FITA TA UKU

82 11 0
                                    

https://www.wattpad.com/story/245794419?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading

ƘAWATA CE! 💕

    ®NAGARTA WRI. ASSOCIATION

©OUM-NASS

*_SADUKARWA GA: BILLY GALADANCHI_*
  
     BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.

FITA TA UKU

      Sai dai kafin idanuwanta su rufe ta ji an ruƙe ta gami da rungume ta.
   "Taho mu shiga ciki, Nabeelah." Sigar yadda aka kira sunan nata da kuma kukan da ya biyo bayan sunan nata, ta san mutum ɗaya ce tak zata kirata da hakan.
  Mutum ɗayan da ta kasance tsakanin farin cikinta da kuma girmamata a matsayinta na ƙawar ɗiyarta.
   "Momy" ta ambaci sunanta a lokacin da take ƙara ƙanƙameta daga jikinta.
    "Kukan ya isa haka, kina buƙatar samun hutu. Zo mu shiga daga ciki." Ta yi maganar tana zame jikinta da nata, tana ƙoƙarin share hawayen da ke kan fuskarta.
    Mutane suna tattaunawa a kan ta da kuma dalilin shigowarta gidan a yau, amma babu wadda ya mata kallon ƙauna da tausayawa a cikinsu da kuma ƴan uwan da suka zama tsatso nata. Abin da mamaki ƙwarai da gaske, ganin hannunta sarƙafe a cikin na Mahaifiyar Nabeeha, tana riƙe da ita da kuma faɗaɗa mata murmushi duk da tana iya hango wani zuzzurfan rami a cikin idanuwanta, ramin da take da tabbacin ba zai taɓa cikewa ba har gaba da abadan.
   Har zuwa lokacin da suka raɓa ta kusa da mutanen da suke zunɗenta cikin rashin sa'a kunnuwanta suka sake ɗauko mata mummunan kalamansu.
    "Ina ji a raina ba haka kawai yarinyar nan ta bar 'yan gidan nan ba, Ma'u. Kiga yadda Hajiya Maryama ta keta dubbanin mutane 'yan gaisuwa ta zo ta kama hannunta suka shige."
     "Kina mamaki da al'amarin talaka, Habi. Wannan kaɗan daga cikin shu'umancin da zai yi domin samun wajen zama a zuciyar masu tsaba a hannu. Sanin kanki ne a tarihi babu wani ƙawancen da ya kai na yaran nan, kamar yadda babu wata mace da zata iya sadaukar da komai na rayuwarta a kan ƙawar da ba su haɗa komai da ita ba. Koda kuwa tana ganin ajalinta a wuyanta ne. A  tunaninki wannan duk ya faru ne a son rai ba wai da dafa'in asiri irin na malaman soro 'yan na gada ba ne?"
   "Tabbas Biri ya yi kama da Mutum, Ma'u. Haka kawai ruwa baya tsami banza, na daɗe ina lalimen amsar da zata gamsar da ni a kan alaƙar Nabeeha da Nabeela ashe wannan ne. Kai Allah ka mana tsari da mugwayen mutane."
   "Amin." Ma'un ta amsa.

    Idanuwa Nabeelah ta lumshe wasu hawaye masu zafi na gangarowa a kan fuskarta.
   Ta riga da tasan shekararta ta kama, kamar yadda watan ƙaddararta ya tsaya ƙyam a sararin samaniya.
  Ita kanta bata san me ya sa idanuwanta suka gaza rufewa ba, kamar yadda bata san dalilin da yasa har a yanzu bugun zuciyarta ke harbawa ba.
    Tana tafiya ne kawai da taimakawar jagorancin da Momy ke mata, ta hanyar riƙe hannayenta, amma badan haka ba da zata iya kuskuren bin hanya a gidan ya ke da hatimin sunanta na ahalinsu.
    Tana ganin mutanen da suke ratsawa a ko ina na gidan, wasu na jero mata sannu da ta'aziyya yayin da wasu suke aiko mata da muguwar harara.
  Ɗakin da yake amsa sunan nasu ita da Nabeeha Momy ta buɗe ta shigar da ita cikin ɗakin, yana zaunar da ita a bakin gadon, da take ganin kamar an ɗorata ne a kan ƙaya.
  Wadda a baya take hawansa da alfahari da kuma koɗa taushin da ke cikinsa.
    "Ki yi haƙuri Nabeela, ki daina kukan. Ki zauna anan zan turo miki Sajida ta zauna tare da ke."
  Momy ta faɗa tana ƙoƙarin juyawa, sai dai kafin ta juya ɗin Nabeela ta riƙe hannunta, kukan da take dannewa tun bayan zuwanta gidan ya fito.
  Muryarta a ciki take maganarta na fita ne da rawar muryar da kuma rauni "Momy da gaske ne Nabeeha ta mutu? Da gaske Nabeeha ta tafi ta barni a duniya? Duk abin da ya faru a kwanaki biyun da suka wuce da gaske ne Momy? Idan da gaske ne me yasa mutuwar bata haɗa da ni ba? Me yasa mutuwar baya ɗauke ni a madadin Nabeeha? Me yasa Momy? Sam ban cancanci rayuwa ba? Ba ni ya kamata na rayuwa ba? Ba ni...."

  Hannu Momy ta ɗora a kan bakin Nabeela tana girgiza mata kai, tana ɗaukan duk dauriyarta da son jajircewa ganin ta kawar da hawayen da ke shirin zuba a idanuwanta, sai dai hakan ya gaza, a matsayinta na uwa ta kasa jure ƙunan rashin Nabeeha da ta yi, kamar yadda Kalaman Nabeela da ganinta a gabanta ya ƙara rura wutar kewar ɗiyarta a zuciyarta.
  
   "A'a Nabeela! Karki yi saɓo a kan abin da ba mu ke yiwa kan mu ba. Karki ƙaryata zahirin da buwayar Ubangiji kan fito. Ubangijin da ya bamu Nabeeha a lokuta masu yawa, ya sanya soyayyarta a zukatan mu, ya kuma sanya mana murmushi a lokutan da muke tare da ita. Ya karɓi kyautarsa, a bayan hakan sai ya bar mana ke dan ki maye mana wajen Nabeeha. Ki zama madadi a gare mu.
   Nabeela, Mutuwar wani takan sama silar ɗaukaka wani, a yayin da mutuwar wani takan zama naƙasu ga rayuwar wani. Wani kuma yakan mutu ya bar baya mai kyau da za a jima ana ta yabo da nanata alkhairinsa. Wadda a zahiri ne kawai ya mutu, amma a baɗini yana raye da soyayyar mutane.
   Ina da tabbacin Nabeeha bata mutu ta bar mu har abada ba, zata ci gaba da kasancewa a raye ne a zuciyoyinmu."
   Ta kai ƙarshen maganar tana jan zuciya da kuma share hawayen da ke sauƙa a kan kuncinta. Ta daɗe tana son ta samu mutum ɗaya da za su tattauna a kan Nabeeha, amma duk wadda yazo ƙara mata rauni yake, yana kiran sun yi rashi, rashin da ba za su taɓa maye gurbinsa ba. Amma ta sani Ubangijin da ya amshi rayuwar Nabeeha a lokacin da suke tsaka da sonta, zai musauya musu da mafi alkhairinta. Amma kuma ta ina? Ta wata hanyar ne hakan zai tabbata? Wannan amsar ce bata da ita.
   Sai dai a duk lokacin da tunaninta ya zo gaɓar nan maganar Nabeeha kan dawo mata tar a kan kunnuwanta kamar a lokacin take faɗa mata.
   _'Momy, kullum kuna ɗora soyayyarku da kulawarku a kaina, kuna damuwa idan ciwo ya kamani. Ni kuma damuwata tana ga damuwar da kuke shiga ne. Ku daina tsoron idan ciwo ya kamani zan mutu na barku. Domin koda na mutu zan bar muku abin da za ku kalla a madadina, za ku kalli Nabeela a matsayin da kuka bani, za ku kalli fuskata a cikin tata fuskar. Nasan itama zata kula da ku fiye da yadda zan baku kulawar, fiye da yadda zan nuna muku soyayyar da nake muku.'_
  Wani hawayen ya sake sauƙowa a kan fuskar Momy a lokacin da wannan maganar ta sake dawo mata, tana ƙara rintsa idanuwanta a lokacin da ta ji rungumar da Nabeela ta mata.
    "Me yasa a komai na rayuwa mutuwa kan zaɓi mutanen kirki ta yi awun gaba da su, Momy? Nabeeha ta tafi ta barni da tarin abubuwa masu nauyi da wahala. Ta barni da nauyin da ya rinjayi kafaɗuna. Ta ina zan iya sauƙe wannan nauyin?" Ta kai ƙarshen maganar tana ƙara fashewa da sabon kuka, ta daɗe tana ji ana cewa hawaye rahama ne ga bawa, a duk lokacin da ka zubar da shi zaka samu sassauci daga ƙuncin da ka samu.
  Sai dai ita bata ji rahamar da sassaucin ba, asalima tana jin ƙuncin da ɗacin da bata taɓa ji ba a tsawon rayuwarta ta duniya. Ko lokacin da suke tsaka da talauci da wahalhalun rayuwa bata ji ƙunci haka ba. Ashe dama ƙarya take data ke cewa talauci ƙunci ne a rayuwa? Ashe dama ƙarya take ji da takai cewa rayuwarta tafe take da rashin sa'a? Ashe rashin sa'arta ta baya sa'a ne gareta idan aka haɗa da ɗaukewar Nabeeha a cikin rayuwar tata?
    "Ya Allah Na tuba ka yafe min?" Ta yi maganar numfashinta na ɗaukewa sama sama, tana jin ƙirjinta yana ƙara yi mata nauyi da zafi, wani maƙoƙon abu na tokarewa a maƙwallaton ta.
    Iskar da ke kaɗawa a ɗakin ta gaza wadata shigarta zuwa hunhunta.
    "Allah baya ɗorawa bayinsa nauyi da wahala har sai ya san zai iya ɗauka. Allah bai ɗora miki nauyin abin da Nabeeha ta bar miki ba har sai da yasan za ki iya." Momy ta yi maganar, sai dai kamar ta makaro domin maganar tata ta fita ne a lokacin da numfashin Nabeeha ya ɗauke cak.
  Ta sulale ta zame a jikin Momy tana shirin kaiwa ƙasa, Momy ta tarota tana kiran sunanta da tashin Hankali.
   "Nabeela!" Sai dai sautin bai kai ya riski kunnuwanta ba balle ƙwaƙwalwarta ta sarrafa shi zuwa ga zuciyarta.
    Kwantar ta tayi, ta fita a ruɗe tana kiran mutane, tana ambatar sunan Nabeela, sai dai kamar mutanen wajen babu kunne a jikinsu, kamar yadda take tsammanin ba zuciya ne a jikinsu ba.
   Kaɗan ne a cikinsu suka iya kallonta da bata amsa "In dai sai mun je mun taimaka mata ne zata rayu, to kuwa mutuwar alkhairi ce a tamu rayuwar."
   Bata san abin ya kai haka ba, kamar yadda take da tabbacin nasu zuciyoyin dutsuna ne.
  "Nabeela amana ta ce, da Nabeeha ta bar min. Dan Allah ku taimaka min." Ta yi maganar da murya mai tsananin rauni a bayyane tashin hankalinta ke fitowa.
   Amma babu wadda ya yi yunƙurin taimaka mata, ganin tana ɓata lokacinta yasa ta shige sashenta wadda anan ne 'yan uwan Nabeela suke, ta kira Maman Nabeela tana sheda mata halin da ake ciki.
   Ga mamakinta taga Maman Nabeela bata girgiza ba, kamar yadda bata damu da jin halin da take ciki ba "Mutuwar Nabeela a yanzu sauƙi ne ga rayuwar mu, Maman Nabeeha. Wataƙila kuma ta zama kaffara ga danginmu da za su samu damar yin yawo ba tare da an nuna su ba.
  Ki barta ajalinta ya ɗauki rayuwarta, ki barta ta mutu a lokacin da take tsaka da tunanin ta cika burinta."
   Ƙamewa Momy ta yi, tana buɗe idanuwanta da bakinta tana kallon Ammin Nabeela da take magana kamar ta maƙiyanta.
    Mayar da kallonta ta yi ga su Ummi da suke zaune suma kansu a ƙasa, ba zata fahimci halin da zuciyoyinsu suke ciki ba, amma tana da tabbacin ƙila su su iya taimaka mata.
   "Ummi zo mu je ki taimaka a sata a mota ki kaita asibiti."
   "Ban amincewa wani daga cikin yarana ta sake taimakon Nabeela ba koda tana bakin kura ne?" Ammin Nabeela ta sake yin maganar tana ƙoƙarin tashi da barin ɗakin.
  Ruƙota Momy ta yi tana kallon Ammin idanuwanta ya yi raurau, tana jin ɓacin rai na rayuwa wadda ko a mutuwar Nabeeha bata ji shi ba.
    "Wata irin Uwa ce ke Zaliha? Me yasa?" Momy ta yi maganar tana neman abin da zata faɗa a ƙarshe tana rasawa.

    "Kamar kowata Uwa ta gari, Momy Nabeeha." Ammi ta bata amsa tana raɓawa ta gefenta tana ficewa.
  Ta dafe kanta a lokacin da ta kai kallonta ga su Anty Ummi da take da tabbacin ba za su tsallake Umarnin mahaifiyarsu ba.
     Juyawa ta yi ta fice daga sashen tana jin zuciyarta kamar an ƙyasta ashana a kan fetir  'Tabbas mutane gajiyayyu ne, haka kuma ruɗaɗɗu da suke ɗauke da rauni na ɗaukan damuwar wani su ɗora a kan tasu. Banda haka me yasa suma ƴan uwanta za su zama kamar gama garin mutane?'
   Komawa ɗakin da ta bar Nabeela ta yi, ta sameta a kwance kamar yadda ta barta.
   Tunaninta ne ya tsaya a kan taimakon da zata iya bata, ƙaramin friegh ɗin da ke ɗakin ta buɗe ta ɗauko ruwa mai sanyi da yake ɗauke da ƙanƙara ta fara zubawa a kan Nabeela.
  Ruwan na sauƙa a kan goshinta zuwa gangar jikinta sai dai kamar tana zubawa gini ne ruwan bayi. 
  Babu alamun numfasawa a jikinta hakan ya ƙara tsorata ta fara jijjigata tana kiran "Dan Allah Nabeela kada kema ki tafi ki bar mu..."

🌷🌹🌷🌹🌿

  Har yanzu ina baku tabbaci a kan labarin ƙawata ce Dabanne da sauran labarai na. Ina jin tasirinsa da haɗuwarsa fiye da labaran da na rubuta, wadda kuma shima ya ke ɗauke da hausa gangariyar da babu surki a cikinta.
 
   Ina fatan kun fara amsar saƙon, kamar yadda nake fatan samun dafifi da ƙauna daga gareku.

Ƙawata ce! Paid book ne a kan N300 kacal, akwai free pages da za su biyo baya a gaba.
  Ga masu buƙatarsa za su iya turo kuɗin ta wannan accnt 👉3051894647 Hajara Ahmad Hussain polaris Bank. Su tura katin shedar biyansu ta wannan lambar 08030990232 ko +234 703 513 3148 Ga wadda basu da accnt kuma za su iya turo katin waya na mtn ta waɗannan lambobin.

#KWTC
#NWA
#CMNTS, LIKE SHARE,
#GIRMAMAWA
#DABANNE.

  Oum-Nass

ƘAWATA CEHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin