsin, sau nawa kake so nayi repeating kai na ne? Bana sonka bana kaunarka, I hate u fool, I really despise u. Ka fita a rayuwa ta please bana son ganinka, u are nothing but a monster, ban taba ganin disgusting somebody irin ka ba. U r such a cunning, irresponsible spoilt brat. Bazan taba sonka ba, ban taba tunanin u'll stoop so low haka akan soyayya ba. Amma kuma ba abin mamaki bane domin charity begins at home, kuma barewa baza tayi gudu danta yayi rarrafe ba. Gargadi na karshe da zan baka shine ka fita a harka ta kafin nayi maka tijara, dan wallahi bazan bari ka zubar min da sauran mutunci na da ya rage ba. Enemy of progress!"

Kalaman wata matashiyar budurwa da ba zata wuce shekara 20-21 ba kenan, yayin da take fuskantar wani saurayi dan kimanin shekara 29-30. Tun da ta fara magana ko kifta ido baiyi ba bakinta ya tsirawa ido yana kallon yadda lebanta yake motsawa, a zahirin gaskia idan ba a kusa da ita kake ba baza ma kaji me take cewa ba wai kuma a haka ita takarkarewa tayi tana zuba masifa.

Dariya ya fashe da ita sanda ya tabbatar da ta gama masifar tata sannan yace.

"Charity begins at home. Wow! Wow Hudah.. har ke zaki ce wani barewa bazatay gudu ba, kin manta wane ne ubanki, Ko kin manta da wa kike magana? To bari kiji, wannan ita ce dama da zan baki ta karshe ko ki yadda ki amshi soyayya ta ko na aiwatar da kudiri na akan kwadayayyar uwar ki da ta biyewa son zuciya ta auri tantirin ubanki. Saboda kinga ina lallabaki zaki kawo min shirme?? Wawiya kawai."

Rawa jikinta ya soma sosai domin kuwa tana iya jure komai a duniya banda a taba mata martabar iyaye, musamman ma Uwarta wacce ta sadaukar da duk wani farinciki nata akan ta.

"Kar ka kuskura ka sake zagar min iyaye Muhsin, ko me zakayi ya tsaya iyaka ni banda iyaye na musamman Nanne ta." Cewar Hudah.

Dariyar wulakanci yayi tare da cewa.

"Nanne, Nanneh. Kaman wata Uwar arziki, naji na daina zagin su amma ki sani hakan ba shi zai hana ni aiwatar da kudiri na ba muddin baki yadda kin amshi tayi na ba. Na baki nan da awa 48 kiyi tunani me kika fi so Ego dinki ko Nannen ki."

Mota ya shige ya fige ta da karfi ya barta nan tsaye tare da bule ta da kurah..

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'una."

Shine abinda kawai ta iya furtawa ta juya itama ta shiga tata motar ta kara gaba..

Gudu take shararawa a kan BUK road babu ko kakkautawa, kasancewar dare ya d'an fara yi yasa bata wani samu tsaiko ba take wuce duk junction din da tazo, unguwar Janbulo naga ta nufa wanda ikon Allah kadai ya kaita gida domin ba kad'an ba tayi reckless driving.

D'an madaidaicin gidan da yake dauke da bakin gate da Abuja brown paint naga ta tsaya, mukulli tasaka ta bude karamin kofan gate din sannan ta shiga ta zuge gate din ta dawo ta shigar da motar ta cikin drive in d'in da a kalla zai ci motoci guda 3. Fitowa tayi naga ta doshi cikin gidan.

Kyakykyawa ce (A bewitching lady)Onde histórias criam vida. Descubra agora