Page 01

826 37 2
                                    



Shin kun san girman hakki kuwa? Kun san girma da darajar da uwa take da shi? Kun san babbar tabewa ce ga mai murje darajar uwa? Kun san cewa hakkinta ba zai bar mutum ba? Ku biyo ni tsamo-tsamo cikin labarin SAFIYYA USMAN BABA, labarin da zai taba zukatan duk masu bibiye da shi. Zai bar ku da al'ajabi gami da tunanin da gaske akwai mutane irin Safiyya Usman Baba? Ba wani dogon labari ba ne, sai dai zai iya shafe dogon zango zaune daram a cikin zukatanku.

BABI NA ƊAYA

Yara ne zagaye da ita, waɗanda ba za su wuce shekaru goma sha ɗaya ba, ta sanya su tsakiya hannunta riƙe da littafin Turanci mai suna 'The Priceless Jewel.' Karanta musu take yi da Turanci sannan ta dakata, ta fassara shi da Hausa.
A daidai ƙarshen shafi na goma sha biyu ta dakata sanadiyyar kaɗa ƙararrawa da aka yi alamun an tashi kwata-kwata daga makarantar.
"Za mu dakata a nan, sai kuma idan Allah Ya sa mun sake samun wata free period ɗin sai mu dasa daga inda  muka tsaya."
Ta faɗa bayan ta rufe littafin ta cusa shi a cikin ɓarkakkiyar jakarta da aka ɗinka da atamfa.
"Sofi tunda dai yau Alhamis babu Islamiyya, me zai hana mu zo gidanku sai ki ƙarasa mana...?"
"Rafi'a? Kin san me kika faɗa kuwa? Ku zo gidanmu wato ganin ƙwaƙwaf ko? To ni ba da ni ba, gaɗa a masallaci. Duk abubuwan da kuke aikatawa babu abin da ba ya dawowa a kunnuwana; an ce kuna zuwa gidajen ƙawaye don ganin arziƙinsu. Ku tambayi sauran 'yan aji idan akwai wacce ta taɓa zuwa gidanmu. Ba na son son a sani sa uwar miji makarantar kyatarin. Duka karatun ma za ku ja in daina."
Dukkansu sororo suka yi kamar bunsuru a mayanka, suka zuba mata idanuwa tare da kallon masifar da take musu. Sun sha jin cewa Safiyya ba ta taɓa bari a je gidansu, sau ɗaya da Amina ƙawarta ta bi sawunta ta gano gidansu ba ƙaramin tashin hankali aka yi ba. Tun abun yana ba su mamaki har ma sun daina, sun rasa gane Safiyya wace irin mutum ce.

A hankali suka hau darewa bayan duk sun ɗauki jakunkunansu, ya rage Safiyya ce kaɗai a cikin ajin tana maimaita Lissafi, darasin da aka yi musu ɗazu. Sai da ta kai ƙarshe sannan ta rufe littafin ta cusa shi a cikin jaka tana faɗin,
"Ku jiye min jaraba, dahuwar fatar raƙumi. Wato da tsiya sai sun je sun ga
Goggonnmu bebiya mai in-ina, ta yi magana su yi dariya saboda jajayen haƙora ko? To ba ku isa ba."
Ta rataya jakarta haɗe da ficewa daga ajin.

A bakin ƙofa ta ci karo da wata yarinya wadda ba za ta wuce shekara bakwai ba tsaye tana jiran ta. Cikin tsiwa da tsino baki kamar shantu ta ce,
"Ke kuma Shatu me ya hana ki tafiya gida?"
"Kin manta Goggo ta ce kar in sake tafiya ba tare da ke ba? Tun ɗazu ai ina nan tsaye ina jiran ki."
"Mtswww!"
Ta ja dogon tsaki haɗe da yin gaba Shatu ta bi bayanta.

Ko da suka isa gida Goggonsu na zaune da faranti a gabanta tana gyaran wake. Baki buɗe kamar gonar auduga ta tarbe su, Shatu ta shiga jikinta, Safiyya kuma daga nesa take faɗin
"Goggonmu ya na ga wake a gabanki? Kar dai sai yanzu za a ɗora mana abincin rana."
Cikin ƙoƙarin fitar da maganar Goggo ta ce
"Da ƙyai na...na samu kuɗin nan Safiyya. Tun...tun ɗazu nake zaman jiyan Indo ta kawo min biyan bashi am...ma shiyu, nini...ni na gaji na bi sawunta. Da ƙyai dai na samu ɗayi biyai a wuyinta. Muna da...da shinkafa shi ne na sayo wake da mai."
Babu 'ra' a bakinta sai dai 'ya' saboda bebiya ce, ga kuma in-ina da take yi.
"Wayyo Allah Goggo to kuma ya zan yi da yunwa? Har cikina ciwo yake fa."
Shiru kawai Goggon ta yi don ta san halin Safiyya daga nan har isha'i ba za ta daina yanyana zancen ba, kamar tsohuwa haka take da mita.

Sai bayan la'asar sannan ta gama dafa abincin, a daidai lokacin Safiyya ta gama mogalewa kamar molaƙaƙƙiyar tasa, saboda yunwa, haka take ba ta da jimirin yunwa ko alama. Shatu da ta kasance ƙarama ma ta fi ta ƙoƙari don tare suka yi girkin duka da Goggo har barkono ita ta daka.
"Ki je... kit...tada Safiyya...daga...daga bacci, ki ce... tazz...ta zo na gama...abincin."
Da gudun Shatu ta nufi ɗakinsu ta iske Safiyya ba bacci take ba sai dai ta yi lamfo tamkar mai baccin. Tana ganin Shatu ta yi saurin miƙewa don ta san kwanan zancen, musamman da ta shigo tana ƙwala mata kira.
"Saura kaɗan in mutu da yunwa."
Ta fita tana faɗi da ƙarfi yadda Goggo za ta ji. Kai kawai Goggo ta gyaɗa don tsayawa biye wa Safiyya ɓata lokaci ta ɗauke shi. Ga iya magana kamar wadda ta tashi cikin tsofaffin mata. Idan ta saki wata karin maganar tamkar mai haddar hirarrakin tsohuwar mace.
A makimancin faranti ta zuba musu abincin ita da Shatu. Tsakar gida suka zauna suka ci sosai abun mamaki a take sai ga Safiyya ta gyagije tamkar ba ita ba.
"Ni...ni ban ma...ban ma ce kokkkkkkok..."
"Koko?"
Safiyya ta yi saurin tarbar Goggo.
"Yaya Sofi ki bari ta ƙarasa mana. Kin fa san ba koko ta ce ba."
Shatu ta faɗa don ta tsani wannan halin na Safiyya, ta sani sarai wulaƙanci ne ke sanya ta yin irin haka.
"To ci gaba da faɗi Goggo. Me kike son cewa?"
Ba tare da ta kalli Goggon ba ta faɗi haka tana ƙoƙarin miƙewa.
"Ko bismillah ban...babbbbaan...ce kin yi ba."
"Na fa yi fi awwalihi wa akhirihi Goggo. Na manta ne."
Gyaɗa kai kawai Goggo ta yi. Halin Sofi sai ita ta faɗa a zuci.

Bayan sun gama cin abinci sai ga sallamar yara daga zaure, shiru Sofi ta yi jin kamar ta san masu muryoyin, babu shakka ta sani ɗin, domin kuwa ƙawayen nan nata ne suka zo kamar yadda suka ci alwashin kawo mata ziyara, da izini ko ba da izininta ba.
Da sauri ta miƙe tana dosar bakin ƙofa, yara biyar ne duka kansu ɗaya, cikin mamaki take bin su da kallon sama da ƙasa, kafin cikin sanyin jiki ta ce,
"Yanzu da tsiya Azima sai da kuka zo? Wait! Da izinin wa ma?"
Caraf Rafi'a ta ce,
"Mun zo ki ƙarasa karanta mana littafin nan ne."
"Shin wai dole ne?"
Sofi ta tarbe ta cike da masifa.
Shiru suka yi su duka suna kallon ta. Sosai suke tsoron tsiwar ta, sai dai fa alwashi ne suka ɗauka dole za su je gidan su Sofi don su ga dalilinta na ƙin son  a je gidansu.
"To ai sai ku juya ku tafi tunda dai kun yi gulmar. Kamar yadda kuka ga zauren haka cikin ma yake. Ba mu da komai sai kujera taya-ni-gulma da tabarmar kaba. Shi kenan?"
Ta faɗa tana watsa musu kallon banza.
"Amma Sofi ai ya kamata mu gaishe da Goggonku. Sauran ƙawaye duk wadda ta je gidajen juna ana gaida ummansu. Don haka ya kamata ke ma mu gai da Goggo. Ko Batula?"
"Azima ki kiyaye ni wallahi. Yau ni na ga tsiya, ɗinkin ludayi. Dole ne wai?"
"Ba dole Sofi. Bari mu tafi to."
Rafi'a ta faɗa tana kama hannun su Azima domin su tafi. Baki ɗaya sai jikin Safiyya ya yi sanyi tamkar kazar da aka watsa wa gishiri. Ta kalli yadda suke ƙoƙarin barin gidan, ta yi gaggawar riƙo hannun Rafi'a, cikin dariyar yaƙe ta ce,
"Ku yi haƙuri ƙawayena kun ji, raina ne a ɓace. Ku jira ni yanzu ina zuwa, sai ku shigo."
Tsayawa suka yi kamar yadda ta faɗa musu, ita kuma ta shiga ciki.

A tsakar gida Goggo take zaune da Shatu gabanta tana koya mata darasin Turanci da aka yi musu yau. Bayan ta zauna kusa da Goggo ta ce
"Goggonmu..." tana son ɗora wata maganar amma ita kanta nauyi take ji. Goggo ta ɗago kanta ta kalle ta, yanayin fuskar Safiyyar ya tabbatar mata da akwai magana, sai ta rufe littafin Shatu, ta ce
"La...laaafiya Safiyya?"
Kamar tana jiran ta ta yi caraf ta ce
"Goggonmu, kin ga ƙawayena ne suka zo, kuma ni dai ba da izinina suka zo ba. Suna da gulma sosai don na tabbata ma gulmar ce ta kawo su. Don Allah idan sun shigo ko sun gaishe ki kar ki amsa, kawai ki yi musu murmushi daga nan zan ja su ɗaki mu yi karatu. Kin ji Goggonmu?"
Gyaɗa kai kawai Goggon ta yi, kai tsaye ta fahimci inda Safiyya ta dosa. Mamakin halin yarinyar take yi, yarinya ƙarama da ko makarantar sakandire ba ta je ba amma ta san ta ɓoye asalinsu, ta san kar ƙawayenta su san larurin mahaifiyarta.
Jin shirun Goggo ya sanya jikinta yin sanyi, ta ɗan runtse idonta sannan ta buɗe su ta sauke a fuskar Goggo da ke neman ci gaba da uzurin gabanta. A marairaice ta ce
"Don Allah fa Gog..."
Da hannu Goggon ta dakatar da ita. Sannan ta ci gaba da koya ma Shatu karatunta.

Jiki babu kuzari Sofi ta koma zaure ta shigo da su Azima. Har ƙasa suka tsuguna suka gai da Goggo,
"La...lallafiya. Sannu...sannunku 'ya'yana." Ta amsa musu, fuskarta ɗauke da annuri.
Duƙar da kai kawai Safiyya ta yi, gani take shi kenan ta shiga uku sun ga wallenta, ƙaryarta ta ƙare. A matsayinta na shugabar makarantarsu wai yau ita ce sauran ɗalibai suka ga Goggonta, Goggonta mai jajayen haƙora, mai in'ina, sannan bebiya. Ta sa hannu ta shafi fuskarta, tana jin wani irin takaici na mamaye duniyarta, gumi na ratsowa ta tsakanin fatar fuskarta yana sauka wuyanta.
"Ku mu shiga ɗaki in karanta muku abin da ya sawwaƙa."
Ta faɗa tana miƙewa duk suka bi bayanta, kowaccensu da abin da take saƙawa a cikin zuciyarta, tare da mamakin mummunan halin Safiyya duk da ƙarancin shekarunsu.

HAKKIN UWAWhere stories live. Discover now