RAYUWAR MU

28 3 1
                                    

RAYUWAR MU.

    Rayuwar mu  rayuwace mai matukar tarwatsa kan mai tunani,rayuwa ce wacce batada iyaka,tafiya Kawai muke acikinta batareda sanin madakatar ta ba,wata bahaguwar rayuwace wadda sai mai kaifin tunani dakuma nazari zai fahimceta,dafarko dai sunana Fatima Muhammad yar asalin jihar borno,mahaifana Sun dawo garin zaria domin anan aka haifeni,rayuwa mukeyi gwanin ban sha'awa kasancewata 'ya daya tilo awurinsu,ina da shekara goma sha biyu ciwon ajali ya riski mahaifiyata,ranar wata juma'a ta rasu ta barni cikin wannan duniyar mai abubuwan ban mamaki,tun daga wannan lokacin nashiga cikin wata rayuwa wadda bazan iya fassarata ga rayuwar jin dadi ba sakamakon zama ahannun kishiyar uwa.Na sha wahala matuka awurin matar mahaifina ta yadda mai karatu baya zato,mahaifina baida masaniyyar azabar da ake gana min kasancewarsa matukin babbar mota ne kullum suna bisa titi.
Ahaka rayuwata tachigaba da kasancewa cikin tsangwama,kyara,da azabtarwar kishiyar uwa,inada shekaru shashidda aduniya Ibrahim ya shigo cikin rayuwata,ganin mun fuskanci juna yasanya mahaifina ganawa da Ibrahim cewar ya turo magabatansa,babu bata lokaci aka fara shirye shiryen biki duk da baqar kiyayyar da mahaifiyar Ibrahim ke nuna min kasancewar mahaifina talaka,qiyayyarta gareni bata taba damuna ba domin ina sawa araina ai ba da ita zan zauna ba.
A kaduna Ibrahim ke aiki a lokacin,amma zamu fara zama agidansu na zaria kafin wani lokaci,na nuna mishi damuwata akan zama tareda mahaifiyarshi anan ne yake fadamin tana da aure gidan Alhaji mai wake ba agidan mahaifinsu take da zama ba,Hakan ne yakara min karfin gwiwar auren Ibrahim,Sati biyu da aurenmu muna zaune cikin farin ciki da kwanciyar hankali mahaifiyar Ibrahim tadawo gidan da zama,saboda ta nuna min qiyayyar datake min a aikace,mijinta na wnn lokacin ya bukaci data koma gidansa ko kuma ya sawwake mata,babu wani tunani ta ce ya sawwake mata ta dawo gidansu Ibrahim domin munanama rayuwata,komai zanyi bata gani,bata kaunata bata kaunar mai kaunata,banza wofi yafini daraja a idanunta,zata yini tana cimin mutunci nikuma banda aiki sai kuka,alokacin dana haifi diyata ta fari gida gida tabi tana fadin anyi daya ba qari,alokacin tafara jifana da munanan asirai,na duqufa na fawwalawa Allah komai duk da halin tsananin rayuwa danake ciki,duk yunkurinta akan Ibrahim ya sakeni ya tashi abanza,asiri take jifanmu daga ni har shi Allah bai bata nasara ba,acikin wannan yanayin na haifi 'yata ta uku wadda taci sunana fatima shima ba irin cin mutuncin da Mahaifiyar Ibrahim batai min akan yace in zabi sunan Yarinyar,bayan kwana goma sha biyar da haihuwar Allah ya karbi ran mahaifi na,narasa mahaifana narasa farin cikin rayuwata,banida yayye banida kanne,dangin mahaifana bawanda ya damu da damuwata bare har ya sharemin kuka na,ganin haka yasa mahaifiyar Ibrahim tsaurara min,qiyayya take nuna min tareda yayana bata wasa ba,kullum Ina cikin kunci da bakin cikin rayuwa,haka yayana suka fara tasowa cikeda tsantsar kiyayyar kakarsu dakuma dangin mahaifinsu.Ta mayar da rayuwarmu tamkar ta bayi marasa galihu,ta rufewa Ibrahim baki baya iya cewa komai akai,Wata ranar asabar Ina zaune tareda yayana ta bankado min cikin dakin tana fadin"mayya Kawai wacce kare ya lashe zuciyarta,mara asali mara amfani,indai nice wallahi saina lalata rayuwarki"jin haka ya tsoratani matuka,amma yaya zanyi?haka nachigaba da zama duk da irin asiran datake jifana dashi,bana iya bacci,gabadaya na firgice nazama tamkar sabuwar mahaukaciya,wannn ne karo na farko dana kai kararta gurin yayan mamana,ga mamakina cewa yayi na tashi nakoma gida kafin ya rufeni da duka,mara hankali,ina kike nufin zaki dawo da yaya biyar ? uban waye zai ciyar dasu?ina kuka na koma gidan Ibrahim badon raina yaso ba sai Dan banida yadda zanyi domin mahaifiyarshi ta mayar min da rayuwata tamkar ta dabba,rayuwar wasu dabbobin ma tafi tawa,sau dayawa nakanyi nazari akan meyasa iyayenmu suke tilasta mana zaman auren da babu komai acikinsa sai tsantsar cutarwa?Haka rayuwata ta chigaba da tafiya babu jin dadi,kullum cikin zagina da yayana,gashi sai Ibrahim yayi wata biyar zuwa shida awurin aiki bai zo zaria ba,narasa inda zan sa kaina inji dadi,yayana kawai nake kallo inji sanyi araina,kullum cikin tunanin yadda rayuwar mu zata chigaba da tafiya ahaka nakeyi,muna cikin haka Ibrahim ya rasa aikinsa,dole ya dawo zaria yazauna babu aikin yi,nan ma mahaifiyarshi ta qara tsaurara Rashin imaninta agareni,acewarta tunda Ibrahim ya aureni ya dena ganin alheri cikin rayuwarsa,nayi kuka har nagaji,banida wanda zai share min kuka na sai Allah,abinci ya gagari bakinmu dani da 'ya'yana,saide mahaifiyarshi ta kirashi dakinta suci alhalin nida yayana muna cikin tsananin yunwa,sau dayawa zuma nake lasa musu abaki su kwanta ko kuma in hada wuta na dora ruwa acikin tukunya yayta tafasa a zuwan girki nake har suyi bacci,sa'ar danayi shine Allah ya azurtani da yaya masu matukar hakuri,sune ke sharemin hawaye idan Ina kuka,sai da takai idanuna suka daina fitar da hawaye,ganin yunwa na kokarin halaka ni yasa na fara barar abinci alhalin mahaifiyar ibrahim na iya ciyar damu,ganin barar bazata fissheni ba yasa na karkade sakamakona na gaba da firare domin neman koyarwa,shima da dakyar na samu,ina murna nadawo gida mahaifiyar Ibrahim tace sam bata san magana ba,ban isa ba ,uban wa zan riqa barwa yayana?nayi kuka tamkar raina zai fita,ga yunwa,ga rashin sutura,rashin kwanciyar hankali,yayana na zaune gida babu makarantar Islamia bare ta boko,alokacin naji karfin zuciya,dole na miqe na kwaci yancina wanda mahaifiyar ibrahim ke wasa dashi,batareda yardarta ba nafara koyarwa tareda toshe kunnuwana ga duk wani zagi da cin mutuncinta,haka nake barin yayana agidan tana azabtarwa tamkar ba jikokinta ba,Aranar wata litinin ina makaranta amma hankali gabadaya ya karkata zuwa ga 'ya'yana,kasancewar akwai yan haya agidan yasa daya daga ciki ya faki idanun sauran yayana ya dauki karamar cikin su yashige daki da ita,Allah kadai yasan irin ta'addancin da yayi mata,koda yan uwanta sukaga tanata kuka mai cin rai suka tambayeta mutumin tariqa nuna musu,ahaka na dawo na samesu,cikeda tashin hankali na fashe da kuka na shako wuyan mutumin daga baya na zube awurin Ina kuka mai cin rai,wannan wacce irin rayuwace?koda mahaifiyar Ibrahim tazo cewa tayi ban isa na korar mata dan haya ba saboda mugun halina,daga karshe ni aka baiwa laifi,nayi kuka mara fasaltuwa daga baya na miqa ma Allah lamurana domin shine kadai zai min magani,tamayar da ibramin mutum mutumi baya iya sawa ko hanawa,bayan kwana biyu yata tafara Rashin lafiya inda likitoci suka tabbatar da lafiyarta kalau,sedai baa kara kwana biyu ba Allah ya karbi ranta,nayi kuka mara mafasaltuwa,na rasa inda zan saka rayuwata,matsaloli sai bullowa suke ta kowani lungu,addu'a da kuka sune aikina,aloakcin na qara zage damtsen kula da yayana da kuma niyyar chigaba da karatu zuwa matakin degree,hakika nasha wahalar rayuwa mara fasaltuwa,nayi kukan da babu hawaye acikinsa,sedai dama idanun dasukai kuka yau wata rana sune zasuyi dariya,bayan wasu shekaru na kammala karatuna na samu aiki mai babban albashi kasancewar karatun boko bai yawaita ba,tun kafin lokacin aurena da ibrahim ya mutu,agidan wata aminiyata nake zaune tareda yayana har lokacin dana kammala makarantar.Kulawar da yayana suka rasa abaya nake basu babu kakkautawa,rayuwata ta gyaru tamkar ban taba shiga halin tsananin rayuwa ba,nida yayana mun zama abin birgewa dakuma sha'awa awurin mutane musamman wanda basusan tarihina ba,idan naji wasu suna fadin dama ni ce ke nakanyi murmushi Kawai domin daga ni sai mahaliccina yasan irin bala'in dana shiga,karatun boko yazame min alheri cikin rayuwata,yazame min gata alokacin dana rasa gatan kowa,karatun boko ya zame min fitilar dake haske bakaken darena,mahaifiyar Ibrahim ta kamu da shanyewar barin jiki yayinda muka shirya nida mijina kasancewar mahaifiyarsa ce sanadiyyar korarsa da akayi a aiki duk dan rayuwata ta zama abar tausayi,se gashi Allah ya min zabi mafi alheri,mun zama tsinstiya madaurinki daya!.
  

Alhamdulillah

Episode two coming soon...

RAYUWAR MU...Where stories live. Discover now